20

6.6K 766 289
                                    

UWA UWACE...20

Batul Mamman💖

~Na san kuna hakuri. Hakurin dai zan yi ta baku akan rashin regular post. Nagode da bin rubutuna da kuke yi.

~Afuwan, wadda ta bamu award sunanta Maryam Muhammad Labaran, nayi kuskuren rubuta sunanta a sakon godiya da nayi.

     This page is for you sister Habiba Haruna (Mantis Kitchen). Allah Ya kara lafiya.

***

Buba da Habi sun shigo gidan sun tarar da Deluwa cikin tashin hankali da fargabar abin da ya sami 'Yashshafa. Sai fada take tana nanatawa lalura ce kuma babu wanda yafi karfin ta kama shi. Talaka da maikudi. Dan kauye da dan birni babu inda ba a aljanu. Su gidan wani abokin Buba suka je. Mutumin da kansa ya zo ya tafi dasu tun kafin fitarsu Abbati. Habi tana jin abin da ya faru ta yi 'yar dariya. Kafadar 'Yashshafa ta dafa ta ce,

"Gwaggo Deluwa dake take fa. 'Yashshafa ko ba Momi kike nufi ba na 'yan gayu?"

'Yashshafa dai kamar ta nutse a kasa. Idanuwa duka a kanta. Dadinta daya ma wannan mai dariyar da yayansa basu biyosu ba. Mami Khadija ma dariyar tayi ta tashi ta shiga ciki za ta hado musu 'yar tsaraba, musamman ma dai 'yar budurwar nan mai abin dariya. Deluwa na ganin ta rufe kofar koriďo din da zai sada ta da dakinta ta kaiwa 'Yashshafa duka a baya rai duk a bace.

"Yanzu ke Momi din ne baki iya fada ba ki ka hau kukan saniya? Ca nake 'yar gidan Bibalo ba momi suke ce mata. Kawai sai mooo, mooo ake ji kamar saniya ta tsinke daga turkenta. Mtseww"

Buba da Habi suka bushe da dariya. Sallamar Farha suka ji Baaba Mari ta soma hamdala. Tafiya zasu yi yanzu yanzu in Allah Ya yarda. Bata bukatar Hanne ta zo ta bar nata abin fadin kamar na Deluwa da 'Yashshafa.

Kafin ta shigo tun a waje Lilu ya tareta ya bata labarin gamonsa da 'yar tashe. Dariya taso yi aka kuma bude gate Abbati ya shigo. Zuciyarta tayi wani irin dokawa mai wuyar fassara. Abin sai ya bata mamaki tunda a hanya ta san Munzali ke jan motar. Bata ga alamun Munzalin ba sai mace. Shi ne ta shige bangaren Mami da sauri don ma kada su hadu.

Ya kula da irin saurin da take yi wanda yake da nasaba da gudun haduwa da Hanne. Da gaskiyar Munzali dai da ya ce masa kishinsa take.

"Wai shiga ka ke so nayi na kirasu? To wane bangaren zan je?"

Hanne ta katse masa tunani da ta bude kofa za ta fita.
"Don Allah Hanne ki kama kanki. Kin san abubuwan da bana so. Kar ki gwada musu a gidan nan. Godiya kawai muka zo yi musu na kyautatar da suka yi mana."

Ya san halinta. Ko babu komai tsakaninsa da Farha ba zai so ta shiga tayi abin da zai zubar mata da kima a idonsu ba. Idan Farha rabonsa ce zai so ta shigo gidansa tana ganin mutumcin wadda ta tarar kuma kanwa gareshi.

"Naji" ta amsa da kunkuni.

Abbati dakatawa ya yi aka yi musu izinin shiga bayan ya yi sallama. Yana saka kafarsa Farha na shigewa wata kofa da yake tunanin kitchen ne. Murmushi kawai ya yi sannan aka gabatar da Hanne ga Mami. Anyi sa a Mami Khadija tayi mata kwarjini shi yasa ta gaisheta a mutumce. 

Da kyar Mami Khadija ta samu suka ci abincin don sun matsu su tafi Kano a ranar. Basu dade suna jiran Munzali ba ya iso. Wurin Mardiyya ya fara zuwa suka yi sallama. Mama Nasima tana son tambayarsa alakarsa da abokan tafiyarsa da Mami Khadija amma yau ba hali. Ciwon karyar Mardiyya duk ya tsaya mata a rai.

Da zasu bar gidan Abbati ya so Farha ta fito ko yaya ya sake ganin fuskarta amma taki. Tsoron ganin matarsa take yi. A yadda ta ganshi hadadde dan gayu da wuya ace matarsa ba haka take ba. Idan kuwa haka ne kila sai ta raina kanta. Karshenta kuma tafiyar da bata taba irinta da wani d'a namiji ba ta sami tangarda. Gara dai kada ta kai kanta kallon abin da zai iya tada mata hankali.

UWA UWACE...Where stories live. Discover now