26

5K 647 100
                                    

UWA UWACE...26

Batul Mamman💖


***

Karfe shida da kwata a kofar gidan Alh. Rabi'u ta yiwa Salihi. Garin da sauran duhu hasken rana bai fara fitowa ba. Wasu magidantan ma basu  riga sun koma muhallansu daga masallaci ba. Daga ganin yadda ya ajiye mota zaka san baya tare da nutsuwa. Kasheta kawai ya yi ba tare da ya rufe ba ya fita ya soma doka sallama a kofar gidan.

Sallamar tasa ba karamin tsinka zuciyar Salima wadda ko tashi daga kan abin sallah bata yi ba tayi. A hanzarce ta mike suka kusa yin karo da Zara don ita ma ta gane muryar waye. Innayo kuwa iccen da take kokarin turawa a murhu tayi jifa dashi su ukun suka hado a kofar gidan da ko budeta ba ayi ba.

"Karbo min mukulli a wurin Alhaji"

Innayo ta furta muryarta tana fallasa fargabarta. Babu wani abu ko daya da zai kawo Salihi gidan nan da duku dukun asuba mai dadi.

Tare da Alh. Rabi'u Salima ta dawo ya sako babbar riga yana murza idanu don ko sallah bai yi ba. Innayo ya kalla ta jingina da bango zuciyarta tana ta dukan kirjinta.

"Aka ce Salihi ne yake sallama."

"Ni ne Alhaji" ya amsa daga waje.

Nasa hannun ma rawa ya kama yi sai Zara ce ta iya budewa Salihi ya shigo. Daga soron ya durkusa ya gaishesu sannan ya dan sosa keya.

Salima da Zara sai suka bar wurin tunda kowa ya fahimci ba tashin hankalin da suke taraddadi bane.

"Innayo ki bata hakuri tazo mu koma. Indai akan Ummule ne zan raba musu gida."

Alh. Rabi'u ya kalli Innayo kallo na wulakanci sannan ya yi wata irin banzar dariya.

"Hajiya Hauwa kenan. Kin nunawa kowa a gidan nan cewa kin fi kowa iya tarbiya da kyawun hali. Rannan har magana ki ka fada mana ni da Asabe akan 'ya'yanki. Sai gashi a tsukin abin da bai kai wata guda ba uku sun dawo gida. Allah Ya kyauta."

Wucewarsa ya yi ko waige babu. Salihi kunya ta lullube shi yaji kamar ya nutse a wajen.

Numfasawa Innayo tayi ta dube shi da murmushin da ya tsaya a fatar bakinta saboda bacin ran Uwani.

"Salihi aure kayi?"

Da sauri ya kalleta ba tare da ya iya boye mamakinsa ba.

"Uwanin bata fada miki ba?"

"Bata fada ba. Allah Ya sanya alkhairi. Sai dai kuma bata zo gidan nan ba."

Kansa da ya yi niyar yin kasa dashi ya sake dagowa da sauri hankalinsa a mugun tashe. Jiya bata da aikin kwana. A ka'ida ma kafin la'asar take dawowa a ranaku irin wannan. Sai gashi har bayan isha babu duriyarta. Ya dinga kiran wayarta babu amsa, wanda kuma tana sane don kada ya katse mata jiran mai haihuwar da zata zame mata alkhairi. Abu kamar wasa har goman dare. Nan fa yaji ba zai iya bacci ba dole ya tafi asibitin nemanta. Nos din da suke da aikin kwana ranar suka ce masa ta tafi. Basu san tana nan ba tunda kafin zuwansu ma 'yan yamma sunyi nasu sun tashi. Sai da ya tafi ne daya daga cikinsu ta ganta take fada mata wani yazo nemanta. Haka nan taji a ranta maigidanta ne amma sai taki kiransa. Dole zai yi mata ta dawo gida ita kuwa bata cikin masu wasa da neman kudi. Haka ya koma gida ko runtsawa bai yi ba. Tunaninsa ya tafi akan ko tayi yaji ne saboda zuwan Ummule. Shi ne  ya taho gidan da sassafe saboda baya son kowa ma hatta Ummule ta fuskanci da b'araka irin wannan tsakaninsu.

"Ikon Allah" ya ce lokacin da yake jin wani irin tsoro a ransa "nima nayi jinkirin zuwan ne saboda tunanin ko ta karbarwa wata aikin  kwana ne..."

Innayo ba shiri tayi 'yar dariya tana cewa "banda abinka Salihi yaushe zaka dinga magana kamar yau ka san Uwani? Ita da ba wasu kawayen kirki ba ai da wuya ne ta karbarwa kowa aiki."

UWA UWACE...Where stories live. Discover now