3

7.9K 750 176
                                    

UWA UWA CE...3

Batul Mamman💖

Duk duniya babu mai rufa maka asiri sama da mahaifiyarka. Komai lalacewar da sai ta kure sai kuma ta jure za ta iya fadawa duniya. Da mai kyakkyawar zuciya da ma mai akasinta duka suna yi ne domin kada rayuwar dansu ta lalace a wani mataki. Amfani ko kuskuren yin hakan ga dan da akayi dominsa kuwa gaba ce kadai za ta nuna.

***
Tsohuwar naira biyar da ta gama shan wahala tsakanin kwandastoci da direbobin tasi ta yayyage Shazali ya dauko daga aljihunsa.

"Ungo ka tafi gida." Ya sakawa Munzali a aljihun gaban rigarsa.

Yaron da kyar yake tsayuwa saboda bakar azabar da ya sha a hannunsu. Da ya tashi tsaye ma kafafunsa duka rawa suke yi.

Warce kudin abokin nasa da suka tafka ta'asar tare ya yi yana magana irin ta takadiran 'yan kwaya.

"Kai da talo-talo ne wani sa'in. Banda hauka ya za ka ce ya tafi gida bamu yanka masa wainin (warning) ba" kwalar Munzali ya ci ya fizgo shi gabansa ta karfin tsiya sai da ya yi kara "idan ka sake ka fadawa wani abin da muka yi maka sai na yanka uwarka. Ka san dai na santa ko? Ko ba Asabe Gantali ba ce gyatumar taka?" Ya karashe da yi masa tsawa.

"Ita ce" Munzali ya amsa da sauri jikinsa na bari. Ga ciwo ga tsoro.

Sai da suka tabbarar ya gama tsorata sannan suka kama gabansu. Tsoro bai bari ya zauna a wurin da sunan ciwo ba. Ga duhu ga kukan kwari da kananan dabbobin da suka mamaye kangon. Da jan kafa ya fito yana cije baki tare da runtse idanu. Idan hawaye ya taho sai ya sharesu da sauri saboda ya rike  kashedin da aka yi masa. Tafiyar minti shabiyar zuwa gidansu sai da ya rubanya ta.

Asabe sai kai gwauro da mari take yi wurin neman Munzali. Ta shiga duka makota gidajen da yake da abokai bata same shi ba. Nemansa take yi saboda nutsuwar kanta ba wai don Alh Rabi'u zai yi mata fada ba. Tarbiyar yaran a wuyan uwar da ta kawosu duniya ya rataya a nasa tunanin. Ummakati yayarsa ta gama karantawa wasu gidajen da za ta je ta fita ita ma ta sake daukar mayafi.

Tana isa soro Munzali na shigowa. Basu da wutar nepa amma akwai hasken farin wata saboda wurin babu rufi. Kunnensa ta jawo iya karfinta sai da ta durkusar dashi a gabanta sannan ta hau shi da fada tana jibgarsa. Bata taba yarda hukunya 'ya'yanta a gaban Innayo. Kullum nunawa take nata 'ya'yan basa laifi.

Munzali bai yi kuka ba ko ya roketa tayi hakuri kamar yadda ya saba idan ya yi mata laifi. Zazzabi yake ji ga ciwo babu wani sauran kuzari ko da na kuka ne a tare dashi.

"Shegen yawon tsiya kamar wanda makiya suka sako a gaba. Ban hanaka yin dare a waje ba? So ka ke babanku ya sani ya daina baka kudin makaranta?"

Naira biyar din da Shazali ya bashi ce ta fado ta kyalla ido ta gani ta dauka ta karkade. A kirjinta ta soke kudin sannan ta cigaba da yi masa fada kunnensa a tsakanin yatsunta tana ja.

"Ki yi hakuri Asabe."

Ya iya cewa da kyar yana jan jiki. Bayansa ta bi tana cewa gara ma ya saki jikinsa domin bata yi masa dukan da zai saka shi irin wannan tafiya ba. Ko kadan tunaninta bai bata ta binciki inda ya sami kudin ba. Ita bata ma son tayi zancensu bare ta ji cewa ba wadanda za ta iya ci bane. Inda ya je ma ba laifi bane indai zai dawo kafin duhun dare.

Innayo ya wuce bai gaisheta ba kamar kullum. An koyar dasu kiyayyar kishiya da 'ya'yanta tun kafin su gama wayo. Yana shiga bandaki ya fashe da wani sabon kukan. Bai taba jin ciwo makamancin abin da yake ji yanzu ba. Ga cikinsa ya kulle amma yana tsoron yi ya tadowa kansa sabon ciwo. Kukansa ya sha ya dauki wandonsa da ya baci da jini ya jefa cikin shaddar (masan kasa) ya fito. Rigarsa ta wuce gwiwarsa ma saboda haka babu mai gani.

"Munzali ina wandonka?"
Muryar Alh Rabi'u ta karade tsakar gidan.

Kafin ya bada amsa Asabe tayi saurin amshewa ta ce wai don ya ga babu wuta ne ba mai ganinsa shi yasa ya fito.
"Zai gyara Alhaji. Da kaina zan yi masa fada." Ta ja hannunsa "Bashi hakuri ka wuce muje ka ci abinci."

UWA UWACE...Donde viven las historias. Descúbrelo ahora