UWA UWACE...39
Batul Mamman💖
Su Innayo basu san wainar da ake toyawa a gidan ba sai da suka dawo ita da Salima. Tambayar inda Uwani ta shiga ta yiwa Zara ta fada mata duk yadda suka yi har fitarta.
"Ban san me yake faruwa ba amma tana fita Asabe ma ta fita"
Dama da tunanin halin da ta bar Uwanin a gida ta wuni. Wannan labari sam bai mata dadi ba. Duban 'ya'yan nata tayi ta ce daya daga cikinsu ta kira mata Uwanin a waya. Salima ce ta kira da aka amsa ta mika mata.
"Ban hana ki fita ba Uwani?"
Fita tayi daga dakin da aka kwantar da Munzali don kada ta tashe shi daga bacci. Kofar ma a hankali ta rufeta sannan ta ce,
"Muna asibiti da Munzali an kwantar dashi"
"Me ya same shi?"
"Bayanin ba zai yiwu ta waya ba Innayo"
Muryarta babu wannan gadarar da ta saba da nuna isa. Kamar ma da sigar rarrashi Innayo take jin amsoshin Uwani. Da taji a wane asibiti suke sallar magariba kawai tayi ta sake tashi. Sai da Salima tayi da gaske wurin hanata fita bata ci komai ba. A lokacin ne ta fadawa Zara abin da ya faru da Ayaah. Suka gama jajantawa sannan suka fita zasu tafi asibitin. Wannan karon dai Zara sam taki yarda su barta a gida. Ciwon dan uwansu da zai kai Uwani asibiti ko biyanta zai yi ba abin rainawa bane. Innayo ta girgiza kai kawai don bata ga alamun zata ji maganarta ba suka tafi.
Basu wani sha wahala ba suka iso dakin da Uwani ta kwatanta musu. Mamakin ganin Salihi a wurin ne ya kama Innayo. Ya gaisheta da fara'arsa sannan ya bata kujerar da yake zaune.
Sai da ta zauna sannan ta kalli inda Asabe take tayi lakwas. Ta kira kannin Munzali namijin mai suna Bature akan yazo ya kwana amma kememe yaki. Uzuri mara tushe ya dinga bata. Dama rabonta da ta sanya shi a ido an tasarma sati. Da dai rabon kudi yake ba zai yi fashin zuwa. Ummakati kuma mijinta yace dare ya yi za su zo gobe, duk da lokacin da aka fada mata shida bata karasa ba. A gidanta autarsu mace ta tare saboda kwadayi. Gashi mijin Ummakati yana mata kulle. Sai abin ya shafi kanwar da ya kula tana yawo. 'Ya'yan Innayo mata wadanda kullum take aibatawa tare da yi musu kallon rashin galihu sune a tare da ita.
"Asabe ya mai jikin?"
"Da sauki, gashi ya sami bacci."
Dakin sai ya yi shiru tunda hirar kirki dai bata taba hada duka mazaunan cikinsa a lokaci guda ba. Uwani waya take yi da wata mai shara tana bata sautun irin abincin da za a siyo da adadin mutanen dakin. Jin haka Innayo ta ce,
"Mu kam a koshe muke"
"Sai a tafi dashi gida. Guda bakwai za ki karbo kinji" ta karkare wayar tana duban Qibdiyya wadda ke faman matse kafa.
"Kina jin fitsari ne?" Ta tambayeta. Da ka ta amsa don ta matsu sosai.
Tashi tayi domin ta kai ta sai Asabe ta riga. Dakin ya zame mata kamar akurki. Kwarjinin Innayo da zuri'arta yasa ta kara jin kanta kamar wata 'yar kora. Suna fitowa taji ance,
"Barka da dare Asabe"
Sakin fuska tayi da ganin fuskar da ta sani.
"Barkanmu dai dannan. Shiga ciki ga dakin da aka kwantar dashi."Qibdiyya da ya gani tare da ita ya jefa tunaninsa a mizanin aune-aunen hanya mafi saukin bullewa. Babu bata lokaci kuwa ya cafki damar da ta zo gareshi da gaggawa.
"Ina zaki je ne?"
Hagu da damanta ta dinga kalla ta ce "wallahi inda zan sami piya wata (pure water) nake nema wai fitsari Qibdiyya take ji"