2

52 3 0
                                    

❄️❄️❄️❄️
*INA MAFITA* ?
❄️❄️❄️❄️❄️

*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞

( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)

/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/

P.W.A✍️

*Short story*

*STORY & WRITING*

*BY*

*SAFNAH ALIYU JAWABI*

2️⃣

*My Best wishes gos to*

_BAMAI DABUWA_
_RABI'AT SIDI BALA_
_SADDIQAH YAHAYA FARU_
_SA'ADAT MADOBI_
_HIBBATULLAH_
_SUMAIYYA NUHU_

*Learn to overcome your challenges. Don’t run away from pain, fear and brokenness. Face them head on. Make a plan. It won’t be easy. But know that you’re never alone. Call on the Almighty. But whatever happens, be sure not to give up. Persistence is key in overcoming challenges.*

______Bayan fitar Yayan nata daga cikin gidan sake fashewa da kuka tayi tana mai dana sanin auran sa ,duk da kuwa tsananin son da take masa.

Kallon ta aunty *Murja* tayi tace,"yanzu ke a haka kike fatan karasa rayuwar ki?

Gyaɗa kai kawai tayi wasu sabbin hawaye suna zuba tace,"Aunty *Murja* yaya zanyi? "Ke kanki sheda ce akan yanda akayi har Yaya ya yarda aka daura mana aure da wannan mutumin, yanzu kuma sai na kwaso jiki na ce, "auran  nawa ya mutu.?

"Hmm kema kinsan abinda sam bazai taɓa faruwa ba kenan.

"To shikenan ALLAH yayi mana mai kyau."

"Aunty yayi saidai ya ƙara."

Daga haka Aunty *Murja* ta shige ɗaki abin ta.

________
Koda ta fito daga bayin da alwala ta fito jan kafarta kawai take saboda tsananin azabar da take ji.

Wasu zafafan hawaye ke sauka a saman fuskarta.

Shi kuwa kallo ɗaya yayi mata ya dauke kai,domin kuwa idan har ya fiye kallon ta tofa babu shakka sake afka mata zaiyi.

Ganin hakan ma bazai wadatar dashi ba yasa ya miƙe ya fita daga gidan ma gabaki ɗaya.

Sauke ajiyar zuciya tayi ta ce,"alhamdullahi alhamdullahi alhamdullahi!!!

Saida ta kwashi tsawan mintina talatin tana zaune saman sallaya tana kaiwa ALLAH buwayi gagara misali kukan ta, sannan ta mike ta nufi kitchen don sama musu abinda zasu saka a bakin salatin su.

Shi kuwa koda ya fita dafe kansa yayi yana jin kamar ma babu abinda yayi,wani irin kuzari ke shigar sa,ciza yatsa yayi ya ce,"kai gaskiya komawa zanyi dan gaskiya bazan iya haƙura ba.

Harya sa kai zai juya ya jiyo sallamar Idi mai tsire,cike da ɓacin rai ya bashi hannu suka yi sallama.

Shi dai Idi kallon sa kawai yayi yana murmushi don basai an faɗa masa ba ,dan kuwa zai iya rantsewa duk duniya banda ALLAH babu wanda ya kaishi sanin halin *Abba* tunda tun suna yara suke abota.

Tsaki *ABBA* ya ja ya ce,"menene ka wani tsare ni da  idanuwa lafiya dai ko"?

Murmushi Idi ya kuma yi yace,"kai malam kasan bansan rainin hankali ko"?

"Rainin hankalin me nayi maka?"

"Ka mance yau mukayi dakai zamu tafi gidan Na Lado"?

Shafa kansa kawai *Abba* yayi yace,"kai amma gaskiya kai baka da mutunci shine tun ɗazu baka zo ba sai yanzu"?

Jan hannun sa Idi yayi suka bar kofar gidan.

*Yumna* kuwa wacce tun ɗazo take window tana lek'en mai gidan nata, sauke ajiyar zuciya tayi tana mai sawa Idi albarka.

*********

Zaune na hango *Hanan* cikin ƙawayan ta kowa ka kalla zaka fahimci irin farin cikin da yake ciki, saɓanin ita da ta haɗa girar sama data ƙasa,tana yi tana sauke ajiyar zuciya. Ji tayi an dafa ta cikin sauri ta waiga, Maryam ce wacce tunda suka shigo gurin take lura da halin da *Hanan* take ciki .

Murmushi tayi mata tace,"zo muyi magana ƙawa.

Bata musa mata ba ta miƙe, duk da zolayar da sauran abokan suke mata hakan baisa tayi koda murmushi ba,domin kuwa raɗaɗin da take ji a cikin zuciyar ta mai yawan gaske ne.

Can nesa dasu suka tsaya kallon ta Maryam tayi ta ce," *Hanan* lafiya kuwa?

Gyara tsayuwar ta tayi tace,"lafiya ƙalau me kika gani?"

Murmushi kawai Maryam tayi tace,"karki mance tun bansan kai na ba na sanki *Hanan*, tabbas kallo ɗaya nayi miki na fahimci kina cikin damuwa,ban sani ba ko zaki iya faɗa min?"

Kallon ta *Hanan* tayi tace,"Tabbas ke ƙawata ce ƙawa irin wacce tuni muka birne wannan sunan muka koma ƴan uwa ,saidai kuma ki sani sam ita rayuwar aure ba kamar yanda da yawan mutane suke daukar ta bane ba,ita rayuwar aure sirri ce Maryam idan nace sirri ina nufin sirri.

Ajiyar zuciya Maryam tayi tace,"shikenan,amma ki sani komai yana da *MAFITA* kuma yana da hanyar magance shi ,da yawa basu fahimci rayuwar aure ba,duk da kuwa Ni banyi ta ba,amma ki sani na  karance ta yanda bakya tunani, *Hanan* bance ki faɗa min sirrin ki ba,amma dai koma menene ki sani akwai *MAFITA*

Jan hannun ta tayi suka koma inda suke zaune ,lokaci zuwa lokaci Maryam takan saci kallon *Hanan* addu'a kawai take mata fatan ko Mecece damuwar ta *ALLAH* ya kawo mata ɗauki.

*Hanan* kuwa jinjina maganar Maryam kawai take a zuciya ,har suka bar gurin.

*********

Hauwa bata koma gida ba sai gabda magrib,bayan Umma ta har haɗa mata kayan kwalliya, turare, da dai sauran su. Tsaye ta same shi riƙe da ƙofar shiga cikin gidan. Ba karamar mamaki hakan ya bata ba ,ganin gashi an  ta yarda sahun salla ,amma shi yana tsaye sai wani jijjiga jiki yake kamar mace.

Murya a raunane tace,"Barka da gida yallaɓai.

Wani uwar harara ya banka mata yana mai jan duguwar tsaki daidai malam Ado mai dabino yazo zai shiga Masallaci.

Murmushi kawai Malam Ado yayi yace,"Namu addu'a kawai zamu maka domin abin naka sai addu'a.

Tsaye take jiki sai mazari yake kamar wacce ta shiga cikin ƙanƙara,bata ankara ba taji ya dauke ta da wani irin mari mai fitar da mutum daga haiyacin sa lokaci ɗaya.

Cike da firgici tace,"wayyo ALLAH na menayi maka   kuma?

Aikuwa kamar ta ƙara ingiza shine,aikuwa ya hau dukan ta saida yayi mata sosai sannan ya rabu da ita yana mai sauke ajiyar  zuciya.

Hauwa wacce tuni ta gama fita a haiyacin ta ,banda numfashi babu abinda take sauke wa.

Sai yanzu yakai idanuwan sa kan ledar data shigo dashi , ɗaukowa yayi ya duba abinda ke ciki.

Cikin ƙunan rai yace,"wani ɗan iska ne ya baki wannan?

"Au Hauwa abin naki har yakai girmar haka

"Yanzu kuma maza kike koma bi?

kawai take maimaitawa saboda sam bazata iya buɗe baki tayi masa magana ba.

Aikuwa ganin tayi masa shiru yasa ya shiga Farfasa kayan nan ,saidai yayi ɗaiɗai dasu sannan ya haƙura.

Huce yake kamar namijin zaki.

*Aunty ALLAH yau da zazzabin na tashi , amma saboda ke nayi wannan pls manage kinji? Much love*

INA MAFITA?Where stories live. Discover now