❄️❄️❄️❄️
*INA MAFITA* ?
❄️❄️❄️❄️❄️*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*Short story*
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
5️⃣
*When you see a bend in the road, it’s not the end of the road. Take the leap of faith and make that turn. That’s life in essence. You have to keep going. No stopping. No quitting. You only win if you don’t quit. So don’t ever give up on yourself!*
😊______Kallon Hauwa yayi yace,"munafuka wato abinda keki yi kenan dama ko?"to ALLAH ya tona asirin ki,koma wallàhi yau dai sai kinyi dana sanin Abinda kika yi".
Banda hawaye babu abinda ke zarya a kuncin ta,kuka take sosai tana roƙon shi ,amma ina sai ma ƙara fisga yake , aikuwa saida yayi mata dukan tashi ki sha gari sannan ya rabu da ita.
_________
Sosai kalaman A'isha suke yawo cikin kan ta,tabbas tasan rayuwa bazai taɓa tafiya a haka ba,shin wazan kaiwa kuka na?
Tabbas idan na faɗa a gida ko shakka babu rabani da *Nazifi* za suyi Ni kuma wallàhi ban shirya rayuwa babu shi ba.Haka ta tayi ta saƙe saƙe a ranta harta iso gida,zaune ta same shi yana danne dannan waya da gani yana cikin farin ciki abin sa.dafe kai tayi tace,"yanzu Nazifi har wani fari ciki kake kenan"?.
A firgice ya miƙe dan kuwa sam baima san ta shigo ba, marairaice fuska yayi yace,"sweet heart kin dawo"?
Kallon sama da ƙasa tayi masa ta shige ɗauki abinta.
Zama tayi tana tunanin yanayi da tazo ta same shi,"kenan babu abinda yake damun sa"?
"Tab aíkuwa wallàhi da sake sam bazan ɗauki wannan cin mutuncin ba .
Tashi tayi ta l shige toilet ,wanka tayi sannan ta ɗauro alwala tayi sallolin da ake binta,saida ta gama addu'a sannan ta samu guri ta ƙwanta,har yanzu zan can A'isha ke mata yawo azuciya,shin ba cutar kaina kuwa nake ba? Lallai akwai bukatar na sama wa kaina *MAFITA*, jin yanda sha'awa yake niyyar kashe ta yasa tayi gudu ta shige toilet,yau dai kam abu yayi tsananin domin kuwa abinda take gudun yinsa shine tayi, sannan ta samu sukuni,sauke ajiyar zuciya tayi tace,"waiyoo ALLAH na,wai shin yaya ƴan lees suke jine?"wallàhi babu wani daɗi anan banda tsantsar wahala, ALLAH ka shiryar damu akan ta farkin gaskiya.
Duk abinda take Nazafi yana kallon ta ,Saida ya tabbatar ta shige ciki sannan yayi murmushi yace,"wallàhi ina tausaya miki amma kuma nima kaina ina tunanin kai na,kome ya tuna kuma naga ya fashe da dariya.
*******
Koda A'isha ta isa gida kallon kanta tayi a madubin ɗakin ta,tana mai jin kunci da ɗaci a ranta,shafe daidai inda *Hanan* ta mare ta tayi tana mai ƙara jin tsanar ta a cikin zuciyar ta.
Ɗaga waya tayi ta danna wasu number,bugu ɗaya aka ɗaga ,ba tare da sallama ko gaisuwa ba tace,"malam ka gyara zama tafa amince,in Sha ALLAH sai kayi sukuwa saman dokin alfarma,kuma sai kasha zuma mai dauke da sinadari mai tsayuwa a rai.
Daga can ɓangaran kuwa *IMRAN* wanda gabaki ɗaya wannan albishiri
da take masa yasa yake ji kamar anyi masa kyautar gidan aljanna,banda godiya babu abinda yake mata,saida ya gama wayar tsaf sannan ya kalli Safyan yace,"kai baba wallahi nayi sabon kamu".Da mamaki Safyan yake kallon shi yace"sabon kamu kuma"?
Tsaki *IMRAN* yayi yace," Wallahi shiyasa sam bana ƙaunar nayi hira da kai ,saboda ka fiya gidadanci"Haba mutum kamar ba ɗan birni ba mtsss".
Murmushi kawai Safyan yayi yace,"wallahi wayewa irin taka *IMRAN* sam bana ƙaunar yinta,domin kuma iya kata da ita mutuwa wacce bana kai ta da nisa,domin kuwa ko yanzu tana iya zuwa ta ɗauke ni,saboda haka wannan hanyar da kake kai wallàhi bamai ɓullewa bace ba".
Duk da kalaman sa sunyi mattukar taɓa zuciyar sa hakan sam ɓaisa yaji zai dana ba, Saidai ma wani murmushi da yayi yace,"naji zancan ka amma ka sani wallàhi da na samu irin matar da nake so Safyan babu abinda zai sa na shiga irin wannan harkar".
Gyara zama Safyan yayi yace,"wace irin mata kake da burin aura *IMRAN*"?
Murmushi yayi yace,"mace mai aji,mace mai kyau da kwalliya,mace mai shiga ta daukar hankali,mace mai iya kalamai,mace wacce shigar ta kawai zai sanarwa duniya nayi dacan mata."
Tunda *IMRAN* ya fara magana Safyan ya sake baki yana kallon sa ,Saida yakai aya sannan yace,"*IMRAN* banji kayi magana akan mace mai addini ba,banji kayi magana akan mace mai tarbiyya ba,banji kayi magana akan macan da zata suturta maka kanta ba,banji kayi magana akan macan da zata kare maka martabar ka ba?"shin *IMRAN* kana cikin haiyacin ka kuwa?"shin kana tunawa da akwai ranar da zaka amsa duk wa'annan tambayoyin a gaban mahaliccin kuwa"? " Wallahi na tausayawa rayuwar ka tausayin irin wacce ake wa maraya.
Yana kai nan ya tashi ya bar gurin yana mai addu'a ALLAH ya shiryar da abokin sa,kenan dama akwai masu irin wannan halin?
To wai ina *MAFITA* ga irin wa'annan mutanan?******
Cikin ikon ALLAH suna fita suka samu mota,gudu sosai Lukman yake yi ganin har yanzu bata ko motsa ba, kasancewar asibitin na kuɗi ne yasa aka amshe su ba tare da ɓata lokaci ba.Kusan awannin Dr suka ɗauka akan ta ,sosai wannan lamari ya firgitar da su saboda sun daɗe basu ga wani abu makamanciyar wannan ba.saida suka tabbatar ta dawo haiyacin ta sannan suka fito.
Da gudu Lukman ya karaso gurin Dr yana tambayar ta jikin*YUMNA*
Kallon sa tayi sama da ƙasa tace,"kaine mijinta"?
Jiki a sanyaye yace,"eh n...
Wani wawan marin data sauke masa ne ya hanashi ƙasara zancan sa,kallon sa tayi hawaye yana zuba tace,"kai dai azzalumi ne kuma da gani zakayi son zuciya wallàhi sai ka girbi abinda ka suƙa ,kuma ka tanadi amsar da zaka bawa hukumar lafiya da kuma hukumar ƙare hakkin dan Adam daga nan zuwa safe,banza sakarai kawai."
Wani irin gume ke karyo masa ta ko'ina shi kansa yasan yayi ba daidai ba,amma shifa haka haliltar sa take,dafe shi Idi yayi yace,"wallàhi baka kyauta ba abokina,kullum maganar da nake maka kenan amma kake jin haushi na,wani lokacin ma sai kace ina maka kutse cikin lamarin ka,yanzu kalli abinda ka aikatawa baiwar ALLAH ,matar da take mattukar ƙaunar ka".
Kallon Idi yayi yace,"kaji abinda Dr ta faɗa yanzu Mecece*MAFITA*?
Sauke ajiyar zuciya yayi yace,"nasan itama abin takaici ya bata shiyasa ta faɗi haka,amma yanzu mu tafi office ɗin ta mu bata haƙuri in Sha ALLAH komai zai daidaita.
Da haka suka nufi office ɗin Dr farida,kallo ɗaya tayi musu ta ɗauke kai,sosai ranta ke zafi da wannan abin ,ji take kamar ƴar ta aka yiwa haka.
Izinin zama ta basu Sannan Idi ya fara da bata haƙuri,sosai ta fahimci Idi mutum ne da yasan ya kamata hakan yasa ta kalle shi tace,"shin kasan illar da yayi wa Rayuwa yarinyar nan"?
Girgiza kai Idi yayi yana jin gabansa yana tsananta faɗuwa,domin kuwa ALLAH shaida ne yana mattukar tausayin *YUMNA*.
Ajiyar zuciya Dr farida tayi tace,"wannan bawan ALLAH ba ƙaramin ciwo ya jiwa yarinyar nan ba,ina mai tabbatar maka saidai wani ikon ALLAH ne kawai zai kubutar da ita daga faɗawa cikin jarabtar yoyon fitsari.
Wani irin zabura sukayi a tare ,tuni Idi ya fara hawaye gogan kuwa gabaki ɗaya kasa kuka yayi saboda wani abu da yaji ya masa tsaye a maƙoshi....