❄️❄️❄️❄️
*INA MAFITA* ?
❄️❄️❄️❄️❄️*PERFECT WRITER'S ASSOCIATION*🌞
( WE AIN'T PERFECT BUT WE'RE ALWAYS, TRYING OUR BEST TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS 💪)
/https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
P.W.A✍️
*Short story*
*STORY & WRITING*
*BY*
*SAFNAH ALIYU JAWABI*
3️⃣
_*Wai wai wai wannan shi ake cewa ƙarshan zance, kai ne ma mallakin mai wannan littafin kan ta,saboda haka cewa na sadaukar maka da liltafin ma ɓata baki ne My heart desire*_
*Ya Hai, Ya Kayum,all praises and admonition to almighty Allah,the Lord of the seen and unseen, the Lord of the known and unknown, bestower of blessings to whom He wants. Please forgive us our shortcomings bless us in this world and guide us to your rewards of Aljana Fridaus.*
__________Kallon kanta take jikin mirron ɗakin tana kara yiwa ALLAH godiya da irin tsarin haliltar da yayi mata.
Ƙarar wayar ta da ta fara jiyowa ne yasa tayi saurin juyowa ta ɗauki wayar tana wani yatsina fuska.
Marairaice fuska tayi daidai lokacin data daura wayar a kunnan ta."Hello.
Daga ɗayan ɓangaran aka amsa da
"sarauniyar matan duniya barka da wannan lokaci".
"Ƴawwa barka fatan kana lafiya".?
"Washe baki yayi yace,"lafiya ƙalau sarauniya."
"Ok."
"Ƴawwa nace ko kin gama shirya wa nazo na ɗauke ki."?
Shiru tayi na ɗan wasu mintina sannan tace,"eh kazo ina jiran ka".
Jiki na rawa yace,"tam in Sha ALLAH yanzu zaki ganni".
Yana ije wayar ya miƙe jikina rawa yace,"kaga Safyan sarauniya tayi kira na,bara na hanzarta.
Kallon mamaki Safyan yake binsa dashi yace,"yanzu kai saboda ALLAH abinda kake yi kana ganin shine daidai?
Nan da nan kuwa ya haɗe fuska kamar wanda aka aikowa da mutuwa yace,"dalla Malam babu ruwan ka cikin sha'anin rayuwa ta , wallàhi idan ba dan ina ganin girma da kuma amintar mu ba , wallàhi da saina faɗa maka abinda bazaka taɓa mance dashi ba,haba shikenan Ni kuma ba zanji daɗin rayuwa ta ba.?
Gyara zama Safyan yayi yace,"yanzu *IMRAN* saboda ALLAH ita matar taka dame ALLAH ya rage ta.?
Yatsina fuska *IMRAN* yayi yace,"wallàhi kyau da tsari matata tafi sarauniya,saidai kuma sarauniya tafi ta komai na aji da gayu,"sarauniya tana da class ,sarauniya tana da zakin murya, Sarauniya tana da iya ƙwalliya , wallàhi idan tayi ƙwalliya duk namijin dayayi arba da ita wallàhi sai ya koka.
Wani irin takaici ne ya turnike Safyan jin wa'annan kalamai da abokin sa yake faɗa.
Tashi kawai yayi yace,"shikenan ALLAH yasa mu dace".
"Amin ɗan sa ido kawai.
***********
*Hanan* kuwa koda ta koma gida gabaki ɗaya zazzaɓi taji yayi mata dirar miƙiya,tashi tayi da ƙyar ta dauko magani ta ɓalla tasha..
Tana kwance *NAZIFI* ya shigo hannun sa dauke da bakar leda.kallon sa tayi ta sakar masa murmushi,dan kuwa tsakani da ALLAH tana mattukar son sa ,so irin wacce ita kanta bata san adadi ba.