Haka siyayyar lefen ta kasance, hatta boxes tare da shi muka zaba Aunty kuma ta siyo, komai sai abinda nake so abinda na zaba sannan zai yarda a saka in kuwa ta sayi wanda ban zaba ba sai yayi mata tijara ta sake wani. Farko in yana mata haka sai inga kamar rashin kunya, daga baya sai na fuskanci akwai wasa sosai a tsakanin su kuma na fahimci ita ce take musu wasan dan ni kaina ta kan kirani a waya ta tsokane ni.
A haka aka hada lefen, kamar yadda na fada kayan kwalliya tare muka je muka siyo da Mufida da Farhan, a lokacin na ga uban kudin da ya kashe a iyakacin kayan kwalliya kawai, sai na fahimci lallai dole samari suji tsoron lefe dan ba karamin aiki bane ba.
A daren ranar ne bayan mun dawo gida mun yi shirin kwanciya sai ya kira ni a waya kamar yadda ya saba duk dare, "Aunty ce ta aiko ni, tace in tambaye ki size din pant da bra" na rufe ido na da sauri kamar yana kallo na "kai dan Allah" ina jin shi yana dariya, "ni dai dan aike ne, amsa kawai za'a bani sai inje in bayar ni ma" nace "ba wani nan, Aunty ba zata yi maka wannan tambayar ba ai tana da number dina zata iya tambayata ko kuma ta saka Mufida ta tambaye ni"
Yace "Allah da gaske nake fa, ta tambaye ni nace ban sani ba tunda ni ban taba gani ba sai dai ta cikin hijab, ta cikin hijab kuma ba gane girman nake yi sosai ba amma dai ina ganin kamar suna da dan girma haka....." Na katse shi "ka ga ka daina, zan kashe waya fa wallahi in baka daina ba" yana dariya yace "sorry Baby. I am just curious, dan Allah ki gaya min size nawa ne, babu wanda zan gaya wa daga ni sai ke"
Nace "kuma kace Aunty ce ta ke tambaya" yace "ni ne nake tambaya. I just want to know" nace "ai kuwa ba zaka sani ba" yace "kar ki rantse dai, only time will tell. In dai size ne kwana nawa ya rage in sani, ba size ba har shape da texture duk zan sani, in auna abina da kai na......." Banji karshen maganar ba na katse wayar tare da tura ta kasan pillow na na kuma rufe kunnuwa na da hannayena amma ban daina murmushi ba. Da gaske zai sani? Duk wannan abinda ya fada zai faru ko? Na shiga uku.
Ina jin wayar tana ta ruri amma ban daga ta ba dan nasan shine har saida ya hakura ya daina kira.
Shigowar Farhan ya dawo dani daga tunanin abinda zai faru a ranar da Umar yake magana akai, ta zauna a bakin katifa tana jujjuya wayarta a hannun ta amma hankalin ta baya tare da ita sam. Na mike zaune ina kallon ta. "Har yanzu bai kira ba ko?" Ta gyada kai kawai ba tare da ta kalle ni ba tace "bai kira ba kuma wayarsa bata shiga. Ina jin yayi blocking dina ma" na jinjina kai kawai sannan na koma na kwanta dan ban san abinda zan ce mata ba.
Kamar yadda komai yake tafiyar min dai dai haka komai yake tafiyar wa Farhan ba dai dai ba. Na farko kuma mafi muni shine yadda Sulaiman ya juya mata baya lokaci daya tunda ta sanar da shi cewa Abba yace ya fito maganar aure, farko sai yace shi bai san yanzu ne za'a yi auren ba dan bai gama sanin ta ba yana so a kara masa lokaci su kuma fahimtar juna, ta nuna masa cewa ba wai a lokacin za'a yi ba za'a dauki watanni kawai dai ana son in da gaske yake ya turo magabatan sa ayi magana.
Tun daga nan ya fara ja mata aji, a hankali ya fara zamewa har ya kasance ya tafi ga baki daya. Tun tana boyewa Abba har dai ta fada masa gaskiya shi kuma yayi mata barazanar ko ta fitar da wani ko kuma shi ya fitar mata dan shi lallai tare yake so ya hada mu. A duk sanda ya yi mata irin wannan fadan in ta koma gefe ta kan ce "to ni in ba ni ake so ince ina son kaina kuma in auri kaina ba ban san ya ake so inyi ba, ba sai ance ana so na ba sannan zan ce a fito? Ko kuma mutum zan tara a hanya kawai ince masa ya fito ya aure ni?
Abu na gaba kuma shine karatu, da bata saka ran zata yi karatu ba dan tun mun yara Farhan itace mai son aure ni mai son karatu amma yanzu ganin kullum ina fita inje makaranta ita kuma tana zaune a gida daga kallo sai kwanciya sai ta fara son makarantar itama. Sai dai fur Abba ya shafawa fuskarsa toka yace ba a gidan sa ba nima wanda zan aura ne ya samo min, ita ma ta fito da miji sai ya samo mata. Haka ta hakura, da kyar ya samu ya siya mata waya irin tawa bayan Hajiya tayi kamar zata kona gidan saboda balain ta.