The Visitor

2.5K 142 8
                                    

Ya ajiye wayar a gefe sannan ya nuna min kan cinyarsa, "come Baby, zo ki fada min waye ya taba min ke da tsakar ranar nan" na tafi naje na zauna a inda ya nuna min, na kwantar da kaina a kirjinsa sannan nace "wannan yarinyar, bai kama ta take shigowa dakin ka har ta kwanta akan gadon ka ba"

Ya dago da fuska ta yana kallona "wai Ummi? But why? She is like a sister........" Nace "like a sister, not a sister. Matsayin ta shine kanwar kishiyar Mama. Babu dangantaka ta jini ko kadan a tsakanin ku" sai yayi murmushi "kishi, kishi, kishi, I feel honored" na ture shi. "Ba kishi bane ba gaskiya ce. Dakina ko gadona duk zata iya shiga ta kwanta amma gadonka ba gurin zuwan ta bane ba. Ba ita ba ko su Mufida da kuke ciki daya dasu bai kamata su zo su kwanta akan gadon ka ba ko da ace baka dakin ballantana kuma kana nan sannan kai ma kana kwance akai"

Ya mayar da kaina kan kirjinsa ya kwantar "shikenan, sorry Baby, ba zata sake shigowa ba tunda ba kya so. In ba kya son ta zauna a gidan ma yanxu sai in kai ta gida tunda ba gidan ubanta bane ba" na dago kai "a'a ni bance ka mayar da ita gida ba, in nayi haka Aunty ba zataji dadi ba, kawai dai ina son boundary a tsakanin ku, bana son yadda kake bari tana taba ka a duk lokacin da tayi niyya dan kai ai ba muharramin ta bane ba kuma shaidan babu zuciyar da baya shiga even the purest of hearts"

Yace "Allahu Akbar. Ya ustaziyya Hauwa'u"

naga alamar wasa yake so ya mayar da maganar, na mike "eh naji ni ustaziyya ce. Ka tashi kayi sallah" na fada half hopping inji yace min yayi amma sai naga ya mike ya shiga toilet, na kalli agogo, almost three o'clock na rana amma bai yi azahar ba.

Ni a gidan mu na saba maza masallaci suke tafiya, in ba wani uzuri mai karfi ba da wahala ki ga wani yayi sallah a gida amma Umar sau da yawa a gida yake abarsa, a gidan ma wani lokacin sai nayi ta tuna masa musamman in yana wani abu sai yace sai ya gama.

Na danga chanji a lamarin sa da Ummi, ya kan cire hannun ta daga jikinsa in ta rike shi ko kuma ya matsa in ta zauna a jikin sa, sai kuma na lura gidan duk ya ishe ta duk tana ta kunci kwana biyu bayan nan ma tace tafiya zatayi gida.

Umar ya siyo mata doguwar riga da takalmi ni kuma na bata mayafi da kayan kwalliya muka kaita gida, amma sai twins suka ki zama suka ce  biyo mu zasuyi mu dawo gida.

Sai naga Mama ta bata rai "ku kun fiya rikici wallahi. Kawai dan kuje su saka su wahala ba kunyi kwana goma a can ba? Shi yana aiki ita tana karatu waye zai zauna daku a gida? Ita kuma Ummi da zata zauna daku din tace ba zata koma ba ya kuke so suyi daku?"

Na danyi murmushi "babu wahala ai Mama, gobe sunday bani da school shi   kadai ne zai fita, jibi kuma in zamu fita sai mu biyo mu ajiye su anan tunda hanyar mu ce"

Ta bata rai. "ba wani hanya, lokacin da zaku bata gurin shigowa da su ai yaci ace kunyi wani abun. Kuma keda ba ke ce mai driving ba ai ba ke ce zaki wahala ba"

Sai naja bakina nayi shiru amma bana jin dadin yadda yaran suka yi kamar zasuyi kuka. Ga Aunty tana Lagos a lokacin. Na daga kai na kalli Faruq da yake ta danne danne a waya kamar ma bai sannan maganar da ake yi ba. Na dan dungure shi da kafata. Ya kalle ni sai na marairaice masa. Ya juya ido sai kuma ya mike yana saka wayar aljihu yace "su taho mu tafi, monday din sai mu dawo dasu"

Muna tsaye a bakin gate muna jiran maigadi ya bude mana gate sai ga bakuwa munyi, Maryam kawata. Tun da ta doso motar take washe baki tana kara sauri, nima nayi mata murmushi sannan na daga mata hannu ina nuna wa Umar ita "ga Maryam nan, kawar mu ni da Mufida, ka gane ta?" Sai naga ya dauke kai kamar bai ganta ba sannan yace "eh" tana karasowa ga mamaki na sai naga ta zagaya ta window dinsa

"Yaya Doctor sannun ku da dawowa, ashe na kusa in daki gurbi na kusa in tarar ba kwa nan" sai naga ya nuna ni da yatsansa "kamar kinyi batan kai, ga kawar taki can" sannan sai ya daga mirror dinsa.

💔 JIDDA 💔Where stories live. Discover now