The New Couple

2.3K 163 12
                                    

Ina komawa daki na mayar da lock dina sannan na hau gado nayi kwanciya ta.

Sai dai duk da gajiyar da nake tare da ita, da tabbatar wa da nayi cewa he is okay amma sai na kasa baccin, ko dan bakunta ne? Yawanci in naje bakon guri bana iya bacci har sai na saba da gurin tukunna. Sai da gari ya kusa wayewa sannan na samu bacci mai nauyi ya dauke ni kuma saboda rashin sallah ta sai nayi dogon bacci sosai har gari ya waye. Sanda na farka har rana ta fito sosai, sai dai duk da haka banji baccin ya ishe ni ba.

Amma sai dai abu daya ne ya saka ni dole na tashi, wata azababbiyar yunwa da naji tana kwakular cikina. Na tashi na nemo sabon brush dina da na saka a karamar jaka ta, sai dai kuma babu toothpaste a toilet din kuma ban zo da shi ba. Haka na hakura na wanke bakin sai kuma nayi wanka na kawai gabaki daya na fito na gyara jikina na kuma shafa mai sannan na dauko doguwar riga zan saka sai kuma na fasa na dauko rigada skirt na atamfa na saka na feshe jikina da turare, ina tunanin sa a raina "ko ya tashi?" Nayi murmushi dana tuno da kalaman sa na cewa zai mutu kafin safe.

Sai kuma na tuno da kajin da ya shigo da su, nasan in ma zai ci ba zai iya cinyewa ba, Allah yasa basu yi komai ba in samu inci dan ba karamar yunwa nake ji ba. Har zan fita sai kuma na dawo na nemi hijab na saka, Umar ba kunya ce da shi ba babu ruwansa da cewa rana ce yanzu zai iya cewa zai taba ni.

Na murda kofar a hankali na leka na tabbatar baya corridor din sannan na saka kafa ta cikin sanda na fita, na bude kofar falon na shiga a hankali ina dosar hanyar da zata kaini kitchen, maybe acan ya ajjiye kajin.

Sai dai taku biyu nayi na ganshi.....

Yana kwance akan doguwar kujera, pillows every where, ya dauko standing pan ya tsayar da ita a kansa ga kuma uban sanyin acn da naji tana ratsa har cikin kashi na. Amma shi ko riga babu a jikin sa sai singlet da dogon wando, Daga yanayin kwanciyar sa na fahimci tun dare yake a haka bana jin ko sallah ya tashi yayi.

Sai na fasa zuwa kitchen din na taho inda yake, na kashe fankar na janye ta ina fargabar in ba sa'a yayi ba sai mura ta kama shi dan ni already sanyin palon ya saka ni ina jina kamar mai zazzaɓi. Sai kuma na tsaya ina kare masa kallo, zuciya ta tana yaba kyawun halittar sa da yanayin kirar jikinsa, Sannan kuma raina yana kara jin tsoron sa. A lokacin na lura duk harken fuskar sa da nake gani fatar jikinsa tafi hashe Sannan kuma raina yana kara jin tsoron sa.

Na koma side din kansa a hankali na daki jikin kujerar.

"Yaya Doctor?"

Na sake daga murya

"Yaya Doctor ka tashi fa.....ko kayi sallah ne? Rana ta fito fa"

Ya dan motsa kadan sannan yayi juyi, yana zubar da some of the pillows daya jejjera akan kujerar, na dauki daya daga ciki na dan dake shi kadan. "Ka tashi fa....assalatu khairun minal...." Ya juyo ya watso min kallon daya saka na yar da pillow din na ja da baya d sauri, banason wannan jan idon nasa.

Yace "go away. Kar ki sake min magana babu ruwana da ke"

Ya mayar da kansa cikin pillow sannan ya dauki wani ya dora a saman fuskarsa.

Na dauki remote din AC dana gani a kusa da shi na fara neman yadda zan rage ta.

"Ka tashi dan Allah, kayi wanka da ruwa mai zafi kar kayi mura"

Ya dauke pillown daya rufe fuskarsa da shi "don't act like you care. Bayan abinda kike yi min jiya"

Na langwabe kai, "kayi hakuri yayana. Nima ba'a son raina hakan ta kasance ba ai na fada maka uzuri na" ya kara hade rai "ba'a son ranki ba? Ba da kafafuwanki kika tashi kika saka hannun ki kika rufe min kofa ba? A matsayi na na ango ace na kwana a falo akan kujera tare da pillow?"

💔 JIDDA 💔Where stories live. Discover now