Page 2
Husna na sauka online, dariya ta kama yi saboda ta san ta kunna Isa,sai da tayi dariya mai Isar ta sannan ta mik'e ta fara da gyara d'akinta sannan ta fita tsakar gida ta fara aikin da ta san ya zamo ita ke yin shi,sai da ta gama gaba d'aya aikin sannan ta shiga wanka a gurguje kasan cewar rana ta fara yi,cikin sauri ta shiga d'akinta ta shirya domin tafiya makaranta,agogo ta kallah k'arfe goma na safiya cikin sauri ta k'arasa shiryawa,fitowa ta yi daga cikin d'akinta da jikkar da kayan karatunta suke ciki,bisa kujera ta aje jikkarta ta nufi kitchen inda ta jiyo motsin mahaifiyarta.
"Mama ba ki k'arasa bane ga shi na makara ina sauri dan ina tsoron ace ba zan samu lecture ba",ta fad'a ta na mai kai hannu gurin bokitin da Maman ta dama masu kunu.
"Ko kin makara Husna ai laifin kine ba zamanki d'aki ki kayi ba", Mamanta ta fad'a ta na mik'o mata filet d'in da ta zubo mata fanke.
"Mama group d'in y'an amana na shiga muka d'an gaisa ", ta fad'a ta na kai kofin kunu bakinta.
Girgiza kai Mamanta ta yi ta ce, "ba ki da magana sai ta group yanzu tunda kin gaisa dasu ai hankalinki ya kwanta koh?"
Murmushi Husna ta yi ta ce, "Mama kin san a duk duniyar WhatsApp babu group d'in da nake jin dad'in shi kuma nake so har a raina kamar shi".
D'agowa da kai Mamanta ta yi ta ce, "in dai ana son aji dogon sharhi gurinki to a tab'a y'an group d'in y'an amana".
Dariya Husna ta yi ta na tauna fanken bakinta sai da ta had'iyeshi kafin ta ce, "Mama group d'in ne ya yi wallahi mutanen da ke ciki suna da bala'in mutunci".
Kallonta Mamanta ta yi yadda ta hak'ik'ance ta na yab'on mutanen da ko had'uwa dasu ba ta tab'a yi ba sai dai a chat d'in, "Husna kiyi sauri ki gama ki tafi kada ki makara saboda ke ba gajiya za kiyi ba".
"To Mama kin san kuwa d'azun sai da na hayak'a Mubarak dashi da Abdul ", Inji Husna.
Kallonta Mamanta ta yi ta ce, "bangane mekike nufi ba?".
Sai da Husna ta cinye fanken da ta sanya ta kora da kunu sannan ta ce, "kwantar da hankalinki Mamana ba wani abu bane kawai dai na ce masu ni ce farin cikin y'an amana ne shine su kai ta musu nasan yanzu sadda zan bud'e data sai naga chapter d'insu kin san Isa ya k'ware da musu".
Bayyanannar ajiyar zuciya Mamanta ta sauke ta ce, "ku dai baku gajiya da shirme".
"Ai Mama dan ma su Umar basu kusa duk su na chan basu tashi bacci ba wani abun ma sai nadawo daga makaranta akwai dirama lokacin kowa ya fito ", Inji Husna.
"Kin san wani abu Mama?", Inji Husna.
Kallonta Mamanta ta yi ta ce, "sai kin fad'a ".
Murmushi Husna ta yi ta ce, "Mama ina rok'on Allah ya nuna man ranar da zamu had'u da y'an amana gaskiya Mama ranar akwai bidiri bured'ed'e".
Dariya Mamanta ta yi ta ce, "Husna ba ki dai rabuwa da shiririta ".
"Kin san Allah dagaske nake Mama ranar zan ji dad'i sosai har a raina kai Allah ya kai damo ga harawa ko be ci ba yai birgima", Inji Husna ta karasa fad'a ta na sa kin wata dariya irin ta duniyar tai maka dad'i.
Kallon Husna mahaifiyarta ta yi cikin ranta ta na jinjina irin soyayyar da yarinyar ta take ma mutanen dake cikin wannan group d'in tun kafin ma su ga junansu, ba ta da maganar yi sai ta group d'in y'an amana.
Dariya Husna ta yi ta aje kofin da ta shanye kunu,wanke hannunta ta yi sannan ta kalli Mamanta ta ce, " Mama na tafi sai na dawo ".
Kud'i Mahaifiyarta ta mik'o mata ta ce, "Allah ya tsare hanya Husna a rink'a kula da mutane kin san wurine da ya had'a jinsin mutane kala-kala dan haka a san irin wad'anda ake mu'amala dasu".
Ansar kud'in Husna ta yi ta ce, "ameen Mama kuma insha Allah Mama zan k'ara kiyayewa na tafi sai na dawo".
"Allah ya maido ki lafiya Husna", Inji Mamanta.
Husna da har ta kai ba kin kofar shiga zauren gidan ta juyo ta ce, "ameen Mamata".
Husna fita daga gidansu Adai-daita sahu ta tare zuwa makaranta,cikin sa'a kuwa ta na zuwa ko zama ba ta yi ba lecturer d'in ya shigo, wata naunauyar ajiyar zuciya ta sauke,cikin sauri ta zauna kusa da k'awarta Mieynart,kallonta Mieynart ta yi su kai ma juna murmushi.
Mahaifiyar Husna ta na ganin yarinyar ta ta fita daga gida,sai ta shiga tunanin wannan wace irin kauna ce ke tsakanin d'iyarta da mutanen wannan group na y'an amana,Allah yasa su ma haka suke jin soyayyarta cikin ransu.
YOU ARE READING
RASHIN ADALCI
ActionLabarine na wata yarinya mai suna Husba da suka hadu a group na whatsapp saboda kyakykyawar alakar da suka kullah har ya kai kowa yasan kowa ana haduwa by face a gaisa zumunci mai karfi ya kullu a tsakaninsu amma daga karshe saboda wani karamin kusk...