Part 3

4 0 0
                                    

*RASHIN ADALCI* 2021

Page 3

Husna su na fitowa daga lecture har sauri take domin ta fiddo wayarta daga cikin jikka,sai da ta dauk'o wayar sannan ta kalli Mieynart dake gefenta ta ce,"Mieynart wai kin jiya kuwa Uncle T yazo gidanmu?".

Kallonta Mieynart ta yi cikin sauri ta ce," dagaske ki ke?wallahi har kin sa gabana ya fad'i to ya aka k'are da yazo".

Murmushi Husna ta yi ta na bud'e datar wayarta ta ce," gaskiya Mieynart tsoronki ya yi yawa meye abun fad'uwar gaba daga na gayamaki Uncle T yazo ina ga ke ya tadda da yazo?Allah ya bani hakuri ni da yazo ya tirke ".

Jan hannun Husna ta yi har sai da suka kai wurin wani benci,zama su kayi sannan Mieynart ta aje jikkarta da handout d'in dake hannunta,kallonta ta maida ga Husna da ke kallon fuskar wayarta hankalinta kwance sai murmushi ta ke faman yi,hassala Mieynart ta yi ta warce wayar daga hannun Husna ta ce,"wai ke Husna meke damunki kin sa hankali ya tashi amma ke sai dannar wayarki kawai kike wannan ai ba hali ba ne me kyau".

Mik'a ma Mieynart hannu husna ta yi ta ce,"ki ban wayata idan har kina so mu yi magana mai muhimmanci dake saboda ina kallon firar da ake group d'in y'an amana ne shiyasa ba wai kuma na sanya masu baki bane saboda ni na had'a maganar shine su ke ta comment akan haka".

Kallon Husna Mieynart ta yi cike da takaici ta ce,"wai ke ba ki da magana sai ta group d'in y'an amana ni fa wallahi har na fara jin haushinsu ke baki da lokacin komai sai nasu ki guji ranar da zasu juya maki baya kin s...".

Cikin sauri Husna ta dad'e bakin Mieynart ta domin Hana ta fad'ar maganar da take shirin fad'a tace,"kada ki ida fad'ar abin da kike so ki fad'a saboda su ba haka suke ba".

Kallonta Mieynart ta yi cikin jin haushi ta ce,"ke Husna kina zama da mutane kuma kina rayuwa da mutane da yawa amma har yanzu kin kasa fahimtar halin mutane a lokacin da suka so juya maka baya".

Gyara zama Husna ta yi sannan ta gyara rik'on jikkarta da ta d'ora saman cinyarta tun lokacin da suka zauna ta ce,"Mieynart nasan me kike hango man amma wad'annan mutanen sun ban-banta da irin mutanen da kike zargi saboda su wad'annan suna da kirki kuma sun san darajar junansu baki ga yadda ake komai a tare ba ko ke in da kin zauna dasu nayi imani za ki ji dad'in zama dasu sosai amma banjin dad'in wannan bahaguwar fahimtar da kike masu a kullum ana so ka rink'a kyautata ma mutane zato ba wai ka munana zato a kansu ba dan Allah ki daina banjin dad'in hakan Allah dagaske nake gayamaki".

Shiru Mieynart ta yi ba tare da ta sake fad'ar komai ba,kallonta Husna ta yi ganin ta k'i kallon inda Husnar take sai kallon mutanen da ke wucewa ta keyi,dafa kafad'ar Mieynart Husna ta yi ta ce,"nasan me kike nuna man Mieynart kuma ina fahimta amma ki sani ba kyau munana zato akan mutane sannan mutanen nan wallahi Mieynart suna da kirki sosai duk wanda ke zaune dasu yana jin dad'in zama dasu sosai kuma ni ban tab'a ganin an samu wani sab'ani garesu ba sai dai kawai fad'an da aka tab'a yi da wadda ta had'a group d'in kuma shima Ina ganin kamar rashin fahimtar junansu da basu yi bane shiyasa har abun ya kai su ga haka".

Cikin sauri Mieynart ta kalli Husna ta ce,"yanzu ina wadda ta had'a group d'in take?".

Husna ta ce,"ta fita daga group d'in tun bayan da suka yi wannan rigimar ".

Murmushi Mieynart ta yi ta ce,"wannan abun kad'ai da yasa ta fita ya isa mai hankali yasa a gane akwai matsala".

Husna kallonta ta maida ga mutanen dake wucewa wasu kuma na hurd'ar gabansu ba tare da ta juyo ba ta ce,"Mieynart wallahi bansan ai nafin matsalar da ta faru ba amma dai wasu sun d'an gayaman wani abu wai saboda ko an ba wata admin ne ke ni dai banji wani cikakken bayani ba".

Murmushi Mieynart ta yi ta ce,"Husna ba wai ina son rabaki da wad'annan mutanen bane amma *gani ga wane ya ishi wane tsoron Allah*dan haka ku shiga hankalinku wallahi".

Ajiyar zuciya Husna ta sauke ta ce,"To Mieynart abin da yasa kika ga ban fita daga group d'in ba kinga bansan meya had'a su ba kinga ai bana shiga tsakaninsu ba amma dai kamar yadda kika fad'a d'in zan yi kokari ina kiyayewa".

"Hakan dai ya kamata saboda kinsan *Banza ba ta kai Zomo kasuwa* duk abin da zai sanya wadda ta had'a group d'in ta bar shi to ba k'aramin abu bane dan haka kuma sai kun yi taka tsan-tsan".

Mik'ewa tsaye Husna ta yi ta rataya jakarta a saman kafad'a ta ce,"insha Allah zan kasance mai lura akan  hakan in naga da matsala sai na fita salin alin nima ki tashi mu tafi masallaci mu yi sallah kada lokaci ya k'ure mana".

Mik'ewa Mieynart ta yi ita ma ta ce,"muje masallacin sai ki gayaman yadda ku kayi da Uncle T d'in kafin lokaci ya k'ure mana".

"To shikenan mu fara zuwa mu sayi ruwa sai mu wuce masallacin dama k'ishirwa nake ji tun d'azun wallahi ",Inji Husna.

Tafiya su kayi domin zuwa sayen ruwa,suna tafiya suna fira a tsakaninsu inda suka had'u da wad'anda suka sani su tsaya su gaisa da haka har suka isa inda ake saida ruwa.

Hussy Saniey

RASHIN ADALCIWhere stories live. Discover now