Open this link to join my WhatsApp Group: https://chat.whatsapp.com/LmbGi3TbkTF2sUurNrJ8zZ
*____________________________________*
*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻
https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association
*____________________________________*
*RASHIN ADALCI 2021*
*NA*
*HUSSY SANIEY*
PAGE 5
Bayan fitowar Husna daga lecture wuri ta samu ta zauna,zamanta da kamar minti biyar Mieynart ta fito tare da wani ɗan Department ɗinsu,hannu Husna ta ɗagama Mieynart saboda ta lura Mieynart ba ta gantaba sai waige-waigen inda za ta hangota take,wanda ke tare da Mieynart ne ya lura da Husna da ke ta ɗagomasu hannu,"Mieynart kin ga Husna chan zaune saman dakali ta na ɗago mana hannu".
Kai tsaye inda ya nuna mata Husna zaune suka nufa,Husna na ganin sun tunkaro inda take sai ta miƙe tsaye ta nufosu,tsayawa su Mieynart su kayi har ta iso inda suke.
"Wai me ku ka tsaya yi a cikin Hall tun ɗazun ina jiran ku,"inji Husna da ta ƙaraso inda suke.
Gyara tsayuwa Sadam ya yi yace,"wannan calculation ɗin muka tsaya har sai da muka gama".
"Mu yi sauri ka da Bus ta cika kuma kun ga sai mun yi tafiyar ƙasa idan ba mu iske ba", Husna ta faɗa ta na kallonsu Mieynart.
"Mu yi sauri gaskiya ni Allah so nake naje gida da wuri akwai inda zanje",inji Mieynart.
"Kun tsaya kuna ta surutu da yanzu mun yi nisa a tafiyar mu",inji Sadam
Jerawa su kayi gaba ɗayansu su na tafiya,fira suke yi nan Husna ke sanar dasu yadda su kayi da ƴan group ɗin su,cikin sigar jan faɗa Sadam ya kalli Husna ya ce,"gaskiya Husna ƴan group ɗinku su na da kirki".
Cikin jin daɗin yabon da aka masu ta ce,"dan ma ba ka cikin group ɗin Allah da sai kaji kamar ai ta zama idan ana fira".
"Gaskiya Husna har naji ina son shiga group ɗin nan saboda na ga wacce wainar ake toyawa",inji Sadam.
Cikin matsanancin jin daɗi Husna ta dakata da tafiyar da take ta ce,"dagaske kana son shiga na bada lambar wayarka a sanya ka a group ɗin".
Murmushi Sadam ya yi saboda ganin yadda Husna ta ɗauki maganar da muhimmanci ya ce,"wasa nake maki Husna kin san ni bana son shiga cikin kowane group saboda matsalolin da ke faruwa a ciki".
Tun kafin ya ƙarasa maganarshi Husna ke girgiza kai sannan ta ce,"wallahi su ba haka suke ba duk wanda ya zauna dasu zai so gobe ma ya zauna dasu su na da mutunci sosai Babban daɗin guda kuma shine sun san darajar mutane ban taɓa ganin sun wulaƙanta wani ba dan haka in dai kana son shiga wallahi na bada lambarka kawai idan aka sanya ka sai kaji daɗin zama dasu fiye ma da yadda nake faɗa maka".
Dariya Sadam ya yi sannan ya ce,"kar ki damu Husna tun da kina ciki ai zan rinƙa jin labarin su hakan ma yana sanyani nishaɗi aminiyar",ya juya wurin Mieynart da ke ta faman ɓoye dariyarta dan ka da Husna ta gani amma ka sa ɓoyuwa dariyar ta yi har sai da ta saketa a fili.
Harararta Husna ta yi ta ce,"kin dai ji haushin gulma wallahi yanzu meye abin dariya anan toh?".
Girgiza kai Mieynart ta yi tare da haɗiye dariyar da take yi sannan ta harari Husna ta ce,"dan kin ga ina dariya shikenan kuma babu da wanda nake sai ke kenan ko Hajiyata?".Bugu Husna ta kai ma Mieynart ta ce,"idan ba dani kike ba to da wa kike nan in ba ni dake magana ba kuma ai nasan akan me kike man dariya banza ai ban ce ki bada lambarki a sanya ki ba bare ki kama yi man wannan banzar dariyar ta ki", Husna ta ƙarasa faɗa a hassale.
Ganin yadda Husna ta hassala ya sanya Mieynart ta haɗiye dariyarta lokaci guda,matsowa ta yi kusa da Husna sannan ta da fa ma Husna kafaɗa ta ce,"meye abin fushi kuma Ƙawata daga magana amma tunda ba ki so shikenan na yi shiru".
Sadam ma matsowa ya yi inda suke shima tare da ƙoƙarin haɗiye ta shi dariyar ya ce,"gaskiya Mieynart ba ki kyauta ba meye abin dariya nan bayan ma ba dake ake maganar ba dan dai k...",saurin dakatawa da maganar shi ya yi saboda wata dariya da ta taho ma shi ya yi,dan lura da yadda Husna ke ta ƙara murtuke fuska.
"Nagode maku sosai ni dai ku ka maida mahaukaciyar ƙarfi da yaji ko dan kun ga ina baku labari shine har abin ya zama abin tsokana ko bakomi nagaode laifinane da nake gayamaku duk wani abu da ya danganceni",ta ida faɗar maganar a matuƙar hassale.
Jinin jikinsu su ka sha saboda ganin yadda take maganar acikin fushi,dan haka sai suka koma bata haƙuri,ko saurarensu Husna ba ta yi ba ta cigaba da tafiya.
Bayanta su ka biyo babu mai magana a tsakanin su saboda ganin yadda Husna ta hassala,nan wurin Bus stop su ka tsaya dan jiran Bus.
*Hussy Saniey*.🥰

YOU ARE READING
RASHIN ADALCI
ActionLabarine na wata yarinya mai suna Husba da suka hadu a group na whatsapp saboda kyakykyawar alakar da suka kullah har ya kai kowa yasan kowa ana haduwa by face a gaisa zumunci mai karfi ya kullu a tsakaninsu amma daga karshe saboda wani karamin kusk...