Bayan fitowarsu Husna daga masallaci,zama su ka yi gaban Hall d'in da zasu yi lecture,suna zama Mieynart ta kalli Husna ta ce,"ba ki gayaman yadda ku kayi da Uncle T ba".
Murmushi Husna ta saki kafin ta juyo ta fuskanci Mieynart ta ce,"K'awata Uncle T fa ya fad'a tarkon ki".
Zaro idanuwanta Mieynart ta yi ta dafe kirji ta ce,"K'awata ba mu irin wannan wasan fad'a man gaskiya dan Allah ".
Hannunta Husna ta rik'e ta ce,"dan Allah ji yadda kika koma cikin mintina k'alilan sai kace wadda aka aiko ma da sak'on mutuwa".
Ajiyar zuciya Mieynart ta sauke ta ce,"wallahi abin ne ya ban mamaki mutumin da girman kai da miskilanci su kai ma shi yawa shine har za ki iya fad'ar ya fad'a tarkona wai shin ma meya gayamaki da har kike wannan maganar".
Dariya Husna ta saki cikin son tsokanar Mieynart ta ce,"ya fad'a man ya lura kina son shi shiyasa zai tausaya maki ya aureki".
Wata irin zabura da Mieynart ta yi har sai da ta tsorata Husna ta ce,"na shiga ukku K'awata k'aryata ta k'are na gama yawo dagaske haka ya fad'a maki?"ta k'arasa fad'a idanuwanta cike da hawaye wanda a ko wane lokaci suna iya zubar da ruwa.
Dariya Husna ta k'ara kwashewa da ita sannan ta mik'e ta rik'o hannun Mieynart ta ce,dallah ni har kin ban tsoro wallahi ji yadda fuskarki ta koma gaskiya ke ba k'aramar matsoraciya ba ce ".
"Dan Allah ki fad'a man gaskiya Husna wallahi hankalina ya tashi sosai idan ya gane ina son shi ai babu k'ima ni kuwa kin san duk abin da zai sanya na rasa k'imata na tsane shi,"Mieynart ta fad'a ta koma inda ta tashi ta zauna tare da share gumin saman fuskarta.Kallonta Husna ta yi ta sake fashewa da dariya ta ce,"kin ganki kuwa kin zama wata kalar tausayi ina ma nayi maki video dan na rink'a kallo duk in na tuna".
"Wallahi ba kiji dad'in halinki ba Husna amma da ni kike zancen zan rama,"Mieynart ta fad'a tare da d'aukar jikkarta ta nufi hanyar shiga cikin Hall d'in da zasu yi lecture dan ta lura Husna iskanci take ji shiyasa take mata haka da ta cigaba da zama tana kunnata ga ra ta koma cikin Hall d'in ta zauna ita d'aya yafi mata sauki kujerar baya ta samu ta zauna dan nanne babu cinkison mutane da yawa.
Husna ganin Mieynart ta shige Hall,sai ta kama dariya ta ce,"zan fad'a maki gaskiyar yadda muka yi amma sai na gama wana ki yarinya".
Wayarta ta fiddo daga cikin jikka,Data ta bud'e sai da sak'onnin suka gama shigowa sannan ta rink'a binsu d'aya bayan d'aya ta na mai da masu da amsa,sai da ta gama dasu sannan ta shiga group d'in y'an amana.
Kamar yadda ta tsammata hakance ta kasance kuwa duk wanda ya shigo yaga firarsu sai ya d'ora tashi a sama,wani sak'one da d'aya daga cikin admin d'in gidan ya turo shine yaja ra'ayinta inda yake cewa gaskiya ne maganarta ita ce farin cikin y'an amana.
Amsa ta bashi da fad'ar,"yauwa Abba fad'a masu dai dan haka su rink'a lallabani".
Sak'on na tafiya kamar jira suke sai aka fara comment,sak'on Abdul ya fara shigowa wayarta inda ya ce,"dallah matsa malama in ba damun mu da kike yi ba mekike mana da har za ki wani ce kece farin cikin y'an amana,"daga k'asan sak'on sai ya turo sticker d'in dake nuna alamar an harari mutum.
Kafin ta ba shi amsa sai ga Hadiza Muhammad(ita ce wadda Husna ke cema kakarta)ta turo sak'on a in da take cewa,"wannan ka dai fad'a san ranka amma ai kowa yasan jikata ita ce farin cikin mutanen gidan nan.
Dariya Husna ta tura sannan ta ce,"yauwa My Kakus fad'a masu dai ki suna kishine da son da ake nunaman a gidan?".
Ibrahim da shigowar shi gidan kenan ya ce,"gaskiya K'anwata (Hadiza yake nufi)ke kike sa yarinyar nan ta na abin da ta gadama ya kamata ki rink'a yi mata fad'a".
"Haba Yaya me jikar tawa ta yi ne daga ta fad'i gaskiya ai dagaske ita ce farin cikin mutanen gidan nan,"Hadiza Muhammad ta fad'a.
"Kai gaskiya ni y'ar gatace nayi abin da nake so a cikin gidan nan saboda ina da Kakata mai sona da son ganin farin cikinta,"Husna ta fad'a ta na k'ara sakin dariyar nishad'i.
"Zan kama kine yarinya jikinki zai gayamaki,"Inji Ibrahim yake fad'a ma Husna.
Sticker mai alamar kuka Husna ta tura ta ce,My Kakus kinji abin da yake fad'a koh?".
"Haba Yaya dan Allah ka kyaleman jikata ta yi abin da take so,"Inji Hadiza Muhammad.
"Yauwa My Kakus shiyasa nake sonki saboda kina son farin cikina,"Inji Husna.
"K'anwata wannan jikar taki ta raina mutane ki barni nayi maganinta kawai,"Inji Ibrahim.
"Yaya dan Allah ka kyaleman jikata naga ai wasane take yi ba gashi ba har kun fito da kun bar gidan shiru,"Inji Hadiza Muhammad.
"Hmmm baza ki gane bane K'anwata amma taci albarkacinki," Inji Ibrahim.
"Yauwa nagode Yaya ga amanarta nan na bar maka zan fita naje unguwa,"Inji Hadiza Muhammad.
"Wallahi ban so My Kakus nima lecture zan shiga ki bar ni wurinshi dan ya rink'a cin zalin d'ina in yaga ba ki nan koh?"Inji Husna.
"Kin taimaki kanki yarinya da kin yaba ma aya zak'inta a hannuna," Inji Ibrahim.
"Kai Yaya! Amma shikenan tunda ita ma lecture za ta shiga sai anjimanku ni na tafi,"
Inji Hadiza Muhammad."Malam Iroro na bar maka tsaron gidan salon ka tafi yawo ka barshi ba kowa,"Husna ta fad'a daga k'asa ta sanya sticker irinta alamar an yi ma mutum gwalo.
"Da ki tsaya mana yarinya da kin gane Allah d'ayane yarinya,"Inji Ibrahim.
Husna tunda ta fad'a mashi magana bata k'a fad'ar komai ba sai dariya da ta kamayi,rufe Data ta yi ta nufi Hall.

YOU ARE READING
RASHIN ADALCI
AzioneLabarine na wata yarinya mai suna Husba da suka hadu a group na whatsapp saboda kyakykyawar alakar da suka kullah har ya kai kowa yasan kowa ana haduwa by face a gaisa zumunci mai karfi ya kullu a tsakaninsu amma daga karshe saboda wani karamin kusk...