Part 6

19 1 0
                                    

*____________________________________*

*🌈🇰AINUWA 🇼RITER'S✍🏼*
*🇦SSOCIATION🤝🏻*
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation

*_domin shiga shafin mu na Bakandamiya danna nan_*👇🏻

https://bakandamiya.com/group/71/Kainuwa-writers-association

*____________________________________*

*RASHIN ADALCI 2021*

*NA*

*HUSSY SANIEY*

PAGE 6

Shiru zaman ya kasance a tsakaninsu,babu wanda ke da ƙwarin guiwar yin wata fira,zaman minti goma sai ga Bus ta zo,su na shiga cikin Bus ɗin Husna ta chanza kujerar zama,da kallo su ka bi ta dashi saboda abin da bai taɓa faruwa a tsakaninsu ba,duk rintsi wuri ɗaya suke zama amma yau ga shi Husna ta raba masu wurin zama.
Husna na kallon yadda su ke bin ta da kallo, ɗauke kanta ta yi kamar ba ta san suna yi ba,a haka tafiyar ta kasance babu daɗi,kowa da abin da yake saƙawa a cikin zuciyarsa.
Ko da aka zo inda suke sauka,Bus na tsayawa Husna ce farkon fita,bayanta su Mieynart suka bi,lokacin da suka fito har ta tsaida Keke napep.
Ji ta yi an riƙe mata Abaya ta baya,juyowa ta yi suka haɗa idanuwa da Mieynart,ɗaure fuska Husna ta ƙara yi ta ce,"sakeni zan wuce!"

Murmushi Mieynart ta yi,"Husna ban taɓa ganin haka a wurinki ba saboda haka kiyi haƙuri hakan bazata ƙara faruwa ba insha Allah."
Girgiza kai Husna ta yi ta ce,"bakomi ya wuce sai Allah ya kaimu gobe."
Kafin Mieynart ta ce wani abu har Husna ta shige cikin keke napep ɗin,ta na shiga mai keke napep yaja suka tafi,sai da suka ɓace sannan Mieynart ta kalli Sadam ta ce,"tun da nake da Husna ba ta taɓa nunaman taji haushin abu ba irin yau,gsky bansan wannan wace irin ƙauna ba ce take ma waɗannan bayin Allah ba."
Cikin mamaki Sadam ya ce,"ni kaina abin nan ya matuƙar ɗaure man kai,wai Husna ce ta iya nuna mana ɓacin ranta saboda mun kushe wasu!"
Mieynart ta riƙe haba ta ce,"abin da yafi ɗaure man kan kenan,fatana dai Allah ya sanya yadda take son su haka su ma suke mata irin wannan son."
Gyara tsayuwa Sadam ya yi tare da ɗaga ma wani mai mashin hannu,duban shi ya maido ga Mieynart ya ce,"ameen dan gaskiya abin ya ban mamaki sosai."
Tsayuwar mai mashin gabansu shi ya hana Mieynart magana, Sadam ya kalli Mieynart dake tsaye amma da gani kasan ba ta cikin yanayi mai daɗi ya ce,"Mieynart idan naje gida zamu yi waya akan wannan case ɗin kar ki damu kinji koh?"
Numfashi Mieynart ta sauke ta ce,"Sadam dagaske hankali na ya tashi saboda Husna duk yadda kake ganinta ba ta da haƙuri to wallahi ta na da kawaici ba abu kaɗan ke sanyawa ta nuna ɓacin ranta ba."
Hawan mashin Sadam ya yi sai da ya zauna sosai sannan ya ce,"kar ki damu Mieynart zamu yi magana idan na koma gida ai dole mu tabbatar Husna ta sauko daga fushin nan saboda wallahi yau ban ji daɗin yadda muka rabu ba."
Gyara riƙon jikka Mieynart ta yi ta ce,"nima abin da yafi ɗaga man hankali kenan amma insha Allah idan ta kama har gida zan taddata sai na bata haƙurin kaje idan mun koma mun yi waya sai anjima Allah ya kiyaye hanya."
Littafin da ke hannun shi ya ɗora bisa cinya,ya kalli Mieynart ya ce,"ki bari idan naje gidan duk yadda ta kama sai ayi kawai kinji kin ga napep chan kije ki hau ki gaida Mama."
Bayan wucewar Sadam babu daɗewa ta samu Keke napep,ta tafi gidansu lokacin har an kusa fara kiran sallar magrib.
**************
Husna na isa ƙofar gidansu,mai Keke napep ɗin ta sallama sannan ta shiga cikin gidansu,da sallama ta shiga,Mama na zaune ta na ɗaurin kunun Aya,kallo ɗaya Mama ta yi ma Husna ta san akwai matsala a tattare da Husnar.
Ganin irin kallon da Mama ke bin ta da shi ya sanya Husna washe baki ta ce,"Mama sannu da aiki na dawo."
Cikin kallon tuhuma Mama ta ce,"yauwa lafiyar ki ƙlau kuwa Husna! kin ga yadda kika yi?"
Cikin ƙoƙarin ɓoye damuwarta, Husna ta yafa ma fuskarta murmushin ƙarfin hali ta ce,"lafiya lau nake Mama kawai tsabar gajiyace kawai ta maidani haka kamar marar lafiya amma lafiya lau nake babu wani abu Mama."
Ba dan Mama ta yadda ba ta ce,"ki je ki ɗan watsa ruwa ki zo ki ci abinci nasan dai kina jin yunwa?"
Murmushi Husna ta ɗan yi duk don son ɓoye damuwarta ta ce,"zan dai watsa ruwa Mama amma ba na jin yunwa na ci abinci a makaranta Mieynart ta zo mana da shi."
Kallonta kawai Mama ta tsaya tana yi saboda zai yi wuya Husna ta dawo daga makaranta ba ta ci abinci ba,wani lokacin har janta ake ace an manta ba'a aje mata abincin ba,ganin irin kallon da Mama ke bin ta da shi ya sanya kawai ta shige ɗaki,dan tsab Mama na iya gano abin da take ƙoƙarin ɓoyewa,kuma ko kaɗan bata san hakan ta kasance.


Hussy Saniey.🥰

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jun 26, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

RASHIN ADALCIWhere stories live. Discover now