_*MIN QALB*_
_Mamuhgee__Bismillahir rahmanirraheem_
Qarar waqar sani sabulu ce ta _duniya wandon roba_ ta cika gidan ta karade wane daki da saqo na gidan sbd qarar muryar radio din da aka Kai qarshe gaba daya,
Hankalinsa kwance yake yana Shan waqarsa Yana sakace haqoransa da tsinke
Daka gansa zakasan babu Abinda ya damesa.Dukkanin mutanen gidan 'dai 'dai suka ringa fitowa rayukansu a 'bace da takaicinsa na kullum Wanda inda sabo sun Saba da dabi'arsa ta tayardasu kullum da sautin radionsa da muryarsa Bata qasa
Gashi bamai ikon mgn 'yar gaban goshinsa da shaqiyin dansa suce ba Wanda ya isa
Amma rshin arzikinsu babu kalar Wanda basa fafatawa dashi wanda kallo daya zakayi musu kasan su din abin mamaki ne,
Rayuwarsu abin kallo ce sbd sudin abin mamakine.Yana ganin mutanen gidan sunfara fitowa ya sake dauke Kai sama Yana jiran yaji wani Mai shafaffun Mai akai ne zaiyi mgn ya sauke Masa masifar dake cinsa ta takaicin iyami daya kwana dashi na biya Masa bashin dabaiyi niyar biyaba yanzu da kudinda yaci burin canza radio dashi na AMATULLAH da USI.
Cikin bacci qarar radio din ke shigarta Yana damunta,
Juya kwanciyarta tayi tana toshe kunnuwanta da pillow Amma
Sam qarar Bata daina shiga kunnuwanta ba.
Tsoki tasaki ahankali tana cewa'Kawuuuu.
Saidata sake rintsawa ta juya kwanciyarta tsawon minti goma Amma Sam baccin ya gagara sbd qarar radio din dole ta yaye lullubinta ta miqe zaune tana miqa tana cewa'
Allah yasa yanda natashi yau cikin qoshin lfy yasa yau ranar sa'atace,
Allah yasa yauma na hadu da irin hajiyar Dana hadu da ita jiya nayi mata kukan tausayi tabani kudinda zanyo......Kasa qarasawa tayi tareda zaro ido sbd USI data tuno
Da sauri ta dauki hularta dake kan katifarta ta sanya akai tareda zura silifas cikin sauri tana fitowa kota kan kawun batabi ba sbd daga yanayin waqar dayake sha a radio din ta fahimci yau ba sauqi a qule yake Wanda zai saukewa haushin yake nema shiyasa ba Wanda yace Masa uffan gudun masifa.Bokiti ta dauka ta nufi fanfon dake can kusada qofar shigowa cikin gidan
Tana zuwa ta tararda wani bokitin yakusa cika
Ta gefen ido ta kalli maman junior dake tsaye alamar natane take jiran yacika hancinta na asalin yorbawa sai cika yakeyi Yana fidda iska sbd ita kullum a shirye take da duk inda masifa zata fado ta hauyi.Shahada tayi ta rintse ido cikin ranta tace'
Bayina bane Allah ne ya qaddaro bazanbi layin jiraba
Ta sunkucesa da gudu ta fada bayin gidan daidai salamatu zata fito bayin tsoron ganin mutum a fujajan yayo ciki yasa ta zame ta Fadi qofar bayin
Aikuwa itakam amah Bata tsaya wata wata ba ta rufo bayin tana cewa'Haka Allah yaso anty salamatu bayina bane Allah ne ya qaddaro zaki Fadi,
Kema maman junior yi hkr Allah ne ya qaddara da ruwanki zanyi wanka bayina bane.Cikin wani irin tsananin baqin ciki da takaici salamatu ke kallon kanta zaune cikin ruwan qazantar qofar bayin bayan tayo wanka.,
Wani irin tiririn masifa zuciyarta keyi ta miqe amatuqar zuciye daidai isowar maman junior itama jikinta harwani mazarin masifa yakeyi tana cewa'
Wlh yau gidan Nan saidai kowa alaji landlord yakore agidan Nan Amma sai anyi balain da ko kawu fatihu duk masifarsa bazai hanani yiwa yarinyar Nan dukan tashi Kisha ruwan gishiri ba.
Kallonta salamatu tayi a harziqe tana cewa'
Saiki sameta cikin bayin tunda akanki aka Fara sauke masifa duniya
Kinzo kina qaramin haushi
Idan ke duka zaki mata wlh ni yau saina dauko motar Yan Banga a gidan Nan kowa yaci ubansa tunda Nagano kowane shege a gidan Nan ya rainani tunda anga Ina zaman kaina.