_*MIN QALB*_
_Mamuhgee_2
Bazai iya ganiba
sunaji suna gani qaton saurayin yake kokarin keta rayuwarta dabata gama sanin ciwon kantaba,
Ita kukan datakeyi dannewar dayayi Mata akan duwatsu suna cin jikinta
Shikuma Usman kukan zabar dayasha yake tunowa itace zaayiwa amatu Wanda sanadin hakan sunzama 6arayi dole da qarfi da yaji.Qoqrin bude qafafuwanta qaton keyi
Usman yayi wani yunkuri tareda kama hannun Wanda ke maqure dashi ya sakar Masa mugun cizo Mai qarfi da haqoransa dasuka gama bushewa da dau'da.A gigice yasakesa Yana yarfe hannu sbd azabar cizon.
Wani qaton dustsi Usman din yadauka baiyi wata wata ba ya buga akan qaton dake kan amatu
Take ya sulale gefe kansa na tartsin jini sosai ko ihu daya beyiba ya zube agurin Yana wani irin Shure Shure.Suna ganin hakan wani irin tsoro yashigesu da gudu ya kamo hannun amatu Yana cewa'"
Zo mu gudu amatu.
A firgice dayan ya riqesu Yana cewa'"
Kun kasheshi....a kidime yake fadar hakan cikin tsananin tsoron ganin abokinsa na Shure shuren mutuwa.
Qoqarin jansu yakeyi Yana cewa'"
Wlh police zan kaiku Kun kashesa,
Bazaki guduba ku barni cikin masifa akamani.Jansu yakeyi da qarfi cikin firgici da tashin hankali suna kuka sosai suna rokonsa ya sakesu Amma Shima a rude yake kansa zai wanke kota halin Yaya.
Irin kukan dasukeyi Basu taba yinsaba arayuwarsu sbd jin wani ya mutu sbd su Kuma Suma kashesu dayan sukaji yanacewa zaayi.
Sosai suke kuka suna rokonsa ya sakesu Amma ko jinsu bayayi Dan Shima kusan kukan yakeyi na tsoro da firgici.
Wata qatuwar gora daga bayansu aka kwadawa qaton a tsakiyar Kai
Ya tsaya cak tareda sakin hannuwansu Yana qoqarin juyawa yaga ko waye ya yanke jiki yafadi jini nafita a qeyar kansa.Jikinsu na rawa cikin tsananin tsoro da firgici suka juyo suna qanqame hannuwan junansu tareda ja baya suna kallon qaton dashima yake Shure Shure.
Cikin sauri megadin makarantar ya matso gabansu tareda riqo hannuwansu yasaka musu kudi Yana waige waige Yace"
Kuyi gudu sosai kuje can qasan layin gaban kasuwar baya akwai makarantar almajirai ku shige cikinsu ku kwanta ku boye zanzo idan ankwana biyu
Kuyi sauri karku taba dawowa tanan
Kuyi sauri kuje..Kallonsa sukeyi suna sake sakin sabon kuka sbd sunqara firgicewa da Abinda yake fada,
Yaturasu Yana cewa'"
Kuje kuje kuyi sauri karku dawo.
Gudu suka Fara suna waiwayensa sbd akaro na farko da wani ya taimakesu arayuwarsu.
Tun suna waiwayensa harsuka bace suna gudu cikin Daren gashi yace karsu hau titi subi kwana kwana.
Koda suka Kai makarantar almajiran dare yayi sosai gashi karnika sai haushi suke musu duk inda sukabi.
Suna kaiwa bakin makarantar suka tsaya suna rarraba idon Ina zasu boye sbd almajiran gasunan kwance birjik a fili kowa da matacciyar tabarmarsa wasu Kuma da kwalaye wasuma hakanan suke kwance a qasa ga cinnakai da qwari da komai Amma ba ruwansu kwance suke abinsu suna bacci.
Hanunta usman yakama suka qarasa can qarshe yacire matacciyar rigar jikinsa data gama yagewa ta mutu ya shimfida musu suka kwanta kowannensu jikinsa na rawa numfashinsu na fita da sauri sbd tsananin tsoron dasuke ciki.
Asubar fari dukkanin almajiran aka tadasu suyi sallah
Wanda wannan shine karo na farko dasuka tabayin sallah Shima Suma dai sunyi yanda sukaga kowa nayi gurin bin Abinda malam yayi.