*_MIN QALB_*
_Mamuhgee_1
Qoqarin durqusawa takeyi ta dauki busashen biredin dataga wani yaro yazo ya zubar a babbar bolar bakin anguwar wadda za'a Kira da qaramar kasuwa sbd hargitsi da cunkushewar anguwar da manya da qananan kwatocinda suke cike taf da ruwa da ledoji tareda qananan abinci na wanke wanke dasuke biyowa,
Daukar biredin tayi tana kakkabewa tareda kaiwa bakinta daya gama bushewa yayi fari fat harya Fara yayyankewa alamar ko yawun bakinta sun gama bushewa ta gutsura kadan ta Dan tauna taji zai shiga
Da sauri ta qarasa turasa cikin bakin tana taunawa da sauri jikinta na rawa tareda hanjinta dasuke qugin jin wani abu ya saukar musu bayan kwanaki dasuka Dan dauka a na'de.Ganin wani almajiri yayo gurin Yana kallon biredin a yunwace Shima Dan ko gabansa baya kallo idonsa nakan biredin ko kyaftawa bayayi yasa tayi saurin miqewa tana qara tura biredin cikin bakinta da sauri sauri tana kallon almajirin karya iso gurinta Bata cinyeba ya kwace sbd wannan shine Abinda yake faruwa a bolar qwacewa daga marasa qarfi Wanda a duniyarma hakane duk me qarfi shike qwace Abinda yakeso gurin masashi,
Batada uwa batada uba,
Batasan kowa aduniyaba Wanda zata ce nata ne,
Ita aduniyarma gaba daya batasan komaiba face yawon bola da tsince tsince.Almajirin na isowa gurinta yayi wuf da qarfi ya qwace biredin hannuwansa na rawa Shima yakai bakinsa yanaci da sauri sauri Yana hadiyewa ko taunawa bayayi sbd sauri yakai bakinsa.
Kallonsa takeyi tana hawaye tana lashe sauran Dan gari garin biredin dake hannunta tareda uwar dau'dar dake tafin hannuwan nata dasuka sauya kala sbd dau'da.
Tana kallo ya cinye biredin ya dago Yana kallon hannuwanta ko zaiga wani abin naci sbd yunwar dakeci hanjinsa yakai ko numfashi baya iyayi ko mushe yagani zai iya ci sbd qarfinsa daya gama qarewa gurin yawon bara.
Ganin yanawa hannuwanta kallon yunwa yasa ta juya ta tafiyarta zuwa tsakiyar bolar tana bincikawa ko zata Kuma samun wani abin.
Yarinyace qarama sosai Yar kimanin shekaru bakwai saidai yunwa da wahala Sunsa ta matse sosai kamar Yar shekaru shida,
Dau'da tasa fatarta takoma baqiqirin ko tantance asalin kalar fatarta ba'ayi
Ga gashin kanta daya gama tsinkewa sbd dau'da da zamansa a bude.Gangarawa tayi yafito cikin bolar tana qoqarin bude gwangwanin data samu cikin bolar fuskarta na nuna 'dokin son ganin me tasamo.
Bakin shagon alhajiyat me abincin bakin titin ta zauna daga can gefe inda ake Mata wanke wanke ta faki idanuwansu ta dauki wata matacciyar butar tsarkinsu ta Dora baki tafara kwankwadar ruwan da sauri sauri wani sanyin rahama na sauka cikin hanjinta ita batamasan wani abu qazantar ruwanba burinta dai su sauka a cikinta.
Fizge butar akayi da qarfi tareda jefarwa cikin masifa matar tasaka qafa ta tureta gefe tana cewa'"
Wannan yarinya wlh anyi muguwar mayya,
Yarinya saikace kafira ayita korarki Amma kullum saikin zo.Kallon matar takeyi tanason yin kuka Amma Sam takasa sbd tunda ta taso batasan wani abu waishi so,qauna,kulawa ba ko gata bare tasan zafin rashinsu hartayi kuka.
Tunda tafara wayo daga ita sai kakarta kurma suke rayuwa a wani mataccen kangon shaguna wadda ita a wayonta batasan shin kakartace kokuma mahaifiyarta
Itadai tasan itace komanta gashi kurma ce bataji Bata iya mgn ga tsufa ahaka suke rayuwar Bara da yawon bola neman rubabben abincinda zasuci idan dare yayi sukoma shagunan dasuke kwana su kwanta duk da Basu kadai bane shagunan duk mabaratane da nakasashshi,Koda iya tsohuwa tayi kwanaki kusan ashirin a kwance batada lfy tana gani tana kalla 'yarinyar ke fita yawon bola da bara tana ciyo abinci dame kyau da Mara kyau,
Wani lokacin ma idan ta ciyo Mara lafiya tana gani zatazo tayita amai da zawo Amma ahaka take sake fitarta tasake samowa Koda a bolar ne taci abinta,
Ciwo da yunwa da tausayin ganinsu ahaka yasa jikinta yin tsanani matuqa ahaka ta rasu batareda jamaa suna ankaraba ita Kuma batada wayon dazatasan meke faruwaba ahaka gawar tayi kwana biyu da yini take layin yafara daukar wani mugun wari wanda yasa sukasan akwai gawa.