*_MIN QALB 5_*
_Mamuhgee_##Zafafa biyar#pay@ 09033181070 or 09032345899
Usi ne yafara ankarewa dashi yaga yanda qarara idanuwansa da fuskarsa suka nuna tsananin qyama da takaicin Abinda idanuwansa suka gane Masa Nan ya fahimci cewar yarigada ya ganta yayi saurin dauke idanuwansa dga kallonsa yayi sbd tsananin kwarjini da cika masa ido da yayi yai saurin yin qasa da murya Yana cewa'"
Amah kiyi saurin barin Nan kokuma ki maida kudin.
Batareda ta fahimci Abinda yafadaba ta kallesa tana cewa'' oya yi sauri mutafi nagama ramawa kura aniyarta anan,
Insfector Garba Kuma zaizo yasameni a gida nasani acan zan fanshe wannan tozarcin dayamin agaban baqonsu da ko kallo bai isheniba bare na tsaya harsu gama kulasaba kafin su dawo kanmu.Gaba tayi tana zuge zip din Jakarta data saka kudin usi na biyeda ita Yana satar waiwayen baqon dake bayansu fuskarsa a hade ko inda suke bai kallaba ua nufi motarsa Yana duba agogonsa dake nuna Masa lokacin ganawarsa da mahaifinsu yayi gashi shi mutum ne dayake aiki da lokaci komai lokacinsa yake ware Masa sbd tsari dayayiwa rayuwarsa.
Amah ko takan babbar motarsa batabi ba sbd gama quluwa datayi da Abinda Garba yayi Mata.
Usman kuwa suna fitowa tafiya kadan sukayi yaja ya tsaya jikin wata bishiya Yana sauke ajiyar zuciya ya zauna Yana jingina kansa jikin icen ya sake sauke numfashi ya kalleta yana sakin 'yar dariya kamar Babu rauni da tsamin duka a jikinsa yace"
Amah kina ganin akwai ranarda zamuyi rayuwa kamar sauran mutane masu daraja???
murmushi itama ta saki tana kallonsa cikin kulawa da rashin nuna damuwa kafin ta bude Jakarta ta shafo kudin dake ciki tana kallonsu tace"
Bama buqatar wani rayuwa ko gatan daya wuce muyi rayuwarmu ayanda take,
Karka saka wani Rai a wani rayuwan bayan kasan mu din asalin 'yayan bola ne,
Bamuda wani rayuwa bayan Wanda muke ciki a yanxu.dariya Usi yayi hadi da miqewa tsaye yafara tafiya yana Dan dingyashi saboda raunin da akai masa a kafa sosai yake masa zugi
cikin sake quluwa Amah tabi shi da idanuwa tana tunano irin kalar rashin arzikinda zatayiwa Garba.Tafiya sukeyi suna firarsu cikin nishadi sbd su Sam Babu Abinda suke ajiyewa arai ya damesu.
Suna shiga gidan da Aunty Salamatu suka fara cin karo aikuwa ta soma sakin numfarfashin masifa dan Sam bata manta dibar albarkan da Aman tayi Mata ba kafin fitarta,
Amah na ganin hakan ta fuske ko kallonta batayi ba ma tai wucewarta zuwa dakinsu jakarta ta ajiye hadi da cire karamin hijab dinta ta fito ta nufi qofar dakinsu kawu ta tararda
Usi zaune tare da Kawu wanda ke tambayar Usin" wane shegen kurtun Dan sandan ne yayi maka wannan ta'asar???Qwafa yayi Yana taba qafarsa dake Masa zogi yace"
Ai kawu idona idon Sargent salisu saina saka anyi Masa zanen yarbawa har a goshi da qeya,
Shikuma insfector Garba duk Yakuma zuwa gidan Nan gurin amah saina Masa askin kwalba.
Cikin takaici kawu yace"
Shi garban me kama da an sulala naman Kai shine yasa aka maka wannan dukan? Kokuwa shi Sargent salisu din dayafi kama da danyar alala yayi gaban kansa yayima wannan dukan kamar wanda yayi kisa¿
Maman basiru dake kusa dasu tana aikin wanke rishonta ta tabe baki tana cewa'"
To meya raba dambe da fada¿
Tsuke fuska kawu yayi Yana kallon iyami dake fitowa daki daukeda robar garin tuwo dazata gyara yace"
Iyami kinajin matar nan nafadamin mgn bazakiyi Mata dukanda mijinta ba mijintaba ko yayanta bazasu ganetaba,
Waini iyami kodai auren dole ne mukayi?da kike wulaqantani ne kokuwa talauci haukane?