Page 1

890 24 3
                                    

*_Abinda Ke Cikin Zuciya_*

©®_Hafsat Rano_

Free page (1)

****Yara ne yan kasa da shekara biyar masu yawan gaske cike da biharabar babban gidan marayun, kowanne na harkar gaban sa wanda mafiya yawancin su wasa suke daidai da karancin shekarun su. Kasancewar yau asabar ce babu karatu sai na yamma, yasa harabar ta zama iya yaran ne kawai inda manyan cikin su ke chan baya suna wanki da gyare gyaren da ya zama kamar al'adar gidan a kowanne mako.
Zaune yake jikin ginin dakunan kwanan su ya tattare kafafuwan sa sama yana kallon su, yaro ne shi mara son hayaniya da rashin ji irin na sauran sa'oin sa, mafiya yawancin lokuta zaka ganshi zaune ya zura musu ido kawai yana kallon su ba tare da ya shiga wasan ba. Duk kuwa yadda Maman Yara take kokarin ganin ya sake a cikin sauran yara sam yaki, sai dai duk da haka wayon sa daban ne, yana da kaifin basira da saurin daukar abu, kokarin sa har mamaki yake basu, duk wani abu da anyi shi yake zama daram akan sa. Babban abinda ya zamar masa jiki shine tausayi, duk da rashin son hayaniyar sa, amma yana da mugun tausayi da kaunar duk wani yaro da yake cikin gidan nan.
A hankali gate din gidan ya shiga budewa,chak yaran suka tsaya da wasa suka zubawa kofar ido cikin son ganin me zai faru. Mota ce karama ta shigo cikin harabar gidan, ta samu gefe ta tsaya, da sauri duk yaran sukayi wajen motar da murnar su, mikewa yayi shima yana murmushi ya nufi motar har da dan gudun sa, kafin ya karasa sun fito, wani mutum ne da a kalla zai yi shekara arba'in ya fito hannun sa rike da dan karamin Yaron da bazai wuce shekara hudu zuwa biyar ba, yadda yaran suka zagaye shi zaka gane cewa ba karamin muhimmanci yake dashi a wajen yaran ba. Wata leda ya ciro a motar sa ya fara raba musu sweet yana shafa kansu d'aya bayan d'aya, duk wanda aka bawa sai ya tafi yana murna. Haka yayi ta raba musu har ya sallame su dukka kafin ya juyo wajen yaron dake tsaye gefe ya saka hannun rigar sa a baki.

"Sultan..." Ya kira sunan sa yana mika masa hannu, da d'an sauri ya karasa garesa yasa hannu ya daga shi sama.

"Baka saki jikin ka ba har yanzu my boy, me yasa ne wai?" Ya fad'a yana kallon Maman Yara data iso wajen

"Alhaji Sultan halin sa sai shi, baya son mutane gashi nan dai tun muna damuwa har mun hakura dan babu me chanja shi."

"Daddy waye shi?" Dan karamin yaron da suka zo tare ya tambaya yana kici-kicin bude ledar sweet din sa, rankwafawa Daddy yayi ya sauke Sultan a gefen sa, sannan ya kamo hannu yaron

"Sunan sa Sultan, abokin ka ne daga yau kaji?"

Sai ya daga kai kamar me tunani kafin yace

"Zamu tafi dashi toh muna wasa tare?"

Girgiza kai yayi sannan ya shafa kansa

"Zan dai dinga kawo ka wajen sa duk Sunday's sai kuyi wasan ko?"

Mak'e kafadar sa yayi irin yadda yara keyi, ya turo baki gaba kamar zaiyi kuka yace

"Ni dai yanzu nake so, dan Allah kaji Daddy."

"Alhaji mu je ciki ko?" Maman Yara ta katse maganar da zai yi, sai ya kama hannun su dukka suka nufi cikin gidan...

Takardu ta baje masa a gaban sa da bayanin duk abinda ya faru daga satin da ya wuce zuwa yanzu, karin yaran da suka samu da kuma karin NGO's din da suka sake hada kai dasu. Sosai yayi farin ciki ya kuma dauki Numbers din su da address domin su samu lokaci su sake zama sosai. Ya jima sosai a gidan yana aikace aikacen sa, da sauraron matsalolin da suke ciki da yin yadda za'a kawo saukin su. Da kyar aka nemo masa Safwan da zasu tafi ya shige cikin yara ana ta wasa kasancewar sa yaro me son mutane da faran faran. Sai dai duk in da yayi yana rike da hannun Sultan wanda a kalla zasuyi kusan sa'anni. A haka sai gashi ya dan saki jikin sa har yana dan shiga wasan. Ganin haka ba karamin mamaki ya bawa ma'aikatan gidan ba, musamman yadda kowa yasan waye Sultan da yadda yake. Har wajen mota ya raka su still suna rike da hannun juna Safwan har da kuka sai da Daddy yayi masa yawo sannan ya yarda ya tafi yana daga ma Sultan hannu.

_Abinda Ke Cikin Zuciya_Where stories live. Discover now