Page 2

200 9 1
                                    

*_Abinda Ke Cikin Zuciya_*

©®*_Hafsat Rano_*

Free page (2)

Amrah

***Ganin both uwar da jaririyar lafiya lou suke sai aka sallame su sukayo gida, tun kafin su karaso gida Hajiya ta iso da kayan ta, suna zuwa suka tarar da ita har ta dora ruwan wanka, nan danan gidan ya soma ciki da yan uwa da abokan arziki kowa da son nuna farin cikin sa, kasancewar tun bayan Adnan sai yanzu Allah ya kawo haihuwar yasa kowa yake jin kamar itace ma ta farkon.
   
Tun da aka kwantar da jaririyar a daki Sultan da Safwan babu wanda ya motsa daga wajen, duk motsin da zatayi suna kallon ta, chan tasa kuka sosai kuka irin na jarirai sabbin haihuwa, da sauri Sultan ya mike ya koma wajen kofa ya tsaya yana rarraba ido cikin yanayin damuwa, kallon sa Umma tayi ta yi murmushi ta cigaba da hada formula saboda rashin ruwan nono, shigowa Mah-Mah tayi dakin ta tsaya da mamaki tace

"Wai dama yaran nan suna makale anan Adnan na chan yana neman su."

Dariya Umma tayi tace

"Suna nan muna jegon tare."

"Lallai kam, toh Hajiya tace an kai ruwan."

Sai ta mike ta bata madarar ta fice ta barsu, hannu Mah-Mah tasa ta kirawo sultan ya dawo ciki suka sata a tsakiyi ta shiga feeding Little angel din da zuwan ta ya zama wani tsani na cikar bururruka da yawa.

   Tun daga ranar har zuwa ranar da akayi suna Safwan da Sultan basu bar umma ta huta ba, idan wannan ya dauke ta sai wannan ma yace sai shi, haka zata sa musu ita a kafarsu suyi ta kallon ta suna jin dadi.
   Ranar suna taci suna Fatima sunan Hajiyan Dr, a take Mah-Mah tace Amrah zasu dinga ce mata saboda shine sunan da ta jima tana so, umma bata ki ba, tun daga lokacin sai rainin Amrah ya zama tsakanin Hajiya da bata tafi ba da Mah-Mah, idan ta dawo aiki take karban ta ta goye sai ta gaji tayi kuka sannan take bawa sabuwar mai'aikinta ta mika tah. Haka yaran ma suke faman jeka ka dawo tsakanin gidan nasu da gidan su Adnan, duk yadda wataran Adnan yake musu gori akan Kanwar sa ce ba tasu ba basa kin zuwa.
    Shekarar Amrah daya cif Umma ta sake haihuwa, sai dai haihuwar tazo da matsala dan sai da akayi mata aiki, sosai ta galabaita saboda haka tun kafin ma su baro asibitin Hajiya ta sa kanwar Umman me suna Safiyya ta hada mata kayan Amrah ta tafi da ita, hakan be wa kowa dadi ba musamman Mah-Mah da yan samarin ta,wanda basu nan ma suna makaranta. Ko da suka dawo suka tarar da abinda ya faru sun nuna bacin ransu sosai, haka dai Mah-Mah tayi ta lallaba su da alkawarin ana yayentan zata dawo nan da sati

Bayan Sati biyu Dr yaje amma sai Hajiya tace a bari Umman ta sake samun karfin jikin ta, ta kuma kula da yar jinjirar me suna Afrah. Haka Dr ya hakura ya dawo gida ya kara bada lokaci Amma sam Hajiya taki.

   Ko da lokacin sata a makaranta yayi Dr (Abba) yazo tafiya da ita sai Hajiya ta daka tsalle tace sam tazo kenan, babu yadda Abba ya iya a haka ya sata a makarantar ya kuma samar mata mai adaidaita sahu da yake kaita ya dauko ta kullum, ajinsu daya da Afrah saboda makaranta daya Abban ya sasu, tare suke komai hatta abinci na mutum biyu umma ke zuba musu haka ma Hajiya.
    Bangaren Yan samarin kuwa sun kara girma suna aji uku a secondary, sosai shakuwar su da Amrah ta ja baya, sai ya zama idan ba ranar Friday ce tayi ba suka zo gaida Hajiya ba basa ma haduwa.
     Amrah bata son mutane shiyasa ko sunzo bata sakewa dasu sai ta makale a gefen Hajiya har su tafi bata musu magana, ita kuwa Afrah sai ta zama me faran faran da surutu ga wayo sosai.
   
***Rayuwa ta cigaba da garawa cikin hukuncin Allah har zuwa lokacin da Amrah suka shiga primary 4 a lokacin ne kuma Abba ya samu invitation daga wata babbar university dake Canada, har lokacin Amrah na wajen Hajiya dan bata ma son zuwa gidan su sam saboda yadda umma ke mata fad'a saboda sangarcin ta, abu kadan sai ta bare baki tayi ta kuka, hakan ba karamin kona wa Umman rai yake ba, sai ta tattara ta, ta maida wa Hajiya ita.
   Sana'ar snacks da foods Umma take, Babar caterer ce, sosai take samun manyan orders na biki, suna da manyan tarukan gwamnati, sai ya zama ta kara zama babbar mace da ake damawa da ita, amintar su da Mah-Mah bata chanja ba sam, sai ma kara karfi da tayi.
  Haka yaran su ma komai tare sukayi, Duk wannan amintar Mah-Mah bata taba fadawa Umman cewa Sultan ba dan ta bane, kuma iya zaman su Umman bata taba ganewa ba sbaoda babu wani abu da zai nuna ma hakan.

_Abinda Ke Cikin Zuciya_Where stories live. Discover now