page 5

133 8 0
                                    

*_Abinda Ke Cikin Zuciya_*

©_Hafsat Rano_

Free page 5

***
Tana kwance bayan ta gama duba gifts din da suka karba tana jiran dawowar Abba da wayar da yàce zai siyo musu a matsayin gift dinsa na grad da sukayi, duk da bata da tarin kawaye balle ace zasu dinga waya ko chat, amma tana so taga yadda duniya ta zama, tana so itama ta zama social ta shiga kowanne lungu da sako na social media taga me ake yi, me ake ji, plus abubuwan da suka shafi harkar chefs, girke girken dishes na kashashe daban daban da ya kasance passion dinta, idan da wayar zata kara samun experience na abubuwa da yawa, gashi tana da sha'awar karatun novels na manyan marubuta online both na turancin dana hausan ma.
    Da sauri ta tashi jin maganar Abban a falo, ta fito da sauri har tana neman tuntube, boxes biyu ne a hannun sa an rufe su, hasken fuskar ta ya karu, ta karasa da d'an gudun ta suka saka Abban a tsakiya, sai da ya gama yi musu nasiha sosai sannan ya basu sabbin wayoyin hade da gargadi da ya fi yiwa Afrah, sunyi masa godia da alkawarin babu abinda zai faru in Sha Allah. Dakin su suka tafi suka hau kan wayoyin sukayi ta fama har dare yayi suna aikin abu daya, sai da Adnan ya shigo sannan ya taimaka ya tayasu yin wasu settings din shima sai da yayi ta ja musu aji.
  Shirye shiryen tafiya Nigeria ya kankama, suna ta murna da dokin zuwa, ranar da daddare Abba ya dawo a gajiye ya shigo lokacin ma suna dakin su suna sabon aikin wayar da ya same su, ya same su man dan tun da wayar tazo basu huta da hidimar ta ba.
   Bayan Umma ta gabatar masa da abinci da ya kasance snacks ne da milk shake, be iya ci ba yace ya koshi ya karbi black tea kawai yasha sannan yace

"School din nan da na taba yiwa Amrah applying sun fitar da circular zasu fara classes next week, akan girke girke da gyaran jiki da abubuwa dai, yanzu ne opportunity din da zata samu tayi kafin su shiga university."

Dan bata fuska umma tayi dan har ga Allah bata son abinda zai katse mata tafiyar ta, muryar Abba ta katse mata tunani

"Ba zan iya hanaku tafiya ba, dan kunsa rai bayan haka ma ya kamata kuje din, dole dai ita Amrah ta zauna sai na hakura ni dama akwai ayyukan da nake son karasawa."

"Toh yanzu ba yadda za'a yi kenan?"

"Eh hakan za'a yi, idan kuka dawo mu sai mu sa lokaci muje in Sha Allah."

"Toh Allah yasa haka ne mafi alkhairi, ita na su Afran basu fara ba kenan?"

"Eh su sai nan gaba, sune batch din da zasuyi bayan mamana sun gama."

"Okh Allah ya kaimu." Tace tana tunanin yadda Amrah zata ji idan aka ce babu tafiya

***
Duhu ne sosai da ya mamaye kowanne lungu da sako na dakin, karamin daki ne na gaske babu komai a ciikin sa sai ta wata yagalgalalliyar katifa data cinye kusan gaba daya dakin, daga chan kuryar dakin take kwance ta zuba wa saman rufin kwanon da rana ta gama dukansa duk ya bule hakan yasa haske rana ke shigowa ciki musamman idan ana tsananin ranar.
   Sha biyu da wasu dakiku na dare, shiru kake ji garin yayi babu karar komai sai chan k'asa k'asa zaka dinga jiyo haushin karnuka da karar injinan gidan masu hannu da shuni dake chan kasan unguwar.
    Juyi take ta tana aikin tunanin yadda rayuwar su ta zama yanzu, idan baka dashi shikenan rayuwar ka ta gama tagayyara, mutane a wannan zamanin kowa kansa ya sani, daga shi sai iyalin sa. Shisa gaba daya rayuwar tayi wahala ainun, babu me jin kan na kasa dashi balle ya taimaka masa, sake gyara kwanciyar ta tayi, ta cigaba da tunanin sana'arta ta kosai da take yi a kullum, abinda suke samu su rayu kenan ita da yayanta biyu mace da namiji Muhammad da Aisha, sosai Muhammad yake fafutuka akan su,tasan yana iyakar kokarin sa wajen ganin ya kyautata rayuwar su, ya inganta musu ita, sai dai komai baya tafiyar musu a daidai, babu me kula su da sunan abota, babu me hulda dasu saboda wani dalili da take ganin sa mara tushe, dalilin da be kai a wulakanta dan adam akan sa ba, musamman idan baka da masaniyar ainihin abinda ya samu rayuwar mutum har ya zama abinda ya zama. Allah da kansa ya ce ya karrama bani Adam, toh me yasa wasu mutanen suke wulakanta wannan darajar da Allah ya basu?

_Abinda Ke Cikin Zuciya_Where stories live. Discover now