Page 6

310 15 6
                                    

*_Abinda Ke Cikin Zuciya_*

©_Hafsat Rano_

         Last free page (6)
  

***
Yana shigowa motar ya ji an kira sunan sa, ya juyo da dan sauri dan be ma lura da ita ba, murmushi yayi mata ya amsa sannan ya juya, sai ta fara masa surutu, dafe kansa yayi ta hannu daya yana jin wani haushi na kamashi, har suka zo gida bata yi shiru ba, haka suka fito suka shiga ciki still tana cigaba da surutun da babu me kulata a cikin su, sai ma kara sauri da Safwan yayi ya shige bangaren su yana daga waya.
   Jerawa sukayi har falon Mah-Mah, kana kallon yadda yake amsa mata zaka gane ba son hirar da take masa yake ba, zama yayi Mah-Mah ta fito kenan daga kitchen da sauri Umaima taje ta rungume ta suka saka dariya a tare

"Yanzu muka gama waya da Amina tace min kin iso? Nace dai Safwan yaje daukar ki ashe tare ma kuke da Sultan."

"Tare muke, sai da muka bi muka dauko shi."

"Sannu da zuwa toh, ki shiga ciki ki huta Hauwa zata kawo miki abinci."

"Ok Mah." Taja jakar ta ciki bayan ta juyo ta sakar ma Sultan murmushi, girgiza kansa yayi ganin irin kalar tata tarbiyyar, be ji lokacin da ta gaida Mah-Mahn ba kuma ko a jikinta,Allah ya kyauta kawai yace ya dan zamo ya ce

"Barka da gida Mah-Mah."

"Barka Sultan, ya aikin?" Ta zauna tana rage karar tv,

"Alhamdulillah."

"Ina dan uwan naka ya tsaya?"

"Ya shiga ciki."

"Owk sannun ku, abinci fa?"

"Um sai dan anjima, ni wani kyakkyawan labari nazo dashi ma Mah-Mah, yaushe Daddy zai dawo gida?"

"Ah Alhamdulillah, ko nayi sirika ne?"

Sosa kansa yayi ya girgiza shi yana dariya

"Scholarship na samu akan course din da nake."

"Alhamdulillah, alhamdulillah kai amma naji dad'i."

"Abin da ya dawo dani ma gida yanzu kenan, kin ga har sun turo komai."

Ya bude mail box din sa ya mika mata, karantawa tayi, sannan tace

"Wannan labarin yanzu zaka kira Daddy ka sanar masa, naga abin ba zai dau lokaci ba sai ka fara shiri."

"Shirin me za'a fara?"

Ya karaso ciki yana kallon Sultan, sai ya mika masa wayar yana murmushi, layi bayan layi yabi ya karanta sannan da sauri ya dago yana nuna farin cikin sa

"Amma gaskia baka kyauta min ba, da wannan good news din amma muka tawo all the way from asibiti har gida baka fad'a min ba."

'dage kafadar sa yayi yana murmushi yace

"Uwa ce gaba da dan'uwa ko baka gane ba?" Ya kanne masa ido daya yana kallon Mah-Mah

"Haka ne." Mah-Mah tace tana dariya

"Kaci bashi wallahi, akwai abinda nake son fad'a ma nima amma na fasa Wallahi, sai komai ya kankama zaka ji."

"Kar muyi haka dakai dan Allah, dan fesa min mana."

"Zaka bushe ka fado kamar ganye aikuwa, idan lokacin jin naka yayi kaji Malam."

"Kai kuwa Sultan kyale shi, dole dai zaka sani din, tashi kaje kaci abinci sai ka kira baban naku, kasan yafi so ku yayan sa ku fad'a masa abu kai tsaye ba wai yaji ta waje na ba."

"Toh Mah-Mah, bari na kirashin dan bana jin yunwa yanzu sai ko anjima."

"Allah ya kaimu anjiman."

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Mar 08, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

_Abinda Ke Cikin Zuciya_Where stories live. Discover now