Page 4

171 9 1
                                    

*_Abinda Ke Cikin Zuciya_*

©®*_Hafsat Rano_*

Free page (4)

***
Tashi yayi da sauri ya shiga contact yayi dailing number Sultan, ringing tayi, tayi be daga ba, sai ya ajiye yana jin wani feeling me karfi na shigar sa, text message ne ya shigo wayar ya duba sai ya ga Sultan ne ya turo masa message

"Ina tare da supervisor dina ne, call back if it's urgent."

"No take care." Yayi masa reply ya ajiye wayar a saman mirror din dakin ya fad'a toilet, wanka yake yana murmushi shi kadai, ya sameta ya gama yasan, shiyasa ba zai yi k'asa a guiwa ba wajen xuwa ya samu Hajiya da maganar ba. Ko da ya fito ya shirya tsaf cikin kananan kaya da sukayi masa kyau ya fesa perfs masu kamshi ya rufe dakin ya bi corridor zuwa shashen iyayen su. Mah-Mah na bawa me aikin ta sautu ya shigo yana d'an kad'a kansa kadan cikin farin ciki, kallon sa tayi, ta zauna tana bin ba'asin mood din sa da ta gani.

"Wannan farin cikin kamar wanda akayi wa kyautar mata."

Tace tana kallon sa, sosa kansa yayi ya saki dariya kadan yace

"Gidan Hajiya zani na gaishe ta, rabona da gidan tun kafin Adnan ya tafi, kar tace dan baya nan ne muka dauke kafa."

"Ka kyauta, shi sultan ya zama agogo sarkin aiki, yace min yau sai dare ma zai shigo gida saboda wani abu da zasuyi a clinic ko me ma yace ne? Yaren nasu ne sai su."

"Eh haka yace min, na kirashi ma yana tare da supervisor din sa."

"Ok Allah ya taimaka wannan karatu me wahala, ko da yake da an gama shikenan."

"Balle ma nasu, sai dai k'wari irin sa dama ba irin namu na masu small brain bane."

Sai ya mike

"Bari naje Mah-Mah, dan Allah yau da daddare ayi mana tuwo miyar zogale, irin na Umma dan Allah Mah-Mahn mu."

"Toh ai ban iya irin nata ba sarkin iyayi." Tace tana dariya

"Please please sai na dawo, yau a farin ciki nake matuka, I can't wait Sulty ya dawo na siyar masa da jaridar."

Yace yana yin gaba, daga murya tayi tace

"Idan tayi wari maji ai, magulmata."

Dariya yayi ya fice yana jin shi on top of the world baki daya.

Motar sa ya shiga ya bata wuta bayan ya kunna wakar soyayya ya nufi gidan Hajiya domin isar da sakon zuciyar sa.

Ta fito tsakar gidan kenan tana kwashe shanyar da tayi ya shigo, da sauri ya karba ya karasa ya bi bayan ta suka shiga ciki suna tsokanar juna, ruwa ya dauko a fridge yasha ya koma ya zauna yana maida hankalin sa kan ta sosai ya ce

"Hajjaju me ran karfe wajen ki nazo fa."

"Ja'iri ai nasan ba takanas dan ka gaishe ni kazo ba, ko da yake kafi dayan dan uwan naka mara kirki."

"Wanne dan-uwan nawa a ciki?" Yace yana dariya

"Wanene idan ba adunanu ba? Ja'iri jiya ya kira ya gama kare min tanadi, harda wai ya sami baturiya ba shi ba dawowa."

"Kai be kyauta ba, ni ai ba haka nake ba." Yace yana guntse dariyar sa

"Kaji dashi, Muhammadu ne kawai na kirki a cikin ku, ko jiya sai da ya biyo ya bani man ciwon kafa."

"Allah sarki ai da tare fa zamuzo, sai kuma Allah be yi ba."

"Kanka akeji, kace waje na kazo, ya akayi?"

Zamowa yayi ya zauna a kasa ya sosa kansa yayi murmushi

"Dama... Dama kamun kafa nazo hajiyar mu."

_Abinda Ke Cikin Zuciya_Where stories live. Discover now