Page 3

170 9 3
                                    

*_Abinda Ke Cikin Zuciya_*

©®*_Hafsat Rano_*

  Free page (3)

***
*_SMM ORPHANAGE_*

Juya aikakkiyar wasikar take a hannun ta, zuciyar ta a jagule kamar ta dora hannu aka ta saka ihu ko taji saukin zafin da take mata, sai da tayi mata duban tsanaki sannan ta ninke ta, ta hada da sauran kayayyakin da take tarawa, ta ajiye su a ma'ajiyar su, sannan ta fito wajen yaran dake jiran ta.
   Ranar a kasalance tayi komai, daga karshe ma sai ta shige ciki da niyyar ta kwanta ta huta ko ta samu zuciya da gangar jikinta su samu nutsuwar da suka rasa.
   
***
Da sauri Safwan ya bi bayan shi, har ya kai gate zai fita ya tsaida shi da d'an gudun sa

"Lafiya kuwa?" Yace sanda ya fuskance shi, sai ya ga kamar idon sa yayi ja

"Babu komai kaina ne ya dan yi dum, sai kuma na tuna sakon Daddy, kasan fa time na kurewa bamu ma gama hada kan kayan ba balle mu kai."

"Shine duk ka damu haka? Chill guy muje mu karasa shan furar chan sai mu karasa hade kayan gobe da wuri sai mu kai musu."

Girgiza masa kai yayi

"Karka damu, bari na je gida idan ka gama sai ka sameni."

"Shikenan tunda ka dage, bari naje sai na shigo.".

Sai ya juya shi kuma ya fita yana jin wani irin emptiness da besan na menene ba, ya san dai kawai ba normal yake jin sa ba. Daki kawai ya wuce direct ya kwanta rigingine ya daga kansa sama yana tunanin yadda rayuwar sa take, idan ya tuna shi din maraya ne, bashi da kowa da zai nuña a matsayin jinin sa, sai yaji duk komai ya kwance masa, amma idan ya tuna gatan da kuma Allah yayi masa ya tsamo shi ya inganta masa rayuwa sai yaji duk tunanin ya kau, baya fatan ganin iyayen sa domin Mah-Mah da Daddy sun cike dukkan gurbin da iyayen nasa suka bar masa shi open, sannan ga dan uwa amini da zai iya cewa bashi da kamar sa duk fadin duniyar nan, soyayyar da yake masa daga Allah ce, Allah ne ya hada su cikin Ikon Sa, ya kuma saka kauna a tsakanin su,kauna me tsanani da ta zama wani jigo na rayuwar sa.
     Bashi da wata matsala da su, haka kuma iyaye ya dauke su, ba kuma ya fatan Allah ya kawo ranar da zai butulce musu. Daya daga cikin abinda yasa ya zabi bangaren lafiya, kuma bangaren zuciya saboda ya riga yasan Safwan ne rayuwar iyayensu, Shima kuma haka, duk lokacin da ciwon sa ya tashi su kan rasa sukuni, har sai sun ga ya dawo daidai sannan komai yake komawa daidai.
    Safwan mutum ne shi be faran faran da jama'a da son duk wani da zai rabe shi, fuskar sa a sake take da wuya ka ga bacin rai a fuskar sa while Sultan bashi da fara'ah sai dai fuskar tasa a sake take ba irin a daure nan ba. Yana da kazar kazar shiyasa ma Daddy yafi dora shi akan duk wani abu kafin yace Safwan sau daya ya kira Sultan sau goma.
   Yana kwance yana sakawa da kwancewa aka kira sallah, sai ya mike ya dauro alwala ya wuce masallaci. A chan suka ya tarar da su adnan bayan sun idar sai suka samu waje a nan bakin layin sukayi zaman su suna hira irin wadda maza samari ke yi galibi, hirar siyasa, kwallon kafa sai kuma hirarrakin yan mata. Safwan da Adnan sune akan gaba wajen kawo tactics din saye zuciyar mace, inda sultan sai dai yayi musu dariya kawai idan abin dariya ne. Chan Adnan ya zungure shi ya bata rai yace

"Kaifa wallahi dan rainin class ne, kana yin kamar baka san komai ba, kamar wani uztaz."

"Toh da menene?" Ya amsa masa yana dariya

Wani abokin su Mubarak yace

"Gaskiya ne ya sheik, irin ku ne soyayya ke wa kamun kazar kuku, kuzo kuna ciwo kamar ba zakuyi rai ba."

"Allah ya kiyaye wallahi.". Safwan yace yana mikewa

"Sultan yafi karfin yace yana so a wulakanta shi wallahi, gaye iya gaye ga nutsuwa ga aji, ai sai na zaba na darje kafin na yarda ya kula koma wace."

_Abinda Ke Cikin Zuciya_Where stories live. Discover now