Five

1.2K 148 3
                                    

🍯 ZUMA 🐝
Five

✍🏻Shatuuu💚

Bansani ba ko tafiyar da mukai da kuma canjin abinci ne yasa Nawwara yin rashin lafiya, dandama normally idan kayi tafiya kana exceeding abinda kake ci, tunda komai aka baka dan ka farantawa host dinka rai zaka ci. Hakan ce ta kasance akan Nawwara, washegari early Monday morning dukka sun tashi suna shirin tafiya school, ni kuwa ina nade cikin bargo ina bacci, se can naji gidan shiru wanda ya tabbatar min sun tafi, fitowa nayi na leka dakin Daddy bayan nayi brushing na samu ya gama shiri zai fita. Na gaishe shi ya amsa yana tambayar gajiyar da muka kwaso

"Daddy kaci abinci ne?"

Kanshi ya girgiza yace

"Aa suna ta sauri ina tunanin suma basu ci ba"

Kaina na gyada dan banga alama ba, se nace

"Idan ba sauri kake ba should I make a cup of tea for you"

Murmushi yayi yace

"Thank you Allah yayi miki albarka daughter me"

Da sauri na juya na shiga kitchen na soya masa kwai biyu na hada da tea da bread na kai masa. Seda ya kammalla sannan ya nufi office se ya rage ni kadai a gidan, na danyi gyaragyaren daya dace na koma bacci. Wajen 12noon na farka na shiga gurin Baba Asabe muka gaisa sannan kuma na koma kitchen dan daura abinci. Na gama grating attaruhu kenan naji sallamar Nawwara da sauri na fito dan ganin ko lafiya tunda nasan time din closing baiyi ba,she looks terrible, idanunta sunyi ja sannan sun nutse ciki, ga wani bags a kasan idanun nata,hannun ta akan cikin ta wanda zai baka insight din cikin ke ciwo, laddle din hannuna na yar a kasan kitchen sannan na nufo ta ina tambayar ta menene? Nawwara shagwaba ai se ta fara kuka tana cemin cikin ta ke ciwo kuma gudawa take. Daki na raka ta inata lallama ta sannan kuma ta kwanta tana ta murkususu, a karamin tunani na se na kawo mata tea, she don't resist tea haka ta karba ta sha se ya lafa tayi bacci ni kuma na lallaba na koma kitchen, lokaci zuwa lokaci ina dubata, a haka na kammalla abincin na zuba inda ya dace na koma dakin da take, tayi amai tun daga bakin gado har toilet ko ina karni yake dole na kure fanka na hau gyara, wasa wasa se karamar magana ta zama babba ko yunkurin amai tayi se gudawa, na rikice na rasa yadda zanyi, se can na kira driver office din Daddy, shi yake kaimu duk inda ya dace apart from makaranta, bai bata lokaci ba muka tafi se Shekoni. ATM din da Daddy yake bar mana reserve na dauka, nasan da kudi a ciki dan dama in case of hakan ya bar mana. Seda na taimaka mata ta gyara jikin ta sannan muka tafi.

Jabir shi ne saurayi na na farko, laboratory scientist ne a cikin shekoni. Bayan an gama duk wata resuscitation procedure kuma God so kind gudawar ta tsaya aka dauka blood aka ce  na kai lab, dake suna da side lab a cikin emergency unit din se yasa ban je can main lab ba. Ina zuwa na bayar aka rubuta min invoice nayi payment sannan aka bani reciept yace naje after 5pm na dawo na amsa. Banma lura da yaya yake ba kawai nasan naga namiji a gurin that's all, dan ni a wannan lokacin soyayya ita ce last thing dana ke kawowa a cikin rayuwa ta.

Na dawo na zauna a gurinta a raina ina ayyana by now nasan sun dawo kuma zasuyi mamakin bana gida, wayata na fara lalubawa amma naga kwata kwata babu wayar, cikin sauri na mike amma ko kadan na kasa ganin inda wayar take, shiru nayi wai ko zan tuna inda na barta amma na kasa, dan na kasa tuna ko ma na dakko ta daga gida. Bayan nayi sallar laasar naje station din nurses na gaida su dan wanda na samu da safen sun tafi se wasu da suka karba dutyn. Mata biyu namiji daya suna hira saboda babu pt din ma sosae. Suka amsa daya daga ciki ta zuba min idanu se dayar ce tace min

"Akwai wani abun ne?"

Hannuna na saki nace

"Dama dan Allah zan dan iya amfani da wayar ku na kira babana nace my sister is hospitalized?"

Namijin ne ya miko min wayar shi na karba nayi dialing number Daddy amma har sau uku baiyi picking ba, dan tsaki nayi na mika masa nace

"Thank you amma baiyi picking ba"

Kara miko min yayi yace

"Babu wanda kika rike number dinshi a gidan?"

Kaina na gyada dan na rike ta yaya Rahama, karba nayi nayi dialing number, kamar jira ake akai picking.

"Ya Rahma Nanah ce"

"Nanah ina kika je keda Nawwara se neman ku muke?"

"Muna shekoni anyi admitting Nawwara, ku fadawa Daddy sannan ku zo"

Daga haka mukai sallama na bashi wayar tareda godiya na koma wajen Nawwara na samu bata tashi ba, na jima ina kallon yadda ta rame lokaci guda, ga period ga diarrhea abin yayi yawa. Ban jima ba yazo da wayar wai ana kirana, karba nayu naga yaya Rahma ce nsyi picking nan take gaya min na bar wayata a lab naje na karba. Se lokacin ya dawo min tabbas acan na bari , mikewa nayi na bashi wayarta na koma side lab din sede wanda na tarar daxun ya tashi it's a new face, fuskarshi a cikeda kasumba wadda tasa shi yayi looking old, amma da zarar kunyi eye contact zaka fahimci he's young. Sallama nayi ya amsa Ba tareda ya dago ba saboda yana dauka sample jikin wata yarinya wadda ke bashi tough time saboda kukan da takeyi. A haka ya dauka uwar tana ta masa godiya. Juyowa yayi ya dube ni ina tsaye a jikin window, hannunshi ya miko min alamar na bashi investigation form din, se nace dashi

"Nazo dazun kawo sample na bar wayata, dan Allah ko ka ganta?"

Kan shi ya girgiza yace

"Ban gani ba!"
Ya fada kanshi tsaye, se na girgiza kai na ciro receipt na nuna mishi nace

"Kaga wallahi i came amma wanda ya tafi bai fada maka ba?"

Receipt din ya karba yayi min retrieving result din ya miko min, karba nayi na fara zama frustrated nace

"Kaga sister dita ta kira kuma ance mata wayar yana lab dinnan fa"

"Kije ki dakko sister din taki"

Shiru nayi ina tunanin yadda zan masa , gani nayi ya cigaba da abinda yake bai ko kara kallona ba, raina yayi mugun baci na wuce na nufi EU din, ina zuwa na samu su yaya sunxo dukkansu, da uban kaya na kai lab result din sannan na tafi wajensu nan na samu Nawwara ta tashi. Abinci take ci na fadawa yaya Rahma yadda akai tace muje lab din. Muka tafi muna karasawa tayi dialing number dita se gata ta fara ringing, dauka yayi zaiyi swiping nace

"Hey! Bani"

Na fada ina mika masa hannu na, kallo na ya tsaya yi kawai se ya miko min, na karba tareda dalla masa harara nace

"Aikin banza kawai"

Se naga yayi dariya wanda ya kara kular dani amma se muka koma naci abinci, anan Daddy ya same mu. Se dare suka tafi ya zama ni zan kwana a gurin ta. Washegari jikin da dama dan har tana tashi, amma sunce akwai medications din da bata gama ba so ba zancen discharge haka dole muka cigaba da zama. Da yamma ina zaune wannan nurse din ta turo aka kirani, naje na sameta tace min

"Meye sunanki?"

"Nanah Fadima"

Na bata amsa, kai ta gyada tace

"Akwai wata da kuke min kama da ita sosae hatta idan kikai murmushi, in fact tafiyar ku ma iri daya ce."

Kaina na yada nace

"Ayya"

Se tayi min murmushi tace

"Kina da yan uwa a Bidda?"

Kaina na girgiza nace

"Aa! Ni yar jigawa ce dukkan yan uwan mu a jigawa suke"

Kai ta gyada tace

"Allah me halitta."

Daga haka na tafi, kilan kuga wauta ta, maganar gaskiya I don't know anything bidda, ban masan ina ne bidda din ba balle nasan mamata yar bidda ce saboda ni Anty Sumayya tace min mamana yar niger ce so na saka niger din a cikin raina.

Ayshatuuu

ZUMAWhere stories live. Discover now