Thirty two

1K 168 13
                                    


🍯 ZUMA 🐝
Thirty two

✍️Shatuuu💜

Kwanaki Suka Dan ja, an maida ni shifting gaba daya dukda ba haka naso ba amma hod yace gwara na Saba tunda yasan Dole watarana zai Kama ni. Ranar na dawo daga monthly clearance da muke Yi a Secretariat, a gajiye na dawo na cire kayan jikina na watsa ruwa sannan na kwanta bayan na kulle dukka windows, yau Yan nepa Zan Rama abinda sukai Mana daran jiya, sukai ki kawo wuta wajen 12am Mai ya Kare a gen. Kamar zanyi hauka saboda zafi se yanzun suka dawo da ita, AC na kunna Babu jimawa bacci me nauyi ya dauke ni, bani na farka ba se bayan laasar dama period nake so no need na tashi yin sallah, Shima Ina tunanin ko Yunwa ce ta tashe ni Dan kamar Zan ci Babu Dana tashi,wanka na Kara Yi na saka skirt da riga na atamfa na daura dankwalin na fito. Amal ce kawai a gidan dan dama nasan zasuje gidan Amina wai zasu taya ta sanitation,

"Yaya kin tashi"

Ta tambaya bayan na fito da plate cike da abinci, Zama nayi nace

"Nasha bacci fa! Basu dawo ba kenan?"

Ta danyi dariya tace

"Ai se dare sannan zasu dawo"

Kaina na gyada na maida dukkan hankalina kan abincin, seda na gama sannan na janyo wayata Dan ganin missed calls din da aka bar min, hibba na fara kira tana picking nace

"Kin haihu ne?"

Tayi tsaki tace

"Thick skull, da cikin kwata kwata watan shi nawa?"

Na tabe baki nace

"Do I know?"

Se muka bar wannan maganar bayan ta fada min ai cikin is five months old, kusan daya dana Amina ta.

" Nanah ya ake ciki?"

Nasan zata tambayeni ko nayi saurayi ne, Dan ta zageni da nace mata mun rabu da Nasir, tabbas da wani yana yiwa wani aure da tuni hibba dasu Anty sumayya sun yimin, Babu dama su ganni da wani sun dinga tambayar shi kenan, Aisha seda ta fadawa Mom zancen Yasir, ta dinga min masifa akan me yasa ban bashi number ta ba nace to ni ya min yarinta da yawa, yace

"Se kije ki aura sugar daddy to, tunda ke kowanne namiji yaro ne a gurin ki."

Nidai hakuri nake bata kawai a haka muka kashe maganar, cousins din mu na hadejia da sukai karatu musamman yayan Uncle Mahmud da suke Abuja, akwai dan shi Usman tun last week take Kirana akan yace mata yana Sona, ni kuwan se dodging nake Amma taki ganewa.

" Shiru Babu wani motsi fa, I'm still the single Nanah you know"

Na bawa hibba amsa, muryar ta naji tayi softening tace min

" Lokaci ne kin sani ko? Ina fata baki damun kanki"

Nayi dariya nace

" Kune kuke making dina nake feeling kamar rashin saurayin nan laifi na ne, idan ba haka ba me zai dameni"

Tace

" Kiyi hakuri! Amma I'm eager ne kawai na ganki a dakin ki wallahi"

" To ba se lokaci yayi ba, Nima ai Ina son nayi auran"

Muka Dan taba hira kadan, sannan mukai sallama, aje wayar nayi not minding in Kira sauran da suka Kira ni, kamar an tsikare ni na Mike tare da janyo wayar anan na ci Karo da number shi ya kirani Shima, ikon Allah nake ayyanawa nayi more than two months tare dashi Amma har yau bansan sunan shi ba, Bai taba fada ba Nima ban taba tambaya ba. Ina kokarin Kiran nashi sega wata number ta kirani, na dauka na Kara a kunne na

" Sunana Yusuf Idrith, Ina magana da Anty Nanah ne?"

"Eh Nanah ce! Amma ban gane waye ba"

Yace

ZUMAWhere stories live. Discover now