Fourteen

982 156 4
                                    

🍯 ZUMA 🐝
Fourteen

✍🏻Shatuuu🖤

Gaba daya kaina ya kulle na kasa cire wayar da kunne na, kuma na kasa yin tunani, se can wajen mintina da suka shude sannan na tashi na zauna wanda ya bawa wayata damar sulalowa tayi zaman dirshan kan gadon, dauka nayi na duba lokaci naga ashe asuba ma ta kusa tunda hudu da mintina goma. Nasan bazan kara komawa bacci ba duk naci na. Se kawai na tashi naje nayi alwala nazo dam nayi karatu, ni kaina nasan ba iyawa zan yi ba amma wani lokacin kana bawa zuciyar ka benefit of doubt. Se da nasa takaddar karatun a gaba kafin kuma na fara tunani. Me ya faru har ta dauki wayar shi? Kenan tunda ya koma gida suke ta fada har ta fi karfin shi ta dauke wayar ta zazzageni? Kaina na girgiza Aliyu bazai taba barin Fatima ta zageni a gaban shi ba. Amma to me ya faru? Meye laifina anan? Kiran shi da nayi, soyayyar da muke yi ko ko me? Kaina na girgiza ina ayyanawa banida laifi ni a zaman mu kullum kokari nake ganin ban shiga hakkinta ba amma ita me yasa zatayi haka?

Se na dauki wayar na duba lokaci naga har mintina ashirin sun karu, to ko nayi dialing number tunda nasan tana hannun ta se inyi knocking senses cikin kanta? Se kuma na ayyana to zan biye ta ne? To kuma idan ya zamana ta goge nata kiran ni tayi min sharri! Se kawai na girgiza kai na ina fadin. Komai zai tafi daidai. Mikewa nayi nayi sallah na jima ina addua sosae sannan kuma na tashi sauran roommates dina na tafi wanka. Lokacin da na dawo gari ya fara washewa se na dama cerelac na sha. Sofy na cemin

"Ni fa Nanah idan naga kina shan cerelac dinnan kunya nake ji"

Murmushi nayi nace

"Haba dai. Da baki je gidan mu ba da kinyi kallo"

Ina gamawa na shirya na dauki abunda zan dauka nayi musu sallama se class. Kadan na samu a class din se na zauna ina duba littafi na. Kafin na shigo class din na kira Anty Sumayya dan fada mata halin da ake ciki, midway wayar ta fara ringing na tuna Hibba ta taba cemin anyi irin haka da sister dinta, matar saurayin ta ta kira ta zage ta ita kuma ta fadawa Mami, mami ta fadawa babansu se aka fasa bikin wai matar tafi karfin mijin kenan. Tunawa da nayi yasa nayi saurin katse call din ina ayyana idan haka ta faru dani bazan kara numfashi ba, kamar yadda relationship din namu zai zama tarihi nima hakan ce zata kasance dani.

Inata kokarin concentrating haka dai na samu na dan taba har Hibba ta zo. Da mamaki ta zauna gefe na tace

"Kora akai daga hostel?"

Harara ta nayi nace

"Na canja ne na daina latti"

"Kamar gaske"

Ta fada tana ciro foil paper daga jakarta, miko min tayi sannan ta miko min kunun aya cikin water bottle me sanyi tace inji Mami. Naji dadi har cikin raina sannan naci naman da samosa na jefa sauran a jaka shi kuma kunun na shanye tas ina lashe baki nace

"Allah ya sakawa Mami da aljanna"

"Ni kuma fa? Ni na kawo fa?"

Se nayi dariya nace

"Har dake mana"

Inata son na fada mata amma na kasa gani nake bazan iya fada ba. A haka ranar tazo ta wuce zuciyata babu dadi, bawai na tsorata da empty threat din ta ba, aa shi da bai kirani ba shi ne matsala ta, ni kuma na kasa samun kwarin gwiwa na kirashi , matar shi sau daya a tarihi taci nasara akaina, duk masifa da fada irin nawa se na gagara bata amsa balle ma na rama, baa taba haka dani ba, bana barin fada saboda ni mafadaciya ce amma imagine wai yau ni ce a hakan.

Wajen karfe tara na dare ina zaune ina kallo saboda na rasa me zanyi ya dauke min hankali amma na rasa, kimai na fara se naji ya isheni, nayi game, nayi chatting amma duka se naji babu armashi se kawai na kunna kallo ina forcing kaina nayi din. Wayata ce ta fara ringing cikin sauri na juyo da ita a raina ina adduar Allah yasa Sahibi ne. Se addua ta ta karbu shi dinne yake kira. Na dauka na masa sallama ya amsa yana fadin

"I'm sorry Sahiba, yau dukka ban kira naji yadda kike ba, kema kuma shi ne kika share ni ko?"

Kaina na girgiza kamar yana ganina, lokaci guda naji ina mantawa da abinda ya faru ina jin anya a yadda Sahibi yake zai ajje dakikiyar mata irin Fatima dama tuni naji na raina class din ta, na zata she can't stoop to the lowest point da zatai haka ba.

"Nasan kana abu ne shiyasa."

"To ya kike kinyi missing dina?"

"Dole ne ai I've to miss you koda minti daya nayi banji muryar ka ba"

Se yayi dariya daga haka muka dan taba hira mostly ta yaran shi ce daga karshe nace masa

"Nikam kayi saving number ta ne?"

"Of course nayi mana na saka miki Sahiba"

Kaina na gyada nace

"Zaka iya deleting?"

"Saboda me?"

Se nace

"Kawai ina son peace ne, idan na maka waya kai deleting a log dinka haka ma message dina!"

"Then dole akwai dalili kenan, me yasa da baki fada haka ba se yanzun"

Se na kasa cewa komai amma ni bana son kai karar matar shi, wannan shi ne karo na farko da tayi hakan ya kamara na mata uzuri, kowacce mace zata iya haka dan ganin ta mallaki abinda take so, amma hakan ba bullewa bane. Ko sallama kirki bamuyi ba ya kashe nima se nayi kwanciya ta kawai nayi bacci.

Washegari wajen karfe uku na yamma ina class naji alamar message, dubawa nayu naga Sahibi ne

Ki same ni inda muke haduwa after your class!

Ban mishi reply ba na cigaba da sauraran karatu na, amma kunsan me kusan rabin hankali na baya class din, yana can wajen shi, ina ayyana me ya kawao shi tunda ko kafin na shiga lecture dinnan seda mukai waya amma bai cemin zai zo ba, kuma munyi agreeing zamu hadu only da weekend banda lectures amma nasan koma menene it's urgent. Seda nayi har sallar laasar kafin nace da Hibba muje gurin shi daga nan ta wuce gida, haka muka sane shi yana zaune yayi shiru too far daga hayyacin shi, yayi nisa cikin duniyar tunani, sede ina masa magana ya jiyo tare da kalkalo murmushi yayi mana yana fadin

"Aminiyar mu se yau na kara ganin ki kenan"

Ta danyi dariya tace

"Kaga yawancin ai da weekend kake zuwa shiyasa"

"Hakane" ya yadda sannan ya tambaye ta mutanen gida itama ta tambayi yaran shi, daga nan se ta mana sallama ta tafi. Se lokacin na tattara dukkan hankalina na bashi,

"Me ya faru tsakanin ke da Fatima jiya?"

Yadda yayi maganar muryar shi cike da bacin rai. Ni kuma se nayi murmushi saboda na danyi calming dinsa nace

"Shi ne kazo a fusaace haka?" Se Nayi dariya nace "To ka saki fuskarka mana ai ba a haka zan fada maka ba"

Ya jima yana kallona wondering only God knows what, se yayi murmushi yace

"Ki fada min mana"

Hakan yasa nace

"Ta kira ni ta zageni tace na rabu da kai, kai mijin ta ne ita kadai da sauran zancen mata na kishi! Ya akai kasan ta kira"

"Kiyi hakuri kinji , nasan baa kyauta miki ba amma wannan shi ne karo na karshe da hakan zai faru. Da kanta ta fada min ta kiraki, kuma ita bacin ranta me yasa kikai mata shiru. Bakida masaniyyar hukuncin da kika yanke yadda ya kara miki daraja a idanuna. Idan wata ce zata rama zagin confirm, tun da sassafe zata kirani ta fada min amma ke se kika nemo mana solution da kike ganin shi ne zai mana amfani baki daya. Ina son ki sani zuciyata zata cigaba da son ki har zuwa karshe."

Waye baya son a yabe shi babu shi, so naji dadi kuma haushin Fatima da nake ji se ya kau nayi mata uzuri da soyayyar minjin ta amma ni fa bazan iya zubda girma na nayi hakan ba, matsayina matar shi kadai ya isa ya fadawa budurwar tashi ni ce gaba da ita.

Ayshatuuu

ZUMAWhere stories live. Discover now