Forty one

1.5K 177 21
                                    

🍯 ZUMA 🐝
Forty one

✍️ Ayshatuuu 🤎

Dakin Babu kowa se ni daya, an lullubeni da katon veil Wanda a iya rayuwata ban taba sa size din shi ba, se a wañnan ranar. Ni kaina nasan aure da da ba daya bane, tunda su hibba, aminatu, Noor, Hasina, Amra hadejia da sauran cousins Dina suka tafi ban Kara bude kaina ba, Ina zaune akan kujerar parlona inata sakawa Ina kullawa, har wajen bayan thirty minutes sannan na fara jiyo footsteps da kuma dariya alamun ana tahowa inda nake, gabana ya cigaba da faduwa, Ina adduar Allah yasa ya shigo shi daya,muryar Yusuf na fara ji yana fadin

" Abbah zamu kwanta Allah ya Sanya alkhairi"

Muryarshi tayi kasa shi yasa banji amsar shi ba, Hanoon tace

" Abbah na shiga naga Antyn? It's been long da..."

Bata karasa ba naji muryar da a gurina is new tace

" Hanoon! Ina ce yanzun kullum Zaki na ganin ta, ki Bari se ku hadu gobe"

A take na fahimci ita ce mummy su Hanoon, ya Dan Kara kamar five minutes sannan a hankali naji ya turo kofar ya shigo, ya mayar ya kulle tare da Murda lock din Wanda yayi Kara har seda naji gabana ya Kara faduwa, ya Jima a tsaye ba tareda nasan me yake ba, na dai San ban ji footsteps ba, hakan ya tabbatar min yana tsaye. Turaren shi ya iso dukda Shima parlon kanshi ne kawai ke tashi Amma dukda haka seda kanshin turaren shi ya Isa cikin nostrils dina. Lumshe idanuna nayi lokacin da ya karaso inda nake, a hankali ya tsugunna gabana, gwiwar shi na gogar tawa ya yaye veil din daga kaina, kaina a kasa but Banda kayataccen murmushi Babu abinda yake fita daga fuskar tawa, hannun shi yasa ya dago habata, dagowa nayi na kalla fuskarshi casually without hesitation, rabon Dana kalleshi a nutse har na manta, Dan ko ranar daurin aure da Suka shigo da abokan shi, kasa sakin jiki nayi. Shima murmushin yake me kayatarwa, murmushi yake na nuna ka samu abinda kake buri, ka cika burin zuciyar ka. Dauke kaina nayi Ina jin kunyar yadda muka Zama so close dashi, mikewa yayi tareda Mika min hannun shi alamun na Kama, na kalla hannun da kana kallon kasan na cikakken namiji ne, kallon shi nayi naga Shima kallona yake, na turo bakina sannan na saka hannun nawa a hankali kamar wadda Zan daura akan naked electric wire. Mikar Dani yayi tareda rungume ni a cikin jikin shi, da farko mutsu mitsu na fara Ina kokarin freeing kaina, daidai kunne na yace

" Amour!"

Ya fada a marairaice, yadda ya fada sunan yasa gaba daya tsikar jikina ta tashise kawai na zagaye hannuna a bayan shi Ina Kara kwantar da kaina a broad chest dinsa. Mun kusa ten minutes a hakan sannan ya sassauta rikon ya Kama hannuna muka nufi bedroom din dake gefe, kamar kowacce amarya, kamar kowanne aure muma sallah mukai Dan nuna godiyar mu ga Allah, Dan mu roke shi zaman lafiya da dawammemen farin ciki a wañnan sabon chapter da muka bude a rayuwar mu.hannun shi yasa ya karba veil dina yace

" Aje shi ki huta mana, tun dazun kike fama"

Babu yadda zanyi haka na bar mishi ya aje a gefen gadon sannan ya fita, kaina na kwantar akan gadon Ina lumshe idanuna jin wata Yunwa da nake ji, ni nasan tunda aka fara hidimar biki banci abinci sau uku ba, da zarar na zauna zanci wani abin zai zo ya dakatar dani haka dole Zan hakura na barshi. Bai Jima ba ya dawo da tray hannun shi, da sauri na Mike na karba sannan ya juya ni kuma na aje na koma inda na tashi ba tareda sanin abinda ya kwao ba, Kara shigowa yayi da ledoji wannan Karan yace Kar na tashi. Ana a week to zaa fara bikin ya tambayeni wanne irin nama nake so, ni na fada Masa yadda nake so Dan gani nake gani ga nama me zai Hana ni naci nayi Kat, Amma duk yadda kake tunanin auren ya wuce gaban hakan, Ina ganin duk sabon da nayi da Abbah me ye bazan iya Yi a gaban shi ba.Da kanshi yayi Mana serving cikin plate daya ya saka Mana fork biyu, na kalla Naman naji wani salivation ya cika min baki, dauka yayi ya fara kawo min bakina, nayi saurin sunkuyar da kaina nace

ZUMAWhere stories live. Discover now