Twenty five

968 157 4
                                    

🍯 ZUMA 🐝
Twenty five

✍🏻Ayshatuuu😍

Ranar Thursday, ita ce ranar dana kammalla final exams dita cikin BUK, paper safe ce so wajen karfe goma mun gama mun fito, muna tsatsaye gaban hall din se pictures muke yi wanda muka dan kara sabawa dasu muna exchanging contacts da social media handles. Wajen sha daya Hibba taja hannuna mukai sallama da sauran muka nufi hostel dan na kara tattara kayana saboda Daddy yace min se wajen 2 zasu daukata. Muna dab da karasawa hostel naji ringing din wayata , da sauri na ciro wayar ina sakin murmushi me kayatarwa, banma dauka ba se wulla idanuna da nake across gurin dan nasan zuwa yayi shiyasa yake kirana. Can na hango shi jikin wata bishiya tsaye ya kara wayar shi a kunnen shi, from all indications bai ma hango ni ba, kallon Hibba nayi dake cemin na daga wayar ita karar ta dame ta, nace

"Kinga Sahibi ne yazo muje gashi can"

Tabe baki tayi tace

"Kauna jaraba"

And i smiled saboda nasan gaskiya ne abinda ta fada, ni kaina ina yawan mamakin wannan kaunar dake tsakanin mu, kullum ina cikin ayyana ya kamata na rabu dashi kodan Daddy amma kullum we're getting more and more closer to each other. Wajen shi muka nufa har lokacin bai lura damu ba seda muka zo gab dashi sannan ya dago ya kalleni ya sakar min murmushi nima banyi wata wata ba na mayar masa da martani wanda seda ya lumshe idanun shi. Hibba suka fara gaisawa sannan nima na gaishe shi ya amsa mana yana mana murna tareda mana adduar clearing dukkan papers dinmu.

"Hibba biki ya matso ko?"

Murmushi tayi tana dan kawar da kanta irin najin kunya dinnan. Se ni nace masa

"Two weeks kawai ya rage"

Kanshi ya gyada yace

"Allah ya sanya alkhairi, saura a manta dani baa gayuace ni ba"

Wanann karon tace

"Kai! Zaa gayyace ka ma, su waye a gaba idan ba hanci ba"

Dariya sosae yayi jin abinda ta fada, daga karshe ya mika mata wata katuwar paper bag dake gefen shi wadda ni banma lura da ita ba se yanzun. Godiya ta masa ta wice hostel ta barmu muna ta hira, ko daga nesa ka hango ni kasan ina cikin madaukakin farin ciki, nidai a rayuwata babu wani mood turner irin kasancewa ta dashi, ko na ayyana nayi aure indai na hassaso wani namijin se inga kwata kwata he doesn't fit indai ban hasaso sahibi ba, se giggling nake. Akwai abinda ni kaina a tarrayyata da Sahibi dake bani mamaki, deep down cikin raina nasan ba auren shi zanyi ba, saboda nasan Daddy is man of his word, he meant dukkan abinda ya fada, amma na rasa dalilin da yasa nake kula shi, na take dukkan maganar da Daddy yayi min akan shi.

"Idan kika tafi se yaushe zamu kara haduwa kuma?"

Se na danyi jim dan nasan yanzun ba lalle mu kara haduwa ba tunda gashi zan bar kano na koma dutse baki daya.

"I dunno buh ai zan zo bikin Hibba zamu hadu lokacin"

Cikeda gamsuwa ya gyada kanshi se muka kara fadawa cikin hira wadda ta mantar dani cewar Daddy yana hanya zai zo dauka na, Hibba na daki itama tana jirana, gashi nayi kuskuren bata wayata ta tafi da ita, da at least ko da yazo zai kirani. Can naji hankalina yaki kwanciya se ina jin kamar one person da bana fatan ya ganni tsaye da Aliyu na tsaye yana kallona, cikin sauri na juya, Daddy na hango tsaye jikin motar shi ya zuba mana idanun shi masu kaifi, a take naji yawun baki na ya kafe haka kuma ilaharin jikina ya dauki rawa, and I know it cewar attack zan samu, hannuna na damke inajin yadda zuciyata ke bugawa numfashi na yana kokarin ficewa haka gumi ya min shrkaaf, Aliyu da bai lura da tsayiwar daddy ba dukda cewar shi ke facing Daddy din.

"Sahiba menene? Subhannallah!"

Ya fada hankalin shi a tsananin tashe, idanuna sun firfito waje kamar zasu fadi saboda yadda numfashi na ke kai kawo, Cikin sauri Daddy ya karaso gurin tareda kama ni na zauna sannan yace

"Take a deep breath dear"

Hannun shi na matse sosae sannan naja dogon numfashi a hankali se jikina ya fara daidaita har na dawo normal, sannan na saki hannun Daddy ina gaishe shi, Aliyu shima ya gaishe shi ya amsa normal sannan ya mana sallama ya tafi, na dubi Daddy wanda ke waya da Doctor daya taba duba ni yana ce masa na kara samun attack din, se yace masa yana jin tsoron kada ya zame min jiki dan repeated episode na panic attack yana komawa panic disorder.

Bai ce min komai ba naje hostel na dakko kayana muka fito da Hibba dake ta kokarin nuna min babu abinda Daddy zai min tunda kowa yasan menene soyayya kuma dole ayiwa wanda yake cikin ta uzuri, amma ina ni duk hankalina a tashe yake, ko sallamar kirki bamuyi ba ta gaida Daddy muka nufi dutse, saboda tsoron kada yace min komai na lumshe idanuna kamar bacci nake shima se ya maida hankalin shi akan wayar shi, time to time na kanji ya amsa kira.

Muna isa gida na manta ma abinda ya faru saboda yadda na samu su Amal an shirya min wani dan karamin get together hatta dasu Mom su Anty Sumayya duk suna gida da yaran su, Daddy ma ya shigo cikin mu yana ta taya ni murna amma duk lokacin da muka hada idanu da Daddy se naji kamar wani panic attack din zai so, a haka dai muka gama muka ci abinci sannan mukai picture na karba gift dina.

Da daddare Sahibi ya kirani, ina kallon kiran nashi na kasa dauka, se fargabar haduwata da Daddy da nake, mikewa nayi na ciciro gift dina ina dubawa, se naji hawaye ya sulalo min saboda yadda kowa ya tsara words jikin greeting card din da aka hada min a gift, na dudduba sauran sannan na dakko ta Aliyu abubuwa da yawa a ciki mostly perfs ne designers, tattarawa nayi na aje a gefe na fada duniyar tunani, anan kiran Daddy ya shigo wayata, saboda yadda gabana ya fadi kadan ne ban fado a gadon ba, kamar bazan dauka ba haka nayi amma ya zanyi dole dole haka na dauka.

"Ina parlor ki sameni yanzun!"

Se ya kashe wayar jikina a sanyaye na mike na saka abaya saman kayan jikina na fita, yana zaune akan sofa yana kallon network news, zama nayi bayan ya bani izini tun kafin yayi magana nce

"Daddy kayi hakuri dan Allah"

Kallona ya tsaya yana yi sannan yace

"So baku rabu dashi ba all this while? Nanah nayi tunanin idan nace ki bar abu ko meye zaki bari"

"Daddy wallahi it was a mistake kayi hakuri"

"Kina ganin ban miki adalci ba? Saurin me kike ? Saboda Amina zatayi aure ta barki gida...."

Na tsani wannan maganar nifa bawai aure nake so ba, ni Aliyu nake so kuma son shi ya fara kissima min nayi aure, a matsayina na yayar Aminatu dole tayi aure banyi ba zanji babu dadi tunda a society da muke hakan ma kamar wani kasawa ce daga bangaren ka ko kuma irin abominations ne.

"...Aure lokaci ne Nanah idan yazo ban isa na hana kiba, nasan kina cikin So shiyasa, but ina son kiyi amfani da kwakwalawar ki, duk matar da zata fito daga gidan ta ta taho uwa duniya dan tayi warning akan mijin ta ba tareda sanin shi ba to tafi karfin shi, bai isa da gidan shi ba, kina ganin saboda son da kike masa zai saka nayi trading dinki for that, bazan iya aura miki shi ba, aure is not a one year pleasure, it's staying with a single soul for eternity, waking up and looking at that face, it's beyond duk tunanin ki Nanah. Ina son kiyi hakuri kiyi addua nima as your father ina yi miki!"

Ayshatuuu

ZUMAWhere stories live. Discover now