RAMIN MUGUNTA
Short story
DEDICATED TO MUHAMMAD GADDAFI
EPISODE 11&12
Atare suka shiga cikin gidan, da sauri daddy ya 'karaso inda malam Ahmad yake ya mi'ka mishi hannu sukayi musahaba tukum yay mishi iso zuwa cikin gidan,
Ammi dake tsaye akan Mukhtar wanda keta faman mi'ka yana wasu surutai baka gane abinda yake fad'i ma, da sauri ta mi'ke ganin abban Mukhtar, drawer kayanshi taje ta d'auko mishi riga marar nauyi ta kawo sannan ta koma gefe guda ta zauna, saka mishi rigar abbanshi yay sannan ya kira malam Ahmad,
Bayan 'yan dube dube da malam Ahmad yay sannan ya d'ago ya kalli ammi cike da kad'uwa, tambarta ya farayi daman Mukhtar yana da iskane? Tunda Ammi taji batun Mukhtar yanada iskane ta 'kara kad'uwa tana girgiza kai, saboda in ta cema yana da iska tayi 'karya gaskiya bata da masaniya akan hakan,
'Dan jim kad'an yay tukum ya d'ibi ruwa a cup da karanta ayoyin Allaah ya watsama Mukhtar, nan da nan Mukhtar ya saki wani 'kara wanda seda na firgita sose, harda na banjama aguje se malam Ahmad ya kirani yana fad'in "haba antyn beauty ta mu keda baki gama d'aukan rahoto ba ina zaki? "
Zaro ido nayi waje kamar MUHAMMAD QADDAFI na kusa da ni nace mai "malam ai wannan lamari seku ina ni ina wannan 'katon aljan! Dan da ganinshi kaga 'kosasshe marar tausayi"
Dariya na malam Ahmad dan haka ya dara sannan ya d'auko al'kalamina ya mi'komin wanda na yar bansani ba garin gudu, ungu ki cigaba da d'aukab rahotonki, yace dani shiyasa na d'auka na koma daga bayan 'kofa ina sauraren abinda ze biyu baya,
Ran'kwashin Mukhtar malam Ahmad yay had'i da fad'in, "rufemin baki koh inci ubanka marar tausayi kawai, daga ina?
Cikin wata kalar murya kamarta dodonni aljanin yace "kai 'karamin halitta, kamar kai zaka tambayeni daga ina?"
Mqganar aljan! 'Din dana jiyo ba 'karamin murd'awa cikina yay ba wanflda har bansan sanda na fara tsinema inna asabe ba,
Ruqiyya malam Ahmad ya fara ma aljanin yana ihu yana fad'in zan fita zan fita, ka dena 'kona ni, zan fita dan allah, amman da sharad'in bazan fad'a maka wanda ya turoni ba, sede inaso in sanarmaka nine na haddasama Mukhtar muguwar sha'awar da harna tunzurashi ya aikata abinda beyi niyya ba, kamin rai malam jikina na 'konewa kana 'konamin jiki malam, haka aljanin nan ya dinga fad'i, malam Ahmad ko bedena karatun ba harsai da ya kai aya tukun ya tsaya da karatun ya d'ago idonshi da suka kama rinewa saboda tsabar 'bacin rai, al'kur'ani ya d'auko ya d'aurama aljanin aka sannan yace duk abinda na fad'a ka maimaita, "tom!" aljanin yace cikin rawar murua sannan malam Ahmad yace "daga yau, nan ma aljanin yace shima, na bar jikinta Mukhtar Ahmad Ma'karfi, inna sake dawowa, allah ka wula'kantani, Allaah ka 'kas'kantar dani, Allaah kajefani cikin halin ha'ula'i, Allaah ka yagalgala namana, haka malam Ahmad yasa aljanin nan d'aukan al'kawari tukum yay mishi wa'azi mai ratsa jiki, sannan ya umarceshi da yatafi masallacin saudiyya yaje ya nemi gafarar ubangiji,tukun ya umarceshi daya fita ta babban yatsan shi na 'kafa, babu 'bata lokaci aljanin ya ware sannan Mukhtar ya saki wata kalar ajiyar zuciya mai 'karfin gaske,
"Alhamdulillah Ammi ta furta idonta cike da hawaye, matsowa wajen Mukhtar tayi wanda yana bud'e ido sai kuma ya rufesu ruf alamun bacci yafara d'aukarsa,
Magungunan da abba ya siyo malam Ahmad yabama ammi sannan yanuna mata yadda za'ayi amfani dashi tukum ya 'kara da cewa "in Mukhtar yaji sauqi zuwa nan da kwana biyu ku turominshi dan nai mishi bayanin abinda ya faru, sannan ita yarinyar tana ina? Malam adamu ya tambaye Ammi,

YOU ARE READING
RAMIN MUGUNTA
Mystery / Thrillerlabari ne akan hassada keta da....... Ku biyoni dan jin abinda zai faru cikin littafin