Shafi na Ukku

15 1 0
                                        

RAMIN MUGUNTA

               

EPISODE 7&8

Wanda ake kira da d'an sholi direct gidan Mukhtar ya wuce dake bayan gidansu hanne, yaci sa'a kuwa yau babu kowwa acikin gidan, Mukhtar ya tafi office gate man d'inshi kuma yaje sayan abinci, haurawa yay ta katanga sannan yaje dede 'kofar babban falonshi ya binne layun da inna asabe ta bashi, ya simince wajen kamar ba'a binne wani abin ba,

Haurowa yay ya fito yana wa'ke wa'kenshi sannan ya nufi gidansu hanne, sallama yay ya sanarma inna asabe ya gama aikinshi, naira dubu da d'ari biyar ta d'auko ta mi'ka mishi, beko raina ba ya 'karama karenshi wuta tunda ya samu na zu'kar ta'ba,

Inna asabe ce ta fito da niyyar d'iban ruwan zafin da ta d'aura tayi wanka taga tukunya wayam babu komi,
'Kwalama salima kira tayi, fituwa salima tayi tana zum'bura baki kamar tsohuwar ja'ba tukum tace "wallahi inna mu kin cika shegen kira kamar tsohuwar mayya, wallahi allah wadai naka ya lalace, haba innarmu wannan ai sai mutuncin mutum ya zube, ni wallahi innarmu bazan iya fitowa in nunaki amazaunin uwata ba, haba dan allah jibeki fa? Kamar kin fito daga bakin kura, jibi yadda kika cire riga kikai tum'bur idan honeyna ya fito fa kice mini?"

Kinga naki nan salima ke wacce kalar 'yar iskar yarinyace shashasha? Na kiraki in tambayeki ko ke kika d'ibarmin ruwan wankan dana d'aura?"

Kema dai innarmu da akwai ki da wani kalan zance kije ki nemi wacce ta d'ibar miki ruwa ba niba, ta idashe maganar da buga tsaki ta wuce,

Hannece ta shigo gidan tana d'angyasa 'kafarta da takejin kamarta karye, tun daga kofar gidasu ta fara jiyo muryar inna asabe tana surfafa uban bala'i,

Shiga cikin gidan tayi bakinta d'auke da sallama, wani kukan kusa inna asabe tayi ta dam'ko wuyan hanne ta had'a ta da bango, dan kutumar ubanki ubanwa yace ki d'ibarmin ruwan wanka? Ke 'yar iskar inace?"

"Cike da kakari hanne tace wallahi innarmu baffa ne yay amai shine na d'ibo ruwan na wanke masa, wani gigitaccen mari inna asabe ta d'auke hanne dashi wanda sai da ya sata ganin wal'kiya,

Jibgarta tafara kamar allah ya aikota harsai da taga ta had'a mata jini da majina tukum ta saketa lokacin ta jigata da yawa, ubanki yaci uwarsa kinji? Sha sha sha jaka, maza ki tashi ga alalacan na gama ki d'au talla matsiyaciya la'analla fasi'ka kawai,

Haka hanne ta mi'ke tana wani kalan kuka mai tsuma zuciya ta d'auki tallar alalan ta tafi,

bafdan hanne dake d'aki yana jin abinda inna asabe ke fad'i ya share hawaye, ahalin yanzun baze iya ta'boka komai ba sedai yabi hanne da addu'ar allah ya kareta ya bata juriya da ha'kuri,

Take anan wani kalan zazza'bi ya rufeshi numfashin shi yay 'kasa sosai dagyar yake iya janyoshi, wani kalan kyarma jikinshi keyi miyau na zalala daga bakinshi, wani irin tarine ya sar'keshi mai tsanani, ahaka hanne ta shigo ta sameshi tunda yau kam ta dawo da wuri, da gudu ta 'karasa wajen baffanta tana tambayarsa lafiya? Baya iya cewa komi sai uban gumi yake fitarwa yana 'kara janyo numfashin shi, hannayenta ya ri'ke dukka yana murzawa, magana yakeson yayi amman ya kasa, lokaci d'aya idanuwanshi sukayi sama, wuyanshi ya karye jikinshi ya saki, lokaci d'aya yay wata kalar duguwar sha'kuwa sannan jikinshi ya saki yay la'kwas,

Ita ko hanne kallonshi kawai takeyi gaba d'aya in banda rawa jikinta daya d'auka kamar mazari, d'aga hannunshi tai taga ya koma dukka, mi'kewa tayi da sauri ta ruga gidan inna mai fure ta kirata dan taga halin da baffanta ki cike, koh da inna me fura dazo ta duba baffanta sai kawai taja bargon dake kusa dashi ta lullu'beshi, kana ta kama hannun hanne ta zaunar da ita bakin gado,

"Hanne inna mai fura ta kira sunanta cike da raunanniyar zuciya, ha'ki'ka ubangiji shike rayawa kuma shike kashewa, shiya fitarda rayayye cikin matacce, hanne allah ya fimu sanshi 'kaddara ta riga fata allah ya kar'bi abinsa, babu abinda baffanki ke bu'kata wajenki sai addu'a, ki d'auki qaddara ki rubutata cikin littafin qaddararki wannan itace qaddararki, ki kasance mai tawakkali ubangiji yana tare dake koh duniya gaba d'aya ta gujeki,

RAMIN MUGUNTAWhere stories live. Discover now