shafi na bakwai

28 1 1
                                        

RAMIN MUGUNTA


               Short story

                            Written by real auntyn beauty

(BURIN KOWWACE MARUBUCIYA AL'KALAMINTA YA 'DAUKAKA📝 NIMA INA RO'KON ALLAAH YA 'DAUKAKA AL'KALAMINA YA BANI IKON RUBUTA ABINDA ZE AMFANI AL'UMMAR ANNABI MUHAMMAD, KARKI KASANCE MEJAN DOGON LABARI, AMMAN KI KASANCE MAI ISAR DA ABINDA KIKESON ISARWA CIKIN 'KAN'KANIN LOKACI, BATARE DA KIN WAHALAR DA MAKARANTA BA, KUMA KIN WAHALAR DA AL'KALAMINKI BA, ALLAH YA SHIGE MANA GABA AMIIN)

DEDICATED TO MY LIFE ALKHAIRIN ALLAH YA KAIMA ADUK INDA KAKE AFA'DIN DUNIYAR NAN, ALLAH YA TSAREMIN KAI YA KAREMIN KAI YA KAWOMIN KAI LAFIYA, ALLAAH YA ALBARKACI RAYUWARMU DUKKANMU,


EPISODE 15&16

"Hannatu kice!"? Baba lantana ta kira sunan hanne cike da tsananin firgici, itama hannen ta firgita da ganin baba lantana kuma bata ta'ba tunanin zata sameta a irin wannan lokacin ba, shiyasa ta yarda butar dake hannunta tana d'ingisawa ta isa wajen baba lantana ta rumgumeta,

Kuka takeyi sose baba lantana ta bubbuga bayanta alamun lallashi, ita koh hajiya Amina tana can gefe ta saki baki galala tana kallonsu cike da alhinin abin,

Hajiya Amina ce tai gyaran murya dana fad'in kuka ba naku bane, ku godewa allah da har yasake had'a fuskokinku,

Baba lantace ta juyo ta bama hajiya Amina hankalinta gaba d'aya tana fad'in,
"Hajiya dole nayi kuka, mahaifin yarinyar nan ya kasance yana bani amanarta tun kafin yabar gidan duniya, koh da yaushe ya shigo gidana gaisheni yakan fad'amin yana ji ajikinshi bazeyi tsawon rai, ga amanar hannatu nan ya barmin, in kulamai da ita, allah ne gatanshi nice gatanta, dan haka inkulamai da ita, d'an shiru d'akin ya d'auka sakamakon kukan da hanne takeyi, sallamar Alhaji Shu'aibu Shanono ce ta dakatar dasu daga maganar da sukeyi, tare da Ammi mummy harma da abban Mukhtar da twins suka shigo saboda, hutunan hanne da aka sanya akafar yad'a labarai yanar gizo, kasuwanni makarantu, Alhaji Shu'aibu Shanono ne yaga hoton ta ma'kale anyi babbanshi ansagala awajen masu saida kayan marmari wajen titi, bayan ya wuto yana mamaki kuma se gashi d'aya daga cikin yaran da aka baza afad'in unguwanni in sunga mutane su dinga nuna musu hotun har allah yasa adace,

Bayan ya d'auki number abban Mukhtar ajikin huton ya kira nan da nan abban Mukhtar ya d'auka jin muryar abban Mukhtar yasaka Alhaji Shu'aibu Shanono tambayar shi ko yasan hanne ne? Nan yake sanarmishi da yasanta sannan ya bashi labarin duk abinda yafaru be 'boyemai komi ba, dan har saida su ammi sukaje gidan sannan Alhaji Shu'aibu ya umarcesu su tao su tafi asibityn zama ba naso bane indai itace toh tana hannunshi, kuma tana asibity, nan ya basu labari ya fito ganin garine wani me mota ya kad'e hanne akan idonshi sannan ya gudu beko tsaya ba, haka suka tartaro suka nufi asibity shima suna zuwa suka tadda hanne da baba lantana suna kuka, Alhaji Shu'aibu ne ya hana kowwa shiga saboda yadda ya gansu dagani akwai sha'kuwa mai 'karfi tsakaninsu, shiyasaka suma suka tsaitsaya sunajin wannan labarin me cike da tausayi,

Gyaran murya alhaji yay sannan yace "ya kamata kibar wannan kukan lantana, abinda ya kamcemu yanzu kowwa ya kwantar da hankalinsa, zuwa anjima in an salami hanne se mu d'unguma mu tafi gidansu mu maidata wajen iyayenta,

Haka koh akayi duk suka firfito da kayan abincin da baba lantana ta kawo suka juya abbar tray kamar yadda suka Sabah koh da yaushe yauma hakance ta kasance, had'a hannu sukayi harda alhaji da hajiya amin a dasu baba lantana suka fara cin abincin dan dama sun Sabah hakan,

Ita koh ammi tayi shiru daga can gefe ta samu ta zauna, duk wani motsin hanne akan idonta takeyinshi, ga twins da suka ma'kale hanne sun hanata sa'kat komi satai zasuce anty dan allah karki 'kara tafiya ki barmu, tun abin baya ba hanne haushi harta zamto yana bata haushi ta sunce anty dan allah karki tafi kibarmu setace "kunaso intsaya d'an iskan yayanku ya 'kara lalatamin rayuwane?  Koh koh kunaso in zauna cikin rashin 'yanci ne, ta fad'a tana fashewa da kuka sose wanda har sai da yasa mummy rumgumeta itama dana fitar da hawaye cike da ba'kin ciki, allah wade da rayuwa irin ta ta, ba wanda ya saka mukhtar cikin wannan halin se ita, bataji haushin mukhtar ba kamar yadda taji haushin kanta, abin na sosa ranta yana mata 'kona azuciyarta inta tuna abinda ya faru, dan ma yarinyar akwai tawakkali bata saka kanta cikin wani hali ba, dan duk abinda allah ya tsarama bawansa toh tabbas shike kasancewarta seda kayi fatan allah ya sauya maka qaddara daga mara kyau zuwa me kyau,

RAMIN MUGUNTAWhere stories live. Discover now