RAMIN MUGUNTA
Short story
Written by ❤real auntyn beauty ❤
DEDICATED TO MUHAMMAD GADDAFI
EPISODE 13&14
Parking space ya nufa yay Parking d'in motarshi, fitowa yay ya zagayo ya bud'ema mummy sannan yay gaba abinshi,
Mummy kuwa kama hannun hanne tayi suka shiga ciki, idon hanne gam ta'ki yarda ta bud'e saboda karta had'a ido da Mukhtar wanda ahalin yanzu take mishi kallon dodo, ya cuceta ya gama da rayuwarta kuma tana ro'kon allah yay mishi abinda yay mata, marar imani da tausayi kawai,
Yam biyu dake zaune suna kallon tashar bollywood suka jiyo sallamar mummy, atare suka waigo suna kallonta kafin su ruga aguje suka rumgumeta suna fad'in "mummy wallahi munyi kewarki sose, shafa kansu tayi da fad'in toh ai gashi nadawo koh ba haka ba,? Had'a baki sukayi wajen cema mummy "la mummy wannan wacece?"
"Antynku ce mummy ta tsinci bakinta da cewa wanda itama tasha mamakin da har bakinta ya iya furta hakan,
Ita koh hanne kanta adu'ke ta'ki koh d'agowa ta had'a ido dasu, ita ahalin yanzu hutu take bu'kata, zuciyarta ba 'karamin zafi take mata ba da 'kona, Mukhtar ya riga ya rabata da darajarta, ya rabata da 'kimarta, ya rabata da komi na matsayin 'ya mace, inta tuna rayuwar da zata fuskanta nan gaba, da wacce zata fuskanta in inna asabe ta gane halin da take ciki gaba d'aya se taji tausayin kanta ya kamata, ta kam rasa kuzarinta da duk wata 'kwarin gwiwarta, hawaye ta share akarona babu adadi,
Fisge hannunta tayi jikin mummy ta runtuma aguje, kafin mummy tai wani abin tuni ta dunfari gate tana wani kalan kuka mai ban tausayi, bata da uwa ba uba ga wannan halin da Mukhtar yajefata,
Tana zuwa bakin gate tayi wani kalan tsalle kafin gateman yay wani 'ko'kari harta 'balle,
Hankali amatu'kar tashe mummy da 'yam biyu da Ammi wacce itama shigowarta kenan cikin gidan suka rufama hanne baya,
Gudu takeyi da iya 'karfinta, wanda tana jin ciwon dake 'kasanta na mata wani kalan zafi kamar ta fama, cikin minti biyar hanne ta 'bacema su mummy gaba d'aya bata babu alamunta,
Su mummy sunyi neman hanne sunyi neman duniyar nan amman basu ganta ba, juyawa sukayi suka nufi gida hankalin kowwa atashe, babu wanda ya iyama wani magana cikinsu har agogo ya buga 'karfe 9:30 na dare,
Mukhtar keta faman rizgar kuka a part d'inshi, hakan ya zame mishi al'ada tun bayan da abin nan ya faru kullum seyay kuka kamar ranshi ze fita tukum zuciyarshi take rage rad'ad'i, kuka yake yana wasu kalar magangunu mararsa amfani,
ganin kukan baze mishi bane ya mi'ke ya shiga toilet d'auro alwallah yay sannan ya fito ya shifid'a sallaya ya tada sallah,Ita koh hanne bayan ta fita a unguwar su Mukhtar tana gudu wanda dagani hankalinta ba'a jikinta yake ba, seda ta tabbarta tayi nesa da unguwar tukum ta sami wani waje ta zauna tana maida numfashi,
Bayan kamar minti goma sha biyar taga wani saurayi yazo wucewa, tsaidashi tai ta tambayeshi dan allah nan wata unguwa take? Unguwar rimi ya bata amsa yana niyyar wucewa, tsayar dashi ta 'karayi ya tsaya sannan tace mishi dan allah in zanje hayin rigasa ta ina zanbi?
Kwatance yay mata dalla dalla, sannan tai mishi godiya ya tafi, mi'kewa tayi ahankali ta fara tafiya tana share hawaye gabanta na wani kalan fad'uwa kamar ze fito saboda bata san abinda zataje ta riska agida ba, tana tsaka da tunani harta hau kan titi bata sani ba, wata ba'kar mota me shegen kyauce ta taho aguje ta d'auke hanne ta yar'bar da ita akan titi,

YOU ARE READING
RAMIN MUGUNTA
Misteri / Thrillerlabari ne akan hassada keta da....... Ku biyoni dan jin abinda zai faru cikin littafin