Duk inda ta taka sai jini ya zuba hakan ya tabbatar masa da cewa ba ƙaramin jini ke zuba a jikinta ba,gudu take sosai tamkar ba mara lafiya wacce ta haihu ba, Yadda take indai ba ficewa tayi daga hankalinta ba babu shakka zai iya cewa aljanunta ne suka ƙara mata gudu ganin yadda take gudun ko joyowa ba tayi, Duk yadda yaso yacim mata kasawa yay sai nisa take masa,kasan cewar harabar gidan nada girma sosai yasa tun daga nesa yake ƙwalawa mai gadi kira,amma ya makara sabida Malam Habu yana ɗakinsa yana sharara bacci kamar matacce,ganin harta isa bakin ƙofar wajan gate tana shirin buɗewa yasa Alhaji Kabeer buɗe murya iya ƙarfinsa jikinsa duk rawa yake cikin kiɗima da firgici yace,
"No!! Zulfa stop kada ki fita bakki ganin halin da kike ciki ne?zoga babbynmu na kuka ke kaɗai yake buƙata,ke ya keso yaji ɗumin jikinki come back please my dear innalillahi wa'inna ilaihir raji'un meke shirin faruwa da Zulfana menene hakan?wanne irin gudu ne haka?ya rabbi ka kawomin ɗauki"
ya faɗa idanunsa na kawo hawaye,ina Zulfa kam sam bata cikin hayyacinta balle taji abinda yake faɗa,domin da zarar tayi niyyar juyawa sai taji ihu da gurnani sun cika mara kunne,can gabanta kuma wata inuwa da kuma tarin bishiyo haɗi da furanni masu ƙyau take ganuwa,abin mamakin idan ta kusa da bishiyoyin sai taga sun ƙara yi mata nisan gaske,hakan tasa take ƙara gudu domin ta isa garesu cikin sauri tasa hannu ta buɗe ƙofar dake jikin gate ɗin,tana buɗe ƙofar ta fice da gudu.Layine irinna masu kuɗi babu kowa duk suna cikin gida jensu hakan ya bawa Zulfa damar damar gudu a tsakiyar layin a haka harta isa babban titi inda manyan motoci suke shigewa.
Ɓan garan Alhaji Kabeer duk yadda yaso ya buɗe ƙofar gate ɗin kasawa yayi sabida cijewa da ƙofar tayi sakamaƙon rufewar da Zulfa tayi mata da ƙarfi wajan fita,cikin zafin nama yasa ƙafa ya daki ƙofar nan take ƙofar ya buɗe hakan yay dai-dai da lokacin Malam Habu mai gadi ya fito daga cikin ɗakinsa hannunsa ɗauke da gora yana shirin kaiwa Alhaji Kabeer duka a tunaninsa wanine ya shigo gidan kasan cewar bacci yake shiyasa bai gane waye a bakin gate ɗin ba,cikin sauri haɗi da jarumta Alhaji Kabeer ya fice daga cikin gidan tare da soma ke waye layin yana faman ƙwalla kiran sunanta Zulfa!! Zulfa!! Zulfa!! amma babu ita babu labarinta,Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un ya fara ambata a fili,ina zashi?ina zai ganta?wazai tambaya?shin mene ma ya fiti da ita a halin da take ciki?menene ya sameta?wannne irin firgicine haka wanda har zai saka ta manta da “ƊAN” data haifa,ya rabbi ka kawomin ɗauke wannan wanne irin abune haka?meke shirin faruwa ne damu baki ɗaya,zubewa yay a tsakiyar layin tare da kifa kansa a tsakanin cinyoyinsa duk yadda yaso ya daure kasawa yay,cikin raunin zuciya ya fashe da kuka,ya ɗauki a ƙalla kusan 30minutes yana durƙoshe kafin ya miƙe da sauri tare da ɗaukan wayarsa dake cikin aljihu ya fara dailing wata number,ringing ɗin farko akai picking call daga can ɓangaren Acp Anwar ya gyara tsaiwarsa tare da saurin ɗaga hannu ya buga ƙafa yace.
"Evening sir fatan lafiya? domin na daɗe banga miss call naka ba"
Numfashi Alhaji Kabeer ya sauke mai ƙarfi tare dasa hannu ya share zufar dake bin saman ƙoshinsa,gaba ɗaya jikinsa rawa yake kallo guda zakai masa kasan cewa baya cikin hayya cinsa,ga kuma tsantsar tashin hankalin dake yawo cikin ƙwayar idanunsa,lokaci guda duk ya sosoce tamkar ba Alhaji Kabeer Mai atile ba,ga yadda narkakkun idanunsa suka sauya kala daga fari zuwa jaa jijiyoyin kansa sun fito sunyi raɗa-raɗa,jin yay shuru babu alamun zai magana yasa Acp Anwar ƙara kamewa waje guda haɗi girgiza kai cikin kiɗima shima ya ƙara faɗin.
"Sir are you okey?komai dai-dai ne ko?"
Ya ƙara faɗa cikin hausar shi wanda baya fita sosai,ajjjiyar zuciya Alhaji Kabeer ya sauke tare da fesar da iska daga cikin bakinsa murya na rawa yace.
"Acp munyi missed Zulfa yanzu,ka yaɗa photonta da ba yananta a kafafen sada labarai redio,t.v,social media,gaba ɗaya a baza rahotanni kota ina,wannan ya zama breaking news kada kayimin wasa Anwar rayuwata na rasa,ina tabbatar maka idan har Zulfa tayimin nisa tabbas zan iya shiga wani hali,zuciyata ba zata jura ba,ina gaya maka hakanne domin ina maka kallon ɗa a wajena bana da kowa wanda zai shigemin gaba,ka tabbatar duk inda tashoshin mota,jirgi,suke kasa an rufesu duk da mana da tabbacin zatai nan wajan"
zubewa Acp Anwar yay akan sofarsa dake makeken office ɗinsa,Aunty Zulfa missed?wannan shine tambayar daya kewa kansa amma babu amsa,shi kansa rayuwarsa tana cikin wani hali indai ba aga Zulfa ba,domin itace shedar kawai data rage masa akan damuwarsa itace garkuwarsa wacce zata tseratar dashi tayaya wannan abun zai faro,anya ba sanya hannun wasu akan wannan labarin,numfashi ya sauke tare da faɗin.
"Amma baka ganin aƙwai sa hannun wasu cikin wannan abun?tayaya mace zata gudu a lokacin data haihu lokacin daya dace ta zauna ta huta a kuma kula da ita,tayaya uwa zata gudu tabar ɗanta gaskiya nidai ina shakku akan wannan matsalar"
Cikin ɓacin rai da kuma takaicin abinda Acp Anwar ya faɗa,Alhaji Kabeer yay sauri daga masa tsawa ta hanyar faɗin.
"Kai!! banson zancan banza,shikenan Ubangiji bazai taɓa jarabtar bawansa ba sai ace wanine dalili ko kuma wani yay asiri,babu ruwana da wannan shirman kabarni da abinda na keji kada ka ɗuramin hakkin wasu akaina haka kurum,Allah shi kaɗai yasan abinda yake ɓoye,kafin nan da awa guda ina son na sami labari akan Zulfata"
Yana faɗin hakan ya kashe kiran kana ya juya ya nufi gidansa,yana zuwa ya shige cikin part ɗin Zulfa inda Mameey ke zauna tana faman jijjiga babbyn daya keta faman tsala kuka duk ya cika gidan.