Zaro idanu waje tayi cike da mamaki da sauri ta miƙe tsaye tare da zuge wata ƙaramar ƙofa dake jikin door ɗin bathroom ɗin,a hankali ta leƙa a tsaye ta hangesa yana kallon mirrow ba tare da tasan abinda yake ba kasan cewar ya bata baya,cikin ƙwanciyar hankali tace "Jalal.."dadaran idanunsa ya ɗaga wanda sukai jaa sosai ya zubawa mirrow'n idanu, ta mirrow'n kuma yake hangen ƴar Kofar da Mameey ke leƙensa lumshe idanunsa yay tare da sakin murmushi har saida beauty points ɗinsa suka loma,ba tare kuma da yace komai ya ƙarasa wajan ƙofar ya murza key ya fito,ajjiyar zuciya tayi tace "kaban tsoro bobo what did you do inside the bathroom? girgiza kai yyi yana nufar parlour yace "babu fa" itama ba tace komai ba tabi bayansa har zuwa parlour'n, gaba ɗaya su Imran suka tawo wajansa da gudu suka rungomesa "ayyya bafiiii ciwooo ko" cewar Irfan, ɗan waro idanu bobo yay tare da shafa kan Irfan yace "shirme kawai naji sauƙi fa"kallon Aryan yyi daya kafesa da idanu yace "ohh hello darling"ya faɗa ya tafa hannunsa kwaɓe fuska Aryan yyi kafin shima ya shige jikin yayan nasa suka haɗe su huɗu waje gudu abin sha'awa "ohhyaa guys Les go" Mameey ta faɗi hakan tana yin gaba, binta sukai a baya ya zamana Jalal shine na ƙarshe yana tafe kamar baya son tafiya hannunsa dafe da mararsa sai lumshe idanu yake,kai tsaye makaranta ta kaisu kafin ta dawo zuwa gida.
da yamma misalin ƙarfe biyar Jalal ya fito compund cikin shigarsa ta farar jallabiya kansa ya sha gyaran da Mummy tayi masa, direct wajan baba Habu ya zauna yana mai sauraran wani news da akeyi a gidan redio a nan yaji mai labaran yana faɗin "hukumar gwamnatin ibadan tana neman yara masu kimanin shekaru biyar zuwa goma domin ɗaukan su zuwa karatu a ƙasar Paris as valunteer,haka kuma duk yaron daya fito da 1st class hukumar zata ɗauke sa ta bashi aikinyi wanda yaga dama" haka yaci gaba da jin labarin a kuma lokacin ya haddace email ɗin da suka bada domin kowa ya tura baya nan sa, baba Habu ne yyi saurin faɗin "wa yaga al'ƙawarin ƴan nepa..., atoo kuyi komai lokaci ne mudai ana watsa mana ƴar yafin shinkafa zamu kaɗa maku ƙuri'a" kallonsa Jalal yay ba tare da yace komai ba, ƙara gyara zama baba Habu yyi yace "sannu boba kai a rasa sunan da za'a saka maka sai na wannan abin zuƙar,ina ruwan ɗan Maraya aida idanuna biyu aljanun suka ɗauki mamanka da gora zan rakasu,ai kaga tun lokacin basu dawo ba,yoo to nima ɗin ai Sheikh ne a ƙauyan mu kaji siminin da ake karantawa aljanun ko NASI KO FATIHA ai saba'in ɗin nan na hadda ce ta"miƙewa Jalal yyi tare da gyara zaman farin glass ɗin idanunsa yace "sittin dai"yana faɗin hakan ya shige cikin gida sabida kiran magrib da akai,babu kowa a main parlour sai Imran yana bacci tashinsa yyi yace "time for paryer" da sauri ya kama hannun bobo suka nufi upstrais part ɗin Abbou suna zuwa yana fitowa daga bathroom al'wala suka ɗaura Jalal kuma ya nufi bedroom ɗin Abbou ya fesa parfume kana ya biyosu a baya,dwonstairs a nan suka samu Aryan da Irfan gaba ɗaya suka nufi masjid ɗin dake wajan gidansu.gaba ɗaya a zaune suke saman babban daining table suna dinner "mene? hauka ake da za'a bar bobo karatu har zuwa paris babu inda zashi" Mummy ta faɗa lokacin da take kai glass cup bakinta da niyar shan lemon inibin da tayi masu ɗazo, haɗe rar Jalal yyi tamkar babba kuma tsill ya gagara faɗin ko "A" sai juya strawberry ɗin da aka yanka masa ya kasa cin koda ɗaya ne, Abbou ne ya kalli Mummy yace "idan yaro yazo da abu ba'a gwasalesa da a kudu ne iyaye sunwle suke neman shawara wajan yaransu sabida hakan na ƙara buɗa masu ƙwaƙwalwarsu, Ni anawa ganin abarshi yyi abinda ya keso is better" cikin yanayin damuwa Mummy tace "amma tayaya ne zai iya kula da kansa? kai kanka wani lokacin birkici maka yake,yaya kake ganin ace babu wani family nasa.." ta ƙarasa maganar cikin raunin zuciya,domin har zuciyarta bata son tafiyar,girgiza kai kawai Abbou yyi domin daman yasan za'a sha wahala da Mummy "manyan makarantu irin wannan aƙwai kula,domin abinda za'ai wa mutum acan ko gaban iyaye sai haka, addu'a shine kawai ya dace da Jalal" cewar Mameey,ganin da gaske kuka Mummy kesonyi yasa Jalal miƙe ya ƙarasu inda take zaune, murmushi yyi kafin yace "my ambition is ur ambition too zaki farin ciki wata rana"gaba ɗaya kallonsa sukai domin Jalal idan yay magana saika rantse ɗan shekara Ashirin ne bayan ko 6yrs bai rufe ba,yana faɗin hakan ya shige part ɗin Abbou,abinda masu sani ba Jalal ya daɗe da tura baya nansa ta email ɗin da suka bayar.