_*AƘIDA TA*_
PERFECT WRITERS ASSOCIATION
(WE AIN'T PERFECT BUT WE ARE ALWAYS TRYING OUR BEST, TO MOTIVATE AND ENTERTAIN OUR READERS)
https://www.facebook.com/Perfect-writers-association-100452275039839/
*Story and written by*
_*AISHA HUMAIRA
(Daddy's girl)*_The experience writer of
*ABDUL JALAL*
* WATA KISSAR.... (SAI MATA) *
And now
*AƘIDA TA *I dedicated this book to my Mum
(Malama Nafisat Adam Muhammad) i love you mumHaƙƙin Mallaka ⚠ : Littafin nan mallaki nane, tun daga sunan labarin zuwa abunda ya ƙunsa, ban yadda wani ko wata ya sauyamin ko yin Amfani da wani ɓangare na labarin ba ba tare da izinina ba, Nagode
https://www.wattpad.com/user/Ayshercool7724?utm_source=android&utm_medium=link&utm_campaign=invitefriends
PART1
Page 7Da sauri Yusuf ya koma gurin partyn ba tare da fargabar komai ba ya shiga kutsawa yana neman Widad, amma babu ita babu alamar ta a gurin, can ya hango Nurat tana ƙoƙarin fita, seda ya bari ta fito daga gurin party, sannan yabi bayan ta a guje ya sha gaban ta, seda ta tsorata da ganin sa ta ɗan tsaya ta kalle shi tace "Are you ok?"
"Ina Widad?" ya jefo mata tambayar
"ban sani ba na barta akan stage tana rawa" tai maganar cikin wata irin gurɓatacciyar hausa.
Subhanallah shine abunda Yusuf ya furta, yai gaba yana sake duba gurin.
ba zato ba tsammani ya shammaci Nur ya fizgota ya shiga cikin duhuwar flowers da ita, yasa hannu ya shaƙeta, ya kalle ta a hasale kamar wani mahaukacin zaki yace
"Ko ki gayamin gaskiya ko kuma zan fita dake daga gurin nan, zan riƙe ki a matsayin garkuwa harse Naga Widad, idan kuwa rayuwar Widad ta salwanta taki ma ta salwanta, ki gayamin ina take?"
Yai maganar cikin ɗaga murya tare da shaƙe Nurat."Dan Allah, please don't kill me I will tell you, please secure my life"
"Your life will be secured if you tell me the truth" ya faɗa yana zare mata ido
Cikin kokawa da numfashi tace "Ok zan gaya maka, Dad ne yasa aka busa mata wani abu, yanzu tana harabar gurin nan a ɓoye, wasu zasu zo su ɗauke ta, idan baka hanzarta ba komai ze iya faruwa"
"Meyasa Mahaifinki yake ƙoƙarin sace ta?"
Cikin kuka tace "I sure to the Almighty ban sani ba, trust me"
Tasa Nurat yayi a gaba ta nuna masa ƙarƙashin bishiyar da aka ajiye Widad, tana kwance helplessly a ƙasa, unconscious kaman babu rai a jikin ta, ga jakar ta a gefen ta.
Ya waiga ba kowa a gurin, Yasa hannu ya sunkuce ta ya tafi da ita motar su da sauri, ya buɗe bayan motar ya kwantar da ita, yaja motar da gudun tsiya ya bar gurin.
Da gudu Nurat ta koma cikin gidan su tana haki, da yake hall ɗin party a cikin gidansu yake, ɗakin ta ta tafi kai tsaye ta shige banɗaki tana sauke numfashi, ta wanke fuskarta, ta buɗe fridge ta sha ruwa me sanyin gaske, sannan ɗakko wayarta ta kira layin mahaifinta.
Seda ta kusa tsinkewa sannan ya ɗaga yace
"Yaya i hope everything is going according to how it's planned?"Cikin rawar baki tace "No Daddy something is going wrong"
Cikin sauri yace "meya faru?"
Cikin Rawar Murya Nurat tace "Daddy basu ƙaraso da wuri ba, nayi abunda kace Amma..
" Amma me? Ki gayamin menene? "
" Daddy ita da wani tazo, nayi abunda kace, but someone intimidate me, yace in ban faɗi inda take ba ze kashe ni"
"Waye shi?" ya faɗa a fusace
"Ban sani ba Daddy, Amma tare suka zo"
"Wace irin wawuya ce ke haka? Kinsan lokacin dana ɗauka ina wannan shirin? Idan wasu suka rigani mallakar Abun nan mun kaɗe"
"Daddy ba laifi na bane, laifin wanda ka turo su ɗauke ta nefa"
"Shut up, kin ɓata min shiri kina gayamin maganar banza"
"Am Sorry Dad is not my fault, but....
" Common Keep quiet " ya faɗa a Hasale, tare da katse wayar yana tsaki, tabbas ba dan wawancin nan 'yar cikin sa ce ta aikata masa ba da ba abunda ze hana yasa a Kashe ta.
A fili Yace
"dole in toshe duk wata kafa da zesa su Alhaji Haruna su san nayi yunƙurin sace Yarinyar nan ni kaɗai, kuma dole in gano wane yaron ne suka je gurin tare"
YOU ARE READING
AƘIDA TA
RandomLabarin wata matashiyar budurwa 'yar hamshaƙin attajiri me murɗaɗɗiyar AƘIDA, Tace So imagination ne da ɓata lokaci katsam.......... 😜 find out in AƘIDA TA labari me ɗauke da cakwalkwalin sarƙaƙiya, yaudara cin amana, fuska biyu kutsen ƙaddara me s...