7&8

64 1 0
                                    

🔆 *WིྀAིྀYིྀAིྀ KིྀAིྀSིྀHིྀEིྀ ZིྀAིྀHིྀRིྀAིྀ'Uིྀ*🔆
➿➿➿➿➰➰➿➿➿➿

*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻   

          *ᴢᴀʜʀᴀ ᴀʙᴅᴜʟ*( *Պ✺Պ⑂ℵ ᾰℏℓᾰℵ*)

_my wattpad_@Fateemah0

*marubuciyar*

*H̸͟͞A̸͟͞L̸͟͞I̸͟͞T̸͟͞T̸͟͞A̸͟͞ D̸͟͞A̸͟͞G̸͟͞A̸͟͞ A̸͟͞L̸͟͞L̸͟͞A̸͟͞H̸͟͞ N̸͟͞E̸͟͞*
*G̸͟͞U̸͟͞D̸͟͞U̸͟͞ A̸͟͞ J̸͟͞E̸͟͞J̸͟͞I̸͟͞*
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
*N̸͟͞I̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞ K̸͟͞A̸͟͞N̸͟͞N̸͟͞A̸͟͞N̸͟͞ M̸͟͞I̸͟͞J̸͟͞I̸͟͞N̸͟͞A̸͟͞*

A̸͟͞n̸͟͞d̸͟͞
       N̸͟͞o̸͟͞w̸͟͞

*w̲̅a̲̅y̲̅a̲̅ k̲̅a̲̅s̲̅h̲̅e̲̅ z̲̅a̲̅h̲̅r̲̅a̲̅'u̲̅*
____________________
_sadaukarwan wannan littafi ga jarumai masu yi mana posting wanda nasani da sanda ban sani ba *YAYA HAYAT, HASSAN ATK,HUSAIN 80K, MU'AZ* kuna dayawa amma gdy da jinjina Allah ya biya_
________________
_wannan book din ba free bane ga mai buqata zai biya #200 sai ya tuntube ni ta numb kamar haka_

      *_Maman ahlan_*
🤳🏻 08165550116
*__________________*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________*

*STILL FREE PAGE SEVEN~EIGHT*

Bayan an dawo daga maƙabarta, jama'a yan karban gaisuwa sai ƙara cincirindo akeyi.

Harta mai girma gwamnar kano da mataimakinsa sunzo yiwa Alhaji Aliyu MD gaisuwa,kasancewa gwamna da mataimakin sa aminansa ne.

Hatta mutanen da baya tunani zasu zo masa gaisuwa, amma sun zo masa jaje sun jajinta masa na rashin yar'sa da yayi, hakan  kuma ba ƙaramin dadi yaji ba,ganin yadda Zahra'unsa tayi jama'a dan ko da shugaban ƙasa ne ya tsaya a haka.

Dama kuma ance jama'a su ne shaidarka, duk wanda yazo badai ya fadi wani mummunar hali na Zahra'u ba sai dai yabonta.

Da washe gari ana kan karban gaisuwa, wata budurwa ta shigo da ihu da kuka,tun daga gate da aka a jiyeta a mota, kallo daya zaka mata kasan cewa tana cikin matsinacin tashin hankali.

Bata zarce ko ina ba sai upstairs, ta wuce su Umma dake zaune  parlour da wasu mata, parlour a cike yake, wasu su na zaune a kujera wasu kuma su na zaune a ƙasan carpet.

Umma tana ganinta ta sake sakin kuka, dan gani take kamar zata ga Zahra'u ,data ga *Sawwama* .

Da gudu sawwama ta ban kaɗe kofar dakin Zahra'u ta shiga tana ihu.

" Innalillahi wainna ilayhirrajiu!!
Zahra'u! Zahra'u! Zahra'u!!

" Dan Allah ku ce min bata mutu ba, wallalhi shekaran jiya mun jima muna waya da ita."

Umma! Umma! Umma!

Dan Allah ina Zahra'u?
Dan Allah wani ya fadamin mana ina Zahra'u !!? ta fada da karfi kamar a tsawace.

Jama'ar parlour'n ne aka fara ƙoƙarin lallashin Sawwama ,amma fir taƙi sauraron kowa.

Sawwama tana kan yin nata suka ji kururuwa na tashi daga kan step tun kafin a hauro sama, Umma ta share hawaye ta ce . "ga Naina itama sai dai muyi hakuri amma Zahra'u yau kwananta daya a cikin ƙasa."

WA'YA KASHE ZAHRA'U?Where stories live. Discover now