17-18

44 0 0
                                    

🔆 *WིྀAིྀYིྀAིྀ KིྀAིྀSིྀHིྀEིྀ ZིྀAིྀHིྀRིྀAིྀ'Uིྀ*🔆
➿➿➿➿➰➰➿➿➿➿

*STΩRΨ ШRITTΣΠ βΨ*✍🏻   

          *ᴢᴀʜʀᴀ ᴀʙᴅᴜʟ*( *Պ✺Պ⑂ℵ ᾰℏℓᾰℵ*)

_my wattpad_@Fateemah0

*marubuciyar*

*H̸͟͞A̸͟͞L̸͟͞I̸͟͞T̸͟͞T̸͟͞A̸͟͞ D̸͟͞A̸͟͞G̸͟͞A̸͟͞ A̸͟͞L̸͟͞L̸͟͞A̸͟͞H̸͟͞ N̸͟͞E̸͟͞*
*G̸͟͞U̸͟͞D̸͟͞U̸͟͞ A̸͟͞ J̸͟͞E̸͟͞J̸͟͞I̸͟͞*
*S̸͟͞H̸͟͞U̸͟͞H̸͟͞A̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞*
*N̸͟͞I̸͟͞D̸͟͞A̸͟͞ K̸͟͞A̸͟͞N̸͟͞N̸͟͞A̸͟͞N̸͟͞ M̸͟͞I̸͟͞J̸͟͞I̸͟͞N̸͟͞A̸͟͞*

A̸͟͞n̸͟͞d̸͟͞
       N̸͟͞o̸͟͞w̸͟͞

*w̲̅a̲̅y̲̅a̲̅ k̲̅a̲̅s̲̅h̲̅e̲̅ z̲̅a̲̅h̲̅r̲̅a̲̅'u̲̅*
____________________
_sadaukarwan wannan littafi ga jarumai masu yi mana posting wanda nasani da sanda ban sani ba *YAYA HAYAT, HASSAN ATK,HUSAIN 80K, MU'AZ* kuna dayawa amma gdy da jinjina Allah ya biya_
________________
_wannan book din ba free bane ga mai buqata zai biya #200 sai ya tuntube ni ta numb kamar haka_

      *_Maman ahlan_*
🤳🏻 08165550116
*__________________*

*بسم الله الرحمن الرحيم*
*____________________________________*

*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
'''{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}'''
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
*____________________________*

*PAGE SEVENTEEN&EIGHTEEN*

Cikin hanzari Sardauna ya kwashi wayoyinsa ya fice, bai tsaya kiran yaransa ba, shi ka dai ya tafi.

Ban da gudu babu abun da Sardauna ke shararawa a hanya.

Yana shiga shoprite din, yayi wata karkacacciyar parking, ya fito ko kulle motar bai yiba, kalle-kalle ya shiga yi in'da zai hango Security Umar amma bai gansa ba,wayarsa ya ta kira amma kuma bai ɗaga ba.

Kiran Zayyan yayi  ya ce, "ku taho shoprite yanzu kai da Naina, yana gama fadi ya a jiye wayar.

A cikin minti20 sai gasu Zayyan da Naina, kamar an korosu.

Sun ƙara ɗibar kusan minti30, sai ga Umar din ya zo cikin hanzari.

Sardauna ya kallesa ya ce.
"Ka kirani nazo amma kuma ban ganka ba, ina Jangash din ya ke?"

Umar ya ce.
Ba shi kadai yazo ba shida abokansa ne, kuma su na zuwa basu jima ba suka fito zasu tafi bayan na kiraka a waya, shine nabi bayansu, tun ina binsu har danger ya tsai damu ,to fa daga nan suka bace min wallahi tun da su a motarsu suke ni kuma a cikin kekenapep nake"

Zayyan ya ce.
"Innalillahi yanzu ba kaga in'da suka bi ba?"

Umar ya ce.
'Wallahi ban gani ba amma tun da suka zo yau na tabbata zai iya ƙara dawowa ko wani lokaci kawai ku kasance cikin shiri."

Godiya suka masa kafin suka shiga mota suka koma station.

Bayan sun shiga office Sardauna ya ce. "inaji a jikina Jangash ya kusan kamuwa"

Zayyan da Naina suka ce. "Allah yasa haka"

Sardauna ya amsa da amin.

Dan tattaunawa suka yi kafin daga bisani Sardauna ya sallamesu.

Tun daga ranar da Security Umar  ya fadawa Dsp Sardauna, akan cewa yaga Jangash ya maida shoprite wajan zuwansa kullum shi da yaransa su na can, har aka kwashe sati.

Amma da shike hausawa su na cewa kwana casa'i da tara na b'arawo kwana daya tak na mai kaya.

Wata ranar laraba da Sardauna har ya ce ya gaji bazai sake zuwa ba shoprite ba, sai wata zuciyar ta ce masa, a'a Sardauna karka gaji shirya kaje.

Haka ya shirya cikin jeans and yellow t-shart, bayan yaje sun gaisa da Security Umar, suka hau dan taba hira, kamar daga sama Umar ya hango Jangash da saura yasa hannu yana tabo Sardauna.

Sardauna ya ɗago yana kallonsa,ya ce.
"Umar ya dai lafiya kuwa naga jikinka sai b'ari yake yi menene meya faru?"

Duk ya jero masa tambayoyin lokaci daya.

Umar ya ce.
"Jangash"

Wata zabura Sardauna yayi kana ya ce.
"A ina yake?"

Umar yayi masa nuni da kofar shigowa.

Nan Sardauna ya ɗago kai yana bin Jangash da kallo har ya ƙarasa shiga parking space, ya faka mashin dinsa, ya sauko daga kan mashin din.

Sosai Sardauna yake ƙarewa Jangash kallo,sanye yake da wandon jeans mai suna crazy tare da t-shart dinsa ita ma crazy.

Wani Shu'umin murmushin gefen baki Sardauna ya saki yana kan ƙarewa Jangash kallo,ga wani dan iskan askin dake kansa wanda ba zaka iya ganewa ba ko crus ne akan oho.

Waya Sardauna ya ciro ya kira yaransa ya ce, su taho shoprite yanzun nan.

Jangash ya kusan minti30 kafin ya fito hannunsa ɗauke da da gwangwanin coke yana tafiya yana sha.

Da sauri Sardauna yaje ya sha gabansa gami da cewa.

"Assalamu alaykum abokina"

Wani banzan kallo Jangash yabi Sardauna dashi har yana yamutsa fuska ,kamar ya ga kashi.

Cike da wulakancin ya ce.
"Kai kuma shashashan ina ne zaka zo ka wani tare min gaba ? wa ya gaya maka ana sha wa Jangashi gaba? hahaha yaro ka kama kanka jangash baya daukar raini yanzu na sa wuƙa na yanke maka ƙunne."

Yana gama fadi ya juya zai hau mashin dinsa, da sauri Sardauna ya cafko hannunsa.

Babu yanda Sardauna bai lallaba jangash ba ta cikin ruwan sanyi ,amma sam jangash yaƙi kulasa ,daga karshe ma jangash da Sardauna ya takura masa, hannu ya dunƙule ya kaiwa Sardauna naushi a baki, nan bakin Sardauna ya fashe sai ga jini.

Dariya Sardauna yayi ,sannan yasa hannu ya goge jinin gefen bakinsa, duk da haka bai sake Jangash ba yana riƙe dashi.

Kallonsa Sardauna yayi kafin ya ce.
"Haba abokina nifa tambayarka nake so nayi amma ɗauki maganar da zafi kayi hakuri"

"Ohh my god!
Cewar Jangash yana buga kafarsa a ƙasa yasa hannu ya dafe kansa.

Kafin ya ce.
"Okay okay fadi inajin ka amma kayi sauri idan ba haka jikin ka ne zai gaya maka"

Dariya mai sauti Sardauna yayi dan acting din Jangash yana burgesa,ganin yadda yake wani zaƙewa.

Sardauna ya ce.
"Shin kasan wata yarinya mai suna *ZAHRA'U YAR GIDAN ALHAJI ALIYU IBRAHIM MD*?"

Tsaki Jangash yayi sannan ya ce . "wannan na riga da na gama da shafinta, na rufe babinta har abada!

Sardauna jikinsa har ya ɗauki b'ari.

Ya ce.
"Dan Allah kasan gidan su ne?"

Wani irin dariya mai karfin gaske Jangash ya saki yana kallon Sardauna kafin ya ce.

"Kwarai kuwa harta iyakar adadin securities din gidan bodyguards din gidan nasani ko ba *Sharada p3* bane?"

Sardauna ya ce.
"tabbas shine so that you are under arest ya fada yana masa nuni da hankwa."

Kallon baka da hankali Jangash ke yiwa Sardauna.

Jangash bai kai ga  magana ba yaran Sardauna suka garƙamesa.


~~~~~~~~~

Kuyi hkr da wannan pls

Comments
But pls
Don't share

By Momyn. Ahlan

WA'YA KASHE ZAHRA'U?Where stories live. Discover now