👸🏻 👑🦚UWAR SARKI 🧝♀️🦚🐲Part(1)
Wannan labarin kirkirarene ba ayi shi domin musgunawa wani ko wata ba kuma muna fata baya kama da rayuwar wani ko wata muna fata Allah yasa muyi shi a sa'a.
Wannan littafin zai zo muku da sabuwar sigar da akajima ba ataba haduwa da irin ta ba dan zai zone da wata fuska ma'abociyar nishadantar da zuciyar mai karantawa.
Duk wanda ya karanta littafin nan nawa mai suna a sama nuna fatan xai mij Adduar karin basira.
ABUNDA MUKA FADA NA DAI DAI ALLAH YA BIYA MANA BUKATA WANDA MUKA FADA NA AKASINSA KUMA ALLAH YA YAFEMNA.
BAN YARDA WANI KO WATA YA JUYAMIN LITTAFI ZUWA WATA SIGA TA DABAN BA BATARE DA IZINI NA BA NA MAI LITTAFIN.
Written ✍️ by team Cyyy
🦚🧝♀️👑UWAR SARKI🦚👑🧝♀️ part one (1) 17/08/2020.
Yarinya ce yar kimanin shekara sha 16 Tafiya take yi a hankali kai dagani kasan a gajiye take sabode yunwar da takejii amma hakan bai hanata waka tanayi tana karkada sandar dake hannunta tana murmushi kafar nan tata tasha wani kunshi da ake kira wai tsohuwa ta fada kwata. Gidansu ta karasa wanda yake daf da shiga cikin garin nasu wato Iyawan Gabas wannan gari yana karkashin Masarautar Kano wanda mahaifin yarinyar mai suna malam haladu yake dagacin wannan kauyen kuma Allah ya bashi rufin Asiri dai dai gwargwado yana iyakar kula dasu.
Kofar gidan naga ta tura tashiga tana ta wuce wasu xauruka waje guda hudu daganan ta shiga ainihin farfajiyar tasakar gidan wanda yake da sassa daban daban a gidan sashen su ta nufa wanda shine na karshe a gidan sakamakon mahaufiyarta itace Amarya kuma cikon ta hudu a gidan nasu wanda yake da mata kala kala kowa dai yana zaune da halinsa. Kowa ta ciki ciki dan gidan ya hada da sashen inna sahura wacce itace uwar gida bata taba haihuwa ba sai kuma inna deluwa wacce tafikowa yara a gidan dan yaranta 7 ne mata 4 maza 3 saikuma inna sailuba itakuma yaranta 4 ne maxa biyu mata biyu sai babar mu kenn anace mata inna amarya amma sunanta na asali shine hassana mukuma mu biyune a gurinta nida kanina Aminu ni sunana shine NASREEN kuma mafi soyuwa a gurin mahaifina dan duk wasu sirrikan sa yana yawan gayaamin kuma shine malamina a gida dan yanada sani sosaii kuma ya iya hadawa da kwance tuggu kala kala shiyasa natsaya nake karantar sa.a komai kuma ba ayi masa karya batare da yakama mutum ba dan baban mu mainkaifin basira ne. Wannann kenn.
Ina kwance A daki babar mu taleko tace min ke dama bata fadar sunan saboda kara ta yan farii datake min "kije babanku yana kiranki" tafada tana sauke tabarman kabar dakin namu " daga kwance da nake na dirgo daga saman gadon karfe namu wanda yasha gyara na damesa yayi kyau nafito ina fitowa daga sashen mu naga fatahiya yayatce yar dakin inna deluwa ce nace wai ke fatahiyya baxaki bani kudina ba ko sai na hadaki da baba wlh xakisan da ne kike kudin nan anfi sati kinacewa zaki bani kuma har yau shiru nake kamar malam yaci shirwa nafada ina yi mata murgude "ke dallah can rufemin bakin nan naki yo kudin naki duka nawa ne kan wata naira ashirin dinki xaki dameni dallah gata nan zoki karba" tana fada tana kwance habar zani tana mikomin, karba nayi ina cewa "naji dai na fada ina cewa anki ai aure anxo ana ciwa mutane bashi" tace min me kika ce "bakomai " nafada ina karasawa turakar mahaifina.
Barakan mudai baban mu Yawau Nasreen nasara nai murmushi ina maijin dadin kirarin baban nawa nasamu gurinna xauna yaka tambayata yaya makarantar Allo ina dai zuwa ko nace wh wlh baba ina Zuwa kasan yanzu dayake lokacin ruwa ne bama yi in anyi ruwa gari yayi danmshi yace mata hakane kinga shin malam nata'ala din ya min maganar amma na shahantar amma zan gaya wa hakimin in nashiga garin insha Allah yauwa dama wasu yan littatafai ne na somiki da ajami akai rubutunsu ai zaki iya karantawa da anjima kuma zaki rubutamin wasika zan tafi da ita gobe garin. Tace to baban mu tace baba nidai dan Allah kaban labarun masarautar kano murmushi yayiii ya gyra zama yana mai cewa nasreen kenan narasa meyasa kike son labarin masarautar Kano amma insha Allah yau zan bakiii shi sai hankalin ya kwanta wani lallatace murmushi tayi wanda ya bayyana kyaywawan hakoranta masu kyau da sheki saboda tana yawan kula da tsaftar jikinta. Baban nata ya dora dacewa kamar ynda kike ji garin kano babban garine yana da kyau da tsaruwa da gine gine amma kallo yana fadar sarkiii gidane ne gidan sarauta katon wanda sai kinsaka garin nan namu a ciki sau goma yafada yana kallonta " ta ware ido tace "kai baban mu " yace mata "wlh " mana zan miki karyane ya cigaba da cewa a gidan sarauta akwai bangarori daa yawa na ma aikata akwai bangaren da suke girke girke(Royal kitchen) kenn sai kuma bangaren da suke da masu dinki da saka (Royal tailoring) saikuma bagaren da suke ma'aikatane wadanda yayan bayine da bayi na barorori (palace maids) kuma ko wanne bangare akwai shigaba ana musu take da jadiya kinga akenan kawai jakadiyar dinkunna jakadiyar abincii jakadiyar bayii ke da sauran ma jakadun da bansan aikinsu ba saikuma babbarsu kuma shugabat jakadun gidan itace Jakadiya babba suke cemata wacce itace ma take kusa da sarkin a cikin gida kuma al'adar gidan ta sha ban ban da wajen fadar sauran kuma inda rabo wataran na karasa miki kinga almuru na kawo kaiii baban ya karasa yana mai kallonta gaba daya ta nutsu tana mai kwadaitwa kanta son zuwa gidan sarautar Kano din amma ta ina ta yaya firgigit tayi ta dawo natsuwar ta sakamakon tabata da mahaifinta yayii tace tom baba bara na shiga ciki ta fada a sanda take fita daga dakin cikin magana da karfi tace ki turomun gyatumar taki Tom tafada tana wucewa.
Wata Safiyar laraba muka tashi gidan namu babu dadi sakamakon rashin lafiyar inna sahura duk muna dakinta ana tayi mata sannu baba ya fita shikuma nemo mota za asata akaita cikin gari zuwa wani asibitin sha katafi a duba ta.
YOU ARE READING
🦚👑🧝♀️UWAR SARKI🦚👑🧝♀️
RomanceLabari ne na gidan sarauta tare da wata rikitacciyar soyyayya mai ban sha'awabda ban al'ajabi ga nishadi da wa'azantar wa shin ko ya zata kasance da yareema Azeez dan sarki jikan sarki kuma yareema mai jiran gado tare da yar talakawa Nasreen wacce t...