Part 9&10

125 7 2
                                    

👑🧝‍♀️🦚UWAR SARKI👑🧝‍♀️🦚
Part (9) and (10)


ABUNDA MUKA FADA NA DAI DAI ALLAH YA BIYA MANA BUKATA WANDA MUKA FADA NA AKASINSA KUMA ALLAH YA YAFEMNA.

BAN YARDA WANI KO WATA YA JUYAMIN  LITTAFI ZUWA WATA SIGA TA DABAN BA BATARE DA IZINI NA BA NA MAI LITTAFIN.

Written ✍️ by team Cyyy


👑🧝‍♀️🦚UWAR SARKI👑🧝‍♀️🦚 Part (9) and (10)


Fulani saudat cikin daga murya da nuna ta isa da dan nata haba azeez sai yaushe xaka dawo ne ace karatu yafi shekara biyu baka gama ba sai kuma cikin sassauta murya kasan shirin mu fa bana so ace ana samun matsala yanxu dai saura kwana nawa ku gama ne ? Take tambayar dan nata cikin wayar daga can bangaren yace fulani kenan karatun mu ai yaxo karshe ma yanxu haka clearance muke a makanta da mungama zamu taho nanda 3wks ki kara hakuri kinji momyna ya fada yana shagwabar da murya "to allah ya kaimu" tace sannan ta kuma cewa 'kana kiran takawa (sarki) a waya ? eh ya bata amsa a kagauce sakamakon kiran budurwarsa dake shigowa xata kuma magana yace mata 'mum malamin mu na kirana bara naje' kit ya kashe wayar ya bi kiran yarinyar yana bata hakvr ita kuma hartayi fushi wai tadauka da mace yake waya dakyar ya samu ta hakvra suka shrya ina xasu hadu dan morewa soyayar su fulani saudat wayar ta sauke tana mai takaicin abunda yaron nata yayi mata hadimar ta ta kwalawa kira tace zo ki ban labarai ko raina yayi sanyi.  Yarinyar tafara bawa fulani labarai ji tayi labaran yarinyar sun isheta cemata tayi to alankosa baki iya komai ba sai surutu cace cace ni maza jeki kiramin kwarkwara asiya tafada tana gyara kwanciyarta angama uwar dakina ta fada tana tafiya domin cika aiken uwar dakin nata ita kuwa fulani a ranta tana kitsa yanda zatayi ta shawo kanta dan cimma wani kuduri da nata da taboye a ranta.  wasu hadimai naji suna cewa juna ta farkon tace ni wlh allah kayan kwalliyata sun kare ta biyun ma tace nima haka kuma gashi dilalya bata zuwa kwana biyu.  

Dilallaya ce zaune tana tafaman kokarin yin daurin nan mai step step dan yau tana so taje gidan sarki dan gayawa aminiyar ta shawarar data yanke wace tke tunanin itace mafita dan ganin sun mallake dan saurayin yareman kasa daurin tayi dan bata da hattara tayin hakan 'iro' naji takira sau uku ba amsa ba kamr tafasa gidan dan kururuwar kiran suna wani dan daudu ne naga yafito da gudu daga bandaki yana cillar da buta kira yake "mun shigesu dilalliya wannan kira haka sai kace kina nakuda, ko ni da xanyi aure yanxu wlh haihuwa baxata ban wuya ba ya fada yana tafa hannu' iro dan daudu dan hayar dilaliya ne suna xaune ne a gda daya xaman da kullum sai an raba hali dilaliya tace 'kajimin mahaukaci ina ka taba ganin dan daudu yayi aure har ya haihu ni dan allah  iro xoka daura min dankwali tafada tana mika masa ya tafa hannu yace yau akeyinta wai anbawa barowa ajiya an sace    kiga ma cimin mutunci na miki daurin dankwali kuma bana rabki da cemin kai ba ki dubeni sama da kasa na miki kama da kai yafada yana nuna kansa' Inxakice anty iro baby kice in baxakice ba kifasa yafada yana murgude to ya hakuri kinji anty iro  shiru yayi wa dilaliya ya karba ya tsantsara mata daurinta mai kyau ya ce ina xuwa kayan kwalliyar sa ya dakko ya zauna ya tsantsarawa dilalliya sai ga yar tshohuwa ta dawo kamr yarinya nagode iro au namanta anty iro katuwar jakarta ta rataya wa ta dakko tare da ghana must go dinta ta pito bayan ta yafa mayafi a kafada tana janyo dakin tana kulewa sai ina kuma jakadiya iro ya tambaya sanda yake wanke tukunyar da xai yi girki sai gidan sarki tabada amsa a takaice wai bata son yawan magana intayi kwalliya kartaje jan bakin ya baje garin yawan magana bakin titi tafita ta tsayar tana gwalli tace sarki house yce bngane ba tace gidan sarkin ne bka sani ba yace mata "  to baga gidan sarkin can ba tace nasani ai ba ta babbar kofa zan shiga ba tacan kofar kiraka zan shiga yace to hau muje tafiya sukai me dan nisa suka kawo wata kofar gidan sarkin wacce ta nan unguwar bayi ce da hadiman gidan dakuma manyan bayin sarki nan aka sauketa ta dauki naira 20 tabashi yace haba iya kudin ki hamsin ne haba yaro wlh bazan baka hamsin ba sai dai na karama ka goma inbaka iya karba kabarmin kudin kai Allah ya isa katafi abunka yace haka kika ce jeki Allah ya isa yaja ma shin dunsa ya wuce yana zaginta  da ita nayi arziki tafada da karfi dan ya jiyota tare da crwa kajimin yaro nan da can shine hamsin dayake kudij a ruwa ake tsamosu ta juya ta tafi tana sababi ta tunkari gidan sarkin.

Asabe juyowar da xatayi taga mijinta da gari yayai zafi a hannunsa ya tsya jikin bushiyar yana kallonta cike da mamaki magana tafara yi cikin kin kina ah.. mai.. maigi... maigid... daaaa yaushe ka shigo  a fusace yabata amsa yana shiga dakinsa sanda kika saka yar mutane a hammatar ki kuma biyoni to tace tana shiga tare da gudun abun da zataje ta tarar fada yafara yi mata waike wacce irin mahaukaciya ce ne eye dan me xaki fada da yar mai gari vakibda hankali ne kinsan halin babanta sarai sai yasa a zaneki ni nagaji da jarabar ki kije gidanku sai nazo guda ta rangada A hayye wai shine xai ce natafi gudan mu gidan naka wata tsiya ake diba to natfi  din saike tafita tana banko kyaurn dakin nasa yariya kenan zaki gane kurenki yafada yana kwalawa amaryar sa kira. Nasreen kuwa ba ita ta tsaya ba sai da taje kan layin gidansu ta tsaya tana haku tareda cigaba da allah ya Isan ta uwani ce ta karaso taake mata sannu nasreen wanu mugun kallo ta watsa mata tare dacewa kina gani Za'a a kasheni amma ko ki kwaceni ko to wlh ni dakene maza kiyi hanyarki nayi tawa taja tsakii ta wuce tabar uwani dake mamamkin halin  kawartata.
Gidansu ta nufa tana jan kafa a hankali sakamakon gajiya da tayi bayan ta shiga gidan  ta nufi dakin na maman nata tana mai cewa mama gani mun dawo uwani ta wuce gida 'yanxu fisabililahi sai yanxu xaki dawo daga rakiyar kitso allah ya shirya tafada tana kallon nasreen din.
Bayan kawana biyu kenan matan gidan su nasreen ne xaune anata hira kowa yana tofa albarka cin bakinsa baba ne yayi sallama ya shigo gdan kansa da rawani irin na dagatan kauye  amsa wa sukai gaba daya yaran kuma suna oyoyo baba sannu da zuwa baba yauwa sannunku da gida yaran baba yafada yana shiga dakinsa ina nasreen ne ya tambaya da karfi akace masa bata dawo daga makaranta ba ana magana sai gata kije baba na kiranki to tace tare da ajje alonta a rumfar tsakar gidan ta nufi dakin baban shiga tayi da sallama ta tarar da shi yan cin abinci guri ta samu ta xauna tana jira yagama cin abincin
Kallon ta yayi yace yar baba wani abu ne ke faruwa a masarautar kano yanzu yafada yna kallon yanayin nasreen data zuba me ido hankalinta na kanshii yacigaba da cewa dama ba wani abu bane face anbada sanarwar cewa za debi sababbin Hadimai ne a gidan wanda aka bawa ko wanne dagaci ya kawo yarinya guda daya nan da sati Uku ko wanne dagaci zai kai yarinyar gidan hakimin da yake cikin gari ni yanzu haka bansan wa zan kai ba sai da ta nisa tace baba ka duba a cikin mu kawai duk wanda hankalinka ya fi kwantawa sai a kaita kawai hakane kuma maganarki Nasreen nasara dan kinga in nace akawo a garin nan kinga ban musi adalci na tun da ina da yara mata Tace gskyne baba Bara naje ana kiran sallar magariba shima cemata yayi nima bara naje sallar nakeson yi taba min buta ta akwai ruwa eh tace sanda ta taba butar tare da fita daga dakin shima butar ya dauka ya fita dan ya zaga bandaki ya fito ya yayi alwala yatafi massalaci bayan ya dawo babar Nasreen ta shigo ta samesa a dakinsa ta xauna a gefensa tare dacewa malam barka da hutawa Yace mata amrya muna lafiya yafada yana mata murmushi dan duk matansa yafi sonta lafiya lau malam dama magana ce nazo zamuyi akan nasreen natsuwa yayi yana sauraranta Ta cigaba dacewa dama manemin nasreen ne yaron nan yana so a bashi izini ya turo take gayamin shine nace bara in dai kadawo nazo nagayama baba cikin murmushi yace masha Allah wannan abu yayi in dai nafita zanda ayi min bincike akan yaron sannan na sanar dake sai ki gayamata abunda na yanke dan akwai wani abu ne da yataso a gari bana son yin gaggawa ne yanzu. To tace masa mu huta lafiya, Bayan kwana hudu malam ne zaune bayan ya tara iyalensa a dakinsa yafara dacewa duk abunda Allah ya kaddarawa bawa babu yanda zai yi domin yauwa saura sha shida za a zo za a tafi da yrinyar da nazaba domin kaita masarautar kano a sata cikin hadiman fadar dakin ne yayi tsit kowacce mata tana sakwa a ranta bata fata akai yar ta wannan Bautar suma yaran haka ne a ransu Baba ya nisa yace bana son kuma jin wata magana ko kuma a ja da hukuncin dazan yanke kowq da yanda Allah yake tsarmasa rayuwarsa INA NASREEN baba ya ambata......

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Jul 30, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

🦚👑🧝‍♀️UWAR SARKI🦚👑🧝‍♀️Where stories live. Discover now