Part 3

104 6 0
                                    

👑🧝‍♀️🦚UWAR SARKI👑🧝‍♀️🦚
Part (3)


ABUNDA MUKA FADA NA DAI DAI ALLAH YA BIYA MANA BUKATA WANDA MUKA FADA NA AKASINSA KUMA ALLAH YA YAFEMNA.

BAN YARDA WANI KO WATA YA JUYAMIN  LITTAFI ZUWA WATA SIGA TA DABAN BA BATARE DA IZINI NA BA NA MAI LITTAFIN.

Written ✍️ by team Cyyy

👑🧝‍♀️🦚UWAR SARKI👑🧝‍♀️🦚 Part (3)

Take cewa yau ace a gidan nan an rasa martaba kima da daraja (etiquettes and decorum) da za azo ace ana tayada jita jita a gidan a nan uban horo kana ina GiWa tafadi haka tana kallon mazauninsa "Allah ya baki yawan rai gani nan kusa" yabata amsa yana fitowa gabanta wani zabgegen kato ne rike da bulalar dukan jakaiii mirtukekiya fuskar nan tasa a daure babau alamun rahama sannan ta kalli barin kwarkwarorin tace "ina kwarkwara Asiya fito nan" tashi kwarkwara hasiya tafiti duk tabi ta firgice uban horo ayi mata bulala hamsin yanzun nan take kuwa aka kawo bencin da ake kwantar da msu laifi a xane su ta hau ta kwanta aka fara zuba mata bulala duk daya sai tayi ihu tana lissafawa shikuwa sai ya dage sannan yake zabga mata bulalalr amma kaf cikin Falon nam babu wanda ya isa ya tanka kowa ma sai shan jinin jikinsa da yake yi sakamakon haka dokar take mai laifi a cikin gida GIWA CE mai hukunci sai dai in sarki ya gada ma ya kwace ka .
"Hamsin" haka naji uban horo ya fada bayan ya sauke bulala ta karshe ya koma gurin dayke tsayuwa ya cigaba da tsayuwa itakuwa kwarkwara Hasiya hadimanta su biyu suk kamata suka tafi da ita turarkar ta tana kudita a zuciyar ta cewa sai ta dauki fansar Abunda aki mata wannan to xarcin sukuma ragowr matan Tace musu nan muka kawo karshen zamna yau sannnan tace jakadiyar Abunci kwana biyu ana kawomin korafim cew kina yi wa bayin gidan dan Zubi a kwanon abincin su dan hak kema ki je  kiyi ta jan guiwar ki a kasa tundaga turakata Har mdafar gidan nan sannan ta mike tana mai tafiya cikin isa

Sukuma Ragowar Matan suka hada baki guri daya tare da cewa "Allah yaja kwannan Giwar sarki"
"Allah ya huci zuciyar giwar sarki" dga nan kowa ya watse yakama gabansa.

Nasreen bayan ta tashi daga baccin da take buta ta dauka domin zuwa bayi dganan in ta dawo ta daura alwala tai sallalr la'asar in yaso sai ta tafi gidan uwani wata kawartace ta yarinta tare suka tashi bayna tafiti tayi sallah taci damara kamar zata dambe tafito ta jawo kyuren dakinsu ta wuce su kuma yangidan nasu suna ta hada hada tazo fita kennan daga gidan suka hadu da babban yayansu wanda basa shiri ko kadan yace mata ke dan uwarki ina zaki ' ciki ciki ta bashi amsa gidan su uwani  ba magana nake miki ba yakawo mata wani mugun naushi tayi waje da gudu tace Allah ya isa ban yafe ba shikuma yayi kwafa yana zakici ubanki ne zamu hadu dake wlh yarinyar nan. Gidansu uwani ta karsa ta tarar da ita tana ta kwalliya bayan ta gaida babar uwani wacce take tambayar ta ya mutanen gidan nasu take bata amsa da abunda aka tashi dashi agidan na rashin lafiyar inna sahura, ke uwani wannan kwalliya haka ina zaki ne Dariya tai tace wlh babu inda zani kawai sha'awar kwalliyar nake amma kinga ke dakike da kyau ai bakiyi kltabata amsa sanda take rufe jan bakinta 24hrs tana dan murmushi Nasreen tace ni ba wannan ne ya kawoni ba kinajina wai Sani ne ya takura min yana so ya turo gidan mu cewa zai aureni tafada tana kallonta uwani tayi guda tace Ahayye huuuuuu ashe abun yazo yo ai gara yazi ayi abunda za ayi muyi bikinki dan wlh kinga gara kiyi auren ki ki huta da wannan jarababnen gidan na ku amma kingayawa inna amarya da babe ne take kallon nasreen da alamar tambaya ta bata amsa da A'a amma indai sun dawo daga asibitinxan tare su da maganar ko ya kikace aminyar tabata hannu suka tafa takuma cewa ke tashi mubi ta yar yara(karamar kasuwa kennan) nayi kwalli da masoyina ko ya kika ce inji nasreen sanda take tashi itama uwani binta tai tace mutafi tabita a baya  bayan sun fita ne take cewa innar su uwani mun tafi sai mun dawo to ta bsu amsa sabida tana turen dabobbi saboda tana kiciniya da wata akuyar gidan.

Aikuwa suna fita saukayi yar yara sunayi suna hira daga nesa wani Abokin Sani yace masa da karfi saboda shi sanin yana cikin dan shagonsa na kayan masarufi saboda duk garin shagon sani yafi girma shi yasa yan matan gain suke sonsa Amma baya sonsu shi sai ya nace akan cewa sai Nasreen
Yace masa kai sani "nayi maka kwalli maza fito kagani"  kafin ya karasa a zancen sa sai ga sani yafito yana wani gyara riga sukuma sun riga sun karaso tana wani fari da ido sani ya budi baki yace "gimbiyar mata ina zuwa haka" ta bashi amsa da cewa "mun dan fito zaga gari ne shine muka buyo ta nan" ta bashi amsa tana kallonsa  yayi kyau yafada yana cewa yau zanzo da dddare fa in Allah ya kaimu' tace tom sai kazo.
Uwani tace to tantabara Uwar soyayya ni ba aganni ba kenn bare mugaisa yace lah kiyi hakuri kawar mu ban kula dake ba kinsan in ina gaban mutuniyar mantawa nake da kowa Amma kiyi hakuri yakike ya kwana biyu tace wlh lafiya lau.
Nasreen taja hannun uwanni tace kinga mutafi mangariba na kawo kai fa kinga kada mu bata lokaci a waje kar ayi mana fada' uwani tace hakane fa sanda take biye da ita sani cikin daga murya yace kijirani kinji mutuniyar. Murmushi tayi tana mai kara sauri dan ta isa gida a hanyar maraba suka rabu kowa yayi nasu gidan. Aikuwa hakan ta kasance bayan sallar magariba saninya tura aka kira masa ita sai da tagama ja masa aji sannnan ta fito tana wani yauki da Ran gwada abun saikace wata babar mace bayan sun kuma gaisawa daga nan aka shiga labarin duniya ana yi ana dariya kai daga gani kasan masoyan nan suna cikin farinciki a karshe bayan isha'i sosai sukai sallama yana kara tuna mata maganar turowa Azo ayi magana ta manya tace masa kar ka samu damuwq da baba ya dawo zn gaya masa kaji masoyina tafada tana shiga gida da gudun ta.

A MASARAUTAR KANO;
BANGAREN FULANI AGADEZ; fulani agadez ce zaune bayan sun dawo daga falon GIWA tana kallon television amma hankalinta ba  a nan yake ba kamar wacce aka tsikara tace jakadiya maza jeki taso mun Yareema Azeez a barinsa tun dazu nake ai kamasa yazo amma bai tashi ba 'To uwar gijiyata jakadiyar ta amsa tana mai tashi domin isar da sakon Fulani Agadez din wasu bangarori ta dinga shigewa na gidan wandanda suka fita mika mukami tana rissinawa ta gaishe su wadanda tafi mukami kuma suna dukawa su gaidata a haka har ta karasa bangaren yareema Azeez din wannda kai sai ka rantse da Allah a turai kake tsbar haduwar sa yaji fulawowi da shuke shuke ga wani swimming pool can dga gefe sai inda yake parking motocinsa su porsche da jaguar da dai sauran su a haka  ta kara sa cikin part din nasa tana ta adduar Allah yasa ya tashi dan kar tasha Wahalar ta dashi daga bacci saboda gabadayansa an shagwaba shi sai kace mace tayi dan tski tana tura kofar fallon wanda fadar haduwar sa ma bata lokacine ta karasa kofar bedroom dintana knocking hade da sallama shiru shiru dai har wajen minti 20 cikin isa da kasaita yace "who is that knocking my door" jiki nabari tabashi amsa Allah ya temakaka tuba nake  jakadiyar fulani Agadez ce "Fulani ce ke son ganinka a falonta" tan fadar haka tajuya a guje gudin kar ya iske ta nan. Dan tsaki yayi sannan ya mike ya shiga toilet. Yana kallon madubi zokuga wanda nagani wani hadadden guy ne wanda yaji kyau iya kyau idanuwan nan sa golden eyes ne kuma sleepy gashi fuskar nan babu saje sosai sai kadan kadan kuma gashin nan nasa ya kwanta luff kamar na larabwa kai ni rasa ganewa ma nai wannan kamar mace danga lips dinsa suna glowing ( kyalli )  a chest dinsa kuwa wani faffdan kirji ne wanda daga gani kasan yaji Gym gashi ba dogo na ba gajere ba kuma Fari ne tass kai duk indai mai kyau yake ya wuce nan. Bath tub ya shiga yayi wanka yafito ya shirya a gaggauce dan yau yana so yafita yawo kaya marasa nauyi yasaka wata blue din jauhace wacce taji aiki ya shafa turarensa mai dan banzan kamshi yafito yana tafiyar kasaita a hankali kamar bazai taka kasa ba duk inda ya wuce kuyangi da hadiman gidan zubewa suke suna gaida shi yan mata kuwa harda dalalar da yawu da sabida shagla wajen kallonsa  wasu har gudu suke dan suzo zuga wucewarsa a haka ma na hango jakadiyar Giwar sarki tana wani mammatse kafafu tana kallonsa ba ko kiftawa idanuwan nan sunyi jaa kai daga gani kasan na jaraba ne saboda ita kallon sa taya mata da sha'awa yake shiyasa take neman dama akansa (kuji tsohuwar nan an tsufa amma ana iskanci) a hakaya karasa turarakar Fulani agadez bayan kuyanginta sun gaidashi da hadimanta kowa ya fita ya basu fallon ta juya ta kalleshi cikin murya mai nuna tausasawa "Yarona".

🦚👑🧝‍♀️UWAR SARKI🦚👑🧝‍♀️Where stories live. Discover now