KOWA YA RAINA TSAYUWAR WATA...(Labarin gasar Matasa 2021

133 4 0
                                    

GASAR MATASAN MARUBUTA (2021)

RUKUNI NA TAKWAS (8)

JIGO: LABARI  AKAN YAWAITAR ZINACE ZINACEN DA SUKA YAWAITA A TSAKANIN MATA DA MAZAN AURE A WANNAN ZAMANIN

KOWA YA RAINA TSAYUWAR WATA...
  (Gajeran Labari)

SHAFI NA ƊAYA (1)

  Zaune take a gaban mudubi, tafi minti talatin tana tsara kwalliya. Kanta ta ɗaga ta dubi agogon bangon da ke maƙale a saman ɗakin, bakwai da rabi na dare (7:30pm) ya nuna, da sauri ta nufi durowar kayanta ta zaɓo wasu riga da wando masu kyau ta saka.

Gaban mudubi ta tsaya tana ƙarewa kanta kallo, ita da kanta tasan tayi kyau matuƙa. Cikinta ta kalla a take ƙwalla ta cika mata ido, sai da ta mayar da ita sannan ta buɗe durowarta ta zaro yadin ɗaure ciki fari ta  ɗaurashi a cikinta,  ta maƙala duk ƙarafan ta sanya dogon hijabi ta tayar da Sallar Isha'i

   Kafin ta idar ta gama jigata, don ba ƙaramin ɗauri ta yiwa cikinta ba, numfashinta da ƙyar yake fita. Kamar ta cire yadin, sai kuma ta haƙura ta barshi, tana tafiya tana ƙobarewa saboda wahala.
  
  Da sauri ta fita falon jin shigowar Yusuf, Jakar hannunshi ta karɓa ta kai masa ɗakinshi ta fito. Kitchen ta shiga ta haɗo masa Abincinsa da duk abinda zai buƙata ta ajje masa a teburin da ke tsakiyar falon, sannan ta koma ta zauna ta fara kallo duk da rabin hankalinta na gurin Yusuf.

  Tun da ya fito ya ke bin ta da kallo, "Masha Allah"  ya furta a fili don tayi masa kyau sosai, sai sheƙi take kamar wata daren goma sha huɗu.  Kama ta yi masa da Ladiyos sai dai Ladiyos siririya ce. Hannu ya sa ya shafi gefen fuskarta, murmushi ta yi ta matsa ta zuba masa abincinshi.

  Satar kallonta ya ke yi, don ta canja masa a komai, yana kammalawa ta kawar da kayan sannan ta dawo ta zauna a gefenshi.

  Hannu ya sa ya miƙar da ita tsaye, ƙare mata kallo ya fara yi tun daga sama har ƙasa. Hannunsa ya ɗora a kan cikinta yace "Dare ɗaya Allah kanyi Bature, wace dabara ki ka yi uwar teɓar nan taki ta ɓace?"
Bata ba shi amsa ba ta sunkuyar da kanta ƙasa hawaye na ɗiga.

Ƙyalƙyalewa ya yi da dariya yace "Wai ɗaure cikin ki ka yi? To ai kin bar kari tun ran tubani, wannan uban cikin naki ba na jin zai koma, sai dai na cigaba da maleji a haka. Ko da yake suma maɗauran cikin zasu yi amfani, kinga idan za mu je wani taron ko party idan ki ka ɗaure sai mu yi tafiyarmu babu mai ganewa. Matsalar ɗaya wannan ƙibar da ki ka narka ko da yake..."

Kukan da ta sanya ne yasa ya harɗe hannayenshi a ƙirji yana kallonta, rigarta ta ɗaga ta cire abinda ta ɗaure cikinta da shi ta jefar a ƙasa, sannan ta goge hawayenta.

Cikin bushewar zuciya tace "Yaya Yusuf na gaji da wulaƙanci da cin mutuncin da ka ke yi mini, mene ne laifina don nayi ƙiba? Idan da mai laifi kai ne tunda kai ne ka mori ƙuruciyata, kai ka yi min ciki har sau uku kuma na haifa maka Ƴaƴan. Yaya Yusuf matuƙar na biyewa munanan kalaman kushe halittar da ka ke yi mini, to tabbas ina dab da halaka kaina."

Hawayen da ya zubo mata ta ƙara sharewa sannan ta ɗora "A kullum bani da aiki sai guje-guje da tsalle-tsalle, da yawon bin likitoci don na rage ƙiba. Daidai da abinci bana ci ina ƙoshi ga shayarwa, duk ba za ka tausaya min ba? To na ji ka je kayi duk abinda za ka yi, wallahi summa tallahi daga yau bazan ƙara yin wani abu da zai rage mini ƙiba ba. Idan  na yi, to sai dai don kaina da lafiyata ba don kai ba. A ƙarshe ina ƙara maimaita maka, kowa ya raina tsayuwar wata ya hau sama ya gyara. Idan har ka isa ka mayar da ni ƴar siririya, kamar yanda Iyayenmu suka kawo maka ni gidanka, tunda kai ka ke halitta." Ta nufi ɗakinta da gudu, fashewa tayi da kuka, nadama da danasanin auren Yaya Yusuf na taso mata a zuciya. Tsakiyar Ƴaƴanta ta kwanta har bacci ya ɗauke ta.

    Jikinsa ne ya yi sanyi, ya nemi wuri ya zauna, tausayin Khadija na ratsa masa zuciya, a karon farko ya kaita maƙura, don tun tana ƙarama har ta girma ya aureta bata taɓa ɗaga masa harshe kamar yau ba. Ko da ya yi mata ba'a a kan jikinta, amsa ɗaya take ba shi tace "Kowa ya raina tsayuwar wata ya hau sama ya gyara." 

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 01, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

KOWA YA RAINA TSAYUWAR WATA...Where stories live. Discover now