Chapter two 🌹🌷

20 4 0
                                    

*BANSAN INDA SUKE BA*
         _a halin yanzun_

       *NA*
*Jameelah Jameey*

*Yar'mutan kankia ce❣️*

*MANAZARTA*
*WRITERS ASSOC*

*Marubuciyar👇*
*Nana Jawaheer*
*Gimbiya Hakima*
*Izzah ko mulki*
*Sanadin link*
*A gidan haya*
*Ɓarawo ne*
*Sadaukin  burhaan*
*Sanadin soyayyar shan minti*
*Bayi ma ƴa'ƴane book 1&2*
          _AND KNOW_
*BANSAN INDA SUKE BA*
_a halin yanzu_

*BISSIMILAHIR RAHMANIR RAHIM*

*Chapter Two🌹*

*precious🌹*

Gidan Ubana? Ke har kin isa daga zuwanki ki nemi ki zaganman uba? Ke kin san ni wacece a class din nan."?

Kallonta nayi na watsar sannan nace.....

*Continues🌹*

"Yo niko nasan ke wacece, ke mutunce kamar kowa daga nan sai kuma mai? Kuma naje na zagi ubanki in kinji haushi sai ki rama tunda naga dai kina da baki." Na ida maganar ina murguɗe mata baki....Nan fa dambe ya kacemai tsakanina da wannan yarinya wanda ni har yanzun bansan sunan ta ba balle na gaya maka a lokacin, sai dai daga gani yarinyar itama tana da fadi sosai, muna cikin dambacewa sai ga prefect  nan ta shigo nan tasa mu rage tsawonmu, amman ni sai nace... "Ni ba zan rage tsawo na ba, Allah ya bani tsawo sai wani yace na rage wani tsawo wallahi ban rage......kafin na kulle baki na naji ta wanke ni da mari tana cewa...."Ke dan ubanki ni zaki kalla kice baki rage tsawo to bari na cire maki wanann haukan da kika zo dashi daga gida."

Dafe kumatuna nayi ina tunanin mai zan yi ma wannan matar da ta mareni ina cikin haka naji ana cewa....."Kam bala'in nan kika mareta."? Basma ce ta tambaya  cikin fushi duk da ita Basma ba cika magana tayi ba, cewa prefect din tayi."....Eh na mareta dan ubanki ko da abunda zakiyi kema ƙaramar marar kunya.... nan kafin wannan prefect din  ta farga Basma ta wanka mata mari lafiyaiye, nima na kara aza mata da wani marin nan muka taso mata mu duka biyun.. Aiko ranar mun  sha na jakki, dan mugun bugu tayi mana sai da ta gama bugunmu, sannan ta hada mu mun duka ukun  ta tambayemu sunayensu..
"Ya sunan ku? Kuma uban mai ya hada ku fada? Tace cikin tsare fuska....."Ni Suna na Asma'u Bishir.. Sae ni nace
"Ni Hassan Muhammad..sanan Basma tace... "Ni kuma Ussaina Muhammad...."cigaba da cewa prefect din tayi....."To ubanmai ya hadaku fada? Asma'u tace...."Yaya Hafsat kawai daga na tafi nayo fitsari na tadda sun zauna man sit wai banda ikon tambayarsu dalili."kallonta wanda aka kira da Hafsat tayi sannan tace....."Ke dawa keda sit din."? Cewa Asma'u tayi...."Bakowa ni daya ce ke dashi." cikin mamaki Hafsat tace ma Asma'u...."To su sauran yan class din  baki zama da kowa."? Cikin garaji da tambayar da Hafsat ke ma Asma'u, Asma'u tace..."Ai nice farkon zuwa ajin ni na kamashi sit din."girgiza kae Hafsat tayi dan ta lura idan ta bar class din ba tare da sasantamu ba, ba ƙaramar rigima za'ayi ba dan mu dukanmu ba daga baya ba shiyasa tace ma Asma'u....."To ga kawaye nan nayi maki daga yau sun zama sit mate dinki kinji ni ko."?  Ba dan Asma'u taso ba tace...."Eh naji." maido kallonta Hafsat tayi wajenmu sannan tace...."to ku kuma su Hassana ga kawa nan nayi maku karku sake kuce zakuyi fada da ita ku hada kanku ku zama yan'uwa kunji."... Ɗaga mata kai kawae mukayi dan har yanzun bamu huce akan abunda tayi mana ba, cigaba da cewa tayi...." kuna da Yaya ne."? cewa mukayi...."Aa bamu da Yaya." cewa tayi."ok shikenan wani hostel aka baku."?...."Red house."...."ok indan an tashi daga class ke Asma'u ki taya su kwasar kayan ku kaiman su corner ta kinji."?
"Eh naji." Asma'u tace  cigaba da cewa Hafsat tayi."dan haka daga yau kin zama friend din su dan ban san fada...."Kuma ku Hassana Kawai ake kiranku."? Cewa mukayi...."Aa Basma da Salma." murmushi Hafsat tayi sannan tace."wacece Basma? Cewa nayi..."Nice." cewa tayi...  "ai bake bace, ni gane ku nike, ce man zakuyi Hassana ce Basma ko Ussaina."sae a lokacin nayi dariya dan na saba ansar wannan tambayar cewa nayi. "Basma ce Hassana sai ni Ussaina." harar Basma ta wurga man sannan tace." lalalala Allah karya take nice Ussaina." nan gardama ta barke tsanina da Basma kowa na cewa  nice dai Ussaina..


Tashi Hafsat tayi tana cewa."Ku dai kuka sani kowa ce zan kira Basma ko Salma shikenan ai ko."? Ɗaga kai mukayi a tare sannan muka ce.."Eh." "yanzun ku tashi ankusa tashi dan haka ku taso kuzo a kwashi kayan ku..


Nan muka tafi muka kwashe kayan muka kai corner din Hafsat itace GAME prefect din lokacin..
Bayan mun  gama kai kayanmu corner din Hafsat baki daya sannan Mau ta tafiyar ta itama hostel din su dan ta shirya..Basma ta kallan sannan tace."Salma wai haka zamu zauna cikin wanann dan wajen."? Nima kallonta nayi dan ba haka nayi tsanmanin zanga boarding ba nace."Hmm nima haka nike tunani, ja fa wajen dan karami Basma.." cikin damuwa da rashin sabo da waje Basma tace. "Gaskiya nidai bani iya kwanciya a bisa wannan gadon karfan."

Ni kuwa cikin murna nace."Ni kuma wajen yayi mani kyau fa Basma." bugu ta kawo man sannan tace "ai da man ke Salma kina san wannan boarding din, kawai da kin barmu ai da yanzun muna gida abun mu."  Yaya Hafsat ta shigo tace."Basma." cikin rashin kuzari tace. "Naam Yaya Hafsat."... ku dauko towels dinku kuzo ku tafi wanka anjima za'ayi ringing din dinning in kuna so sai kuje ku ansa."

Cewa Basma tayi."Aa mudai mun koshi ko Salma."? Ɗaga man kai tayi sannan nace. "Eh mun koshi." cewa Yaya Hafsat tayi."to ku taso na raka ku
Bayan Hafsat ta kaimu Class, ta wuce class din da take Supervisor...

Nan muka zauna saman dask muna ta shurutu daga zuwanmu ba wanda ya kaini shurutu, Asma'u ce ke biye man itako Basma sai dai tayi dariya idan mukayi abun dariya ita da yan class   muna cikin wannan dan bazan surutu sai ga Supervisor din mu tazo..
"Ke zo nan." nan tayi pointing din na tace nazo.. Tashi nay nace...."Gani yaya." harara ta tayi sannan tace...."Surutun mai kuke yi mana cikin class."? Cewa nayi. "Bakomai."cewa tayi... "Kawai saboda iskanci shine kuke saki baki sai surutu kuke yi mana, yaushe aka kawoku dan ni bansan ku ba a cikin class din na."? Cewa nayi... "Yau."... Cewa tayi "OK  to daga yau Idan aka zo evening ba'a surutu karatu akeyi kunji."?
"Eh munji." cigaba da cewa tayi."ko kuna san ayi maku repeating."?  Dasauri mukace..."Aa wallahi bamu so ayi mana repeating Yaya.".... "to tunda baku san repeating ya zama dole ku bar surutu ku kama karatu dan nan makarantar in mutun baiyi karatu ba repeating ake yi mashi."..."To shikenan insha Allah."...ku tashi ko koma sit ku zauna,  amman ya sunanku."?
"Ni Salma ita kuma Basma."..."ok ku tashi kuje ku zauna, wai yan class din nan wacece class captain dinku."?  Nan suka ce..."Babu class captain." "ok shikenan yanzun kun kai nawa a class din."?
"Mu hamsin ne yanzun."..."ok ai kun cika ma dan haka ke Salma daga yau kece class captain kina jina."?..."Eh naji Yaya.".. "yan class kuna ji na? Na sa Salma ta zama class captain dinku, ke kuma Salma daga yau ke zaki dunga yi man Noise makers a class kinji."?..... "Eh naji." "sannan ai kin iya yanda ake roster ko."?.... "Eh na iya."..."to zaki yi roster daga Monday to Friday zaki rubuta yan shara banda ke da assistant dinki, sai ki zaba assistant da kanki..
"To na zabi Asma'u.".... "to shikenan ke Asma'u ke zaki ringa taimaka mata kinji."?
"Yaya Zainab naji." cewar Asma'u..... "to shikenan ku dauko litafin ku ku fara karatu, ku kuma su Basma ki samu aran note gun wanda ta'iya note sosai ku kwafa inda akayi baku nan.. "To yaya Zainab..
Nan muka  anshi note wajen Asma'u muna kwafa, ita kuma Asma'u tana karatu..
Preferd master sai round yake yana bugun Wanda suka fito waje , filin makarantar yayi shiru kamar ba kowa a wajen kowa sai karatu yake mune bamu tashi ba sai six pm sanann aka tashi, nan fa juniors suka kama jin tsoron bin hanyar hostel, suna tsoran karda a dauke su *HAYA*(mu a sandamu muna cema daukar ruwan seniors *HAYA* )

"Nidai su Basma kuzo mubi ta bayan yellow, wallahi muka bi ta normal hanya haya za'a dauke mu fa."Asma'u take ce mana haka cikin tsoro da yake ita ta kwana biyu tasan yanda ake rayuwar boarding, ce mata nayi.... "Dallah wallahi wanann Asma'un kin cika tsoran bala'i, ba wata hayar da za'a dauke mu, indan ma an dauke mu sai mu basu hakuri mu wucewarmu, Amman Kawai dan saboda haya sai mu shiga daji."
Ce man tayi "Ai ni ba tsoro bane Kawai ina guje mana wahala ne."....Ce mata nayi, "karki damu zo mu wucewarmu."
"To shikenan." haka dai Asma'u ta bimu ba dan taso ba, ita dai taso tabi ta daji tasamu ta shige warta hankalinta kwance...
Muna cikin tafiya muka ji an shako mana hijab mu duka ukun anyi gife guda damu, cema wanda ta ja  mana hijab nayi.....


*Muje zuwa..... 🖤*

*Yar'mutan kankia ce❣️*

Share
Comment
Pls

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: Aug 12, 2021 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

BANSAN INDA SUKE BA A HALIN YANZUNWhere stories live. Discover now