DAMUWATA. (Sanin abin adona)
By Mrsjmoon.E.W..F.
Page 18.
K'arar na'urar da ke nuna Deejah na da rai shi ne ya tashi su Mama barci a dai-dai lokacin kuma anata kiraye-kirayen sallar subahi. Dr. Jalal tare da Nurses ne suka shigo a hanzarce sakamakon jiyo k'aran na'urar. Fita su Mama sukayi suka tsaya bakin k'ofar cikin jan addu'o'i nasara.
Bayan wucewar wani lokaci Doctor ya fito da sauri Mama ta sha gabansa murmushi ya sauke mata ya nuna mata d'akin da hannu.
"Tafi ta ganki dan itama ke ta ke ta ambata."
"Da gaske Likita?"
"Eh Mama."
Cikin rawar jiki Mama ta fad'a d'akin ta yi ido biyu da Deejah jingine da gado Nurse na wanke mata baki.
Kulle ido na yi na bud'esu kan Mama wacce ke tsaye hawaye na bin kumatunta.
"Mamana kina raye dama ban saraki ba?"
"Alhamdulillah."
Shi ne abinda Mama ta furta a maimakon bani amsa.
"Gawa ta k'i rami ya jikin naki?"
"Hajiya Inna taho taji d'uminku."
Da sauri suka iso tare da rungumeni. Murna kam naganshi wurin Mama, ni kaina farin cikin da na samu kaina ciki na ganin Mama a raye ba mai misaltuwa ba ne.
"Ina Baba Umaru?"
Ta ambata saboda shi kawai na ke son sanyawa a ido.
"Yana Jigawa."
"Lafiya ko?"
Mamata ta ambata cikin sauri idanunta zube kan Hajiya Inna.
"Sai ya dawo muji saboda bayan na taho Habibu ke sanarmin sun tafi."
"Allah yasa dai lafiya wannan irin tafiya cikin dare."
"Amin."
"Mama muma mutafi dan Allah naga Dattijon kirki wanda bakya gajiya da bani labarin karamcinsa gareki."
"Uwata insha Allah kina warkewa zan shirya mana tafiya."
"Da fatan har Sokoto zakuje?"
"A'a Inna kowanne tafiyarsa daban zan shirya masa da yarda Allah."
"Allah ya amince."
"Amin."
"Mama ki saka mana ranar zuwa dan Allah, ina son ga nina cikin dangi masu yawa, naje can gidan naje can."
"Kin ganki Takwara da salo tamkar abin da kike ambata zaki iya aikatawa, ke da kike kifin rijiya sam ba kya son jama'a."
"Allah Hajiya Inna ina son ganina cikin dangi irin masu yawan nan."
"Uwata bari in had'o miki tea ki Sha."
Mama ta kauda maganar.
"To amma wanda na ke son yi jikina duk ciwo keyimin."
"Ai kam dole ki jiki ba dai-dai ba, kwanaki biyu a kwance ba motsi dole gab'b'ai su amsa."
"Hajiya Inna wai dogon suma na yi ko me?"
"Eh fa, irin wanda ke kama, coma inji turawa."
Shiru na yi ina tuno kalaman da suka shigo kunnuwana lokacin.
"Uwata sannu kinji? Allah kada ya k'ara nuna mana irin wannan lamari."
"Amin Mamana."
"Hajiya Likita ya ce abata abu mai d'umi sai ta sha magani kada abarta ta yi tafiya ita d'aya saboda jikinta ba kwari."