*TSAKA MAI WUYA*
Safiyyah galadanchi
4
A dakin uwani suka zauna suna tunanin maganar da suka gama tattaunawa akai tareda rashin mafita, uwani ce tayi kokarin kawo shawara tana cewa, kin manta da yarinyar nan wata Halima da tasamo ciki daga irin wannan kuskuren kodai kema hakan ta faru dake ne? Kinga tashi zakiyi tunda kinsha panadol kije asibitin ki sameshi ki fadamai halin da ake ciki dan gaskiya wannan ba karamar matsala bace.
Fadimatu ta gyara zaman ta tace, yar amana kardai bakin su inna ne ya kamani, ina murna na tsallake wannan siradin saiga wani bala'i yana neman kifewa dani, ya zanyi da rayuwata idan cikin ne ajikina? Hawaye ya zubo tasa bayan hannunta ta share taci gaba da cewa, nasan mama bazata barki ki fita ba bari ni nayi sauri naje duk da banda tabbacin zan iya zuwa da kafa amma dai gara koma menene ya sani.
Uwani ta kalleta cike da tausayi kamar itama zatayi kukan tace, to bazaki sha ko kunun bane? Girgiza kai uwani tayi tace, inasha amai zanyi ki ajiyemin harna dawo.
Bata jira uwani ta amsa mata ba ta fita tana tafiya kamar batada karfi har ta isa asibitin sai ta samu duk asibitin a yamutse ana gyara ta leka hanyar office din taganshi a bude anata fito da kayan dake ciki karasawa tayi yana shirin fitowa ta matsa daga gefe, har zai wuce se muka ya dawo ya zuba mata ido, baiyi magana ba ya shiga office din sai tabi bayanshi, takalminta ya nuna mata yace, ga sunan ban cinye su ba dauka kifitar min daga office malama.
Runtse idonta tayi sosai tana tsananin jin kunyar abinda zata fada, mekayimin ranar nan likita? Laulayi nake, don Allah ciki kayimin? Ka fadamin gaskiya.
Dariyar takaici yayi ya shafa gemunsa dan baima san ta inda zai fara ba sannan yace, mema kikace sunanki ranar? Koma yayane kafin raina ya baci kifitar min daga office.
Kuka ta fashe dashi tana cewa, in tafi ina? Laulayi fa nace maka, don Allah ka dubani ko cikin ne da gaske.
Daga danyin wannan abu zaki fara tunanin ciki, idan shine ma kije ki nemi wanda yamiki nidai bani ba, fitowa yayi daga office din ta biyo bayanshi bayan ta dauko takalminta tana yi masa magana ya juyo a hasale, malama karki taramin mutane kinjini ko?.
Tsaye tayi tana kallonsa har ya shiga hadaddiyar motarshi ya wuce, a galabaice ta isa gidansu uwani, ta labarta mata yadda sukayi babu wanda ya sake cewa komai har ta baro gidan ta dawo gida ta kwanta a dakinsu.
Washe gari da safe ta shiga dakin inna ta gaisheta, a wulakance ta amsa mata tareda fadin, akwai abinda kikeso ko dan daga ganin makirar fuskar nan taki ba gaisheni tazo yi ba, bata damu da kalaman innar ba se tace, don Allah so nake ku aramin wayarku nakira wannan mutumin na tasha idan yaje Tangaza ya fadawa mama banda lafiya ta aikomin da kudi insiya magani.
Inna ta mike tsaye tana gyara daurin zaninta tace, kije ki siyo kati na dari ayi masa pilashin inya kira sekuyi magana, cike da mamaki fadimatu tace, inna katin dari kuma flashing kawai ba kira zaki ba muyi magana? Nidai to kiyimin alfarma kibani numbernshi inje in ari wata wayar.
Fita tayi ta kama sabgogin gabanta ta kyale fadimatu zaune a wurin, lallabawa tayi ta koma daki saboda kanta da jikinta dake mata ciwo sosai, sauran kunun da uwani ta bata tazo dashi ta dauko tasha ta sake kwantawa tana nazarin abinda iyayenta ke nufi da ita ta dai san nan dangin uwarta ne ama babu mutum guda da take karkashinsa, shin rikonta ake ko zaman kanta takeyi? Duk rashin hakurine ya janyo haka tana son sanin dalilin dayasa bata san babanta bama, tana wannan tunanin amai ya taso ta ta fito waje tana kwararashi inna na gefe tana kwaba gumbar kunu acikin kwarya, tayi saurin daga gumbar ta ajiyeta bayanta ta nufi inda fadimatu take ta riko rigarta tana cewa, ohh ni yau naga ikon Allah, menene haka zaku cika mana gida da shegu yan gaba da fatiha? Ciki kika yo? Ba mamaki naga kirji kamar ya faso riga , malam! Zo ka gani ga abinda dai ake cewa bazata iyaba yau tayi. Da sauri ya fito yana daure wandonsa yana tambayar menene, inna tace, ciki gareta wallahi duba dakyau ka gani, kalli nonuwanta yadda suka wani kara girma ga haske datayi sata agaba kaji watansa nawa musan abinyi karsu cika mana gida da shaggun diya.
Kallon fadimatu yayi yace ke wannan cikin watansa nawa? Fadimatu tace, baba bafa ciki bane nidai bansan inada ciki ba wallahi nida bana kula maza ma baba kaima ai shaida ne. Matsawa baya yayi yace shaidar wa? Badai ke ba ko? Nan likita yace mana maza kala goma sunyi amfani dake akan me zan yadda dake, kalli kiga abinda fa'iza tayi ai ke sekinyi ubansa, wallahi ko ki fadamin cikin nan na waye kuma watansa nawa ko ki bar gidan nan, shuru tayi kanta akasa gabanta na masifar faduwa, yanata maimaita tambayar hankalinta baya ma kanshi sai saukar bugu taji ta ko ina har seda taso yin gudu yashiga daki ya dauko mata hijab da takalmi ya jefa mata, maza-maza awa biyu na baki ki nemo uban cikin nan kizo, dole uwarki tazo garin nan wallahi mungaji da bakar wahala dake yar iska.
Jiki na rawa ta saka hijabin ta fita dan ta gama yadda cikine da ita, tana isa asibitin taga motarshi ta fito daga ciki tahau titi da sauri ta tare mashin tabi bayanshi basuyi wata tafiya mai nisa ba taga an bude masa gate a wani babban gida ya shiga mashin na tsayawa ta ruga ta gudu tabi bayanshi, waya yakeyi bayan yayi parking a wurin ajiye motoci sai ganinta yayi a tsaye, har ga Allah ya tsorata dan gudu ma yaso yi, sai kuma ya dake, ya yamutsa fuska yana kallonta sannan ya juya yana kallon mai gadi daya biyo bayanta yana zaginta ta baro mai mashin a waje bata sallameshi ba, kallonta yayi daga sama har kasa yace, ke fita daga gidan nan, ta durkusa har kasa ta kasa magana sai hawaye, dakyar ta zaro kalaman tana cewa, likita kasan abinda ya faru tsakanina dakai, ciwo naketa yi kalleni dakyau da uwata da ubana a raye amma ina cikin matsanancin talauci ko paracetamol banida mai siya min, ka dubi girman Allah ko baka karbi cikin nan ba ka zubarmin dashi, wallahi babu namijin daya taba rike koda hannuna ne inba kai ba.
Mai gadi ya kalleshi yace Hisham kodai mahaukaciya ce? Bari na sanarwa hajiya gaskiya tazo ta roketa ta fita.
Hisham bebi takansa ba ya juya ya kalleta yace, ke zaki fita ko kuwa sai kinci na jaki, ni menayi miki ranar, ai kin yadda kikayi ban kutsa cikin mutuncinki ba saboda kyankyamin wurin nake bakya askewa dan haka maza ki fita daga gidan nan kafin in hadaki da yan sanda.
Innalillahiwa'inna'ilaihiraji'un ta fara maimaitawa tana cewa don Allah kajikaina korata zasuyi daga gidan basu sona.
Tana daga tsugune tajiyo saukar bulala a bayanta daganan sai gani tayi ta mike tsaye saboda dukane bana wasa ba, yana daga zaune cikin mota yana kallon kannensa mata su biyu halisa da saima suna dukanta har ya rufe mota zai wuce ciki sai kuma ya dawo yana kiran sunayensu amma basa ma saurarensa sai zaginta suke suna duka saida ya daka musu tsawa tareda fadin, bakuda hankaline? What if cikin ne da ita dagaske fa? Ke! yafada yana kallon fadimatu, fita daga gidan nan.juyawa tayi har ta kusa kai gate sai ta juyo tace, likita kaine na farko daka shiga rayuwata ka lalatamin, idan har baka taimakeni ba bayan cin amanata da kayi na barka da Allah zai mana hisabi ranar kiyama dan nasan yanzu banida karfi ko ikon da zai bimin hakkina Allah ya isa tsakanina dakai.