*TSAKA MAI WUYA*
Safiyyah galadanchi
6
Ran Abba a matukar bace ya kalleshi tareda cewa "she's not your type kamar yaya? A wurin aure ba type dinka bace amma ka iya...? Karka batamin rai Hisham na gama magana" ya sake kallon fadimatu yace, "fatima waye ya fada miki kinada ciki" tana wasa da yatsun hannunta tana kallon kasa tace " bayan abinda ya faru a asibitinsa naje wajen kawata na fada mata abinda ya faru shine tace aikuwa iskanci ne dagaske kuma gashi ya fada da bakinsa, yanzu kuma dana fara rashin lafiya se tacemin cikine dani kar injira kowa inje wurin shi wannan Dr din na fada masa inada ciki kuma nashi ne"
hajiya da takeji kamar tasa muciya ta make fadimatu tace "to nidai wannan batun bada yawun bakina ba, kai a ganinka yarinyar da ta dace Hisham ya aura itace wadda zata biyoshi gida tana fada mana kai tsaye yayi mata ciki, bayan kuma anje an bincika babu ciki wane irin aure kuma za'a yi illa kowa ya kama gabanshi, don Allah abar maganar nan anan kar a daga da ita" tsaki Abba yayi saboda takaicin Hajiya yace "ya kina ganin gaskiya zaki rufe idonki hajiya Halima, shi yaron naki baki san halinsa bane? Ni confidence dinta ma ya burgeni tanada alamar gaskiya kai tsaye bayan haka kiji irin maganar da take fada bafa tasan komai ba shine yake kokarin bude mata ido, ni dakike ganina na riga na gama magana" ya dubi Hisham yace "dauketa ka maida ita gida ka gano gidansu" "fatima kiyi hakuri da abinda faru kaddara ce bata wuce kan kowa insha Allahu kuma shi zai aureki bazai zauna yana taka mutane yadda yakeso ana kyaleshi ba" fadimatu tayi kasa dakanta, harga Allah bata son Hisham bawai dan tana ganin yafi karfinta ba sai dan tana yi masa kallon dan iska, dakyar ta bude bakinta tayiwa Abba godiya. Bacin rai yasaka hajiya ta tashi ta fita daga palon, Hisham yabi bayanta shima rai a bace, Abba yayiwa fadimatu nuni da tabi bayanshi, fita tayi itama tana tunanin yadda zatayi dasu inna idan ta tafi gida, yanzu ma tasan dole zasuce daga wurin Shashanci ta fito, tsaki tayi wanda batasan ma ya fito ba hakan yasa Hisham juyowa ya kalleta ya sauke haushinta dake ransa sai yaga ta cigaba da tafiya tana magana a fili tana cewa "to duk abinda suka dauka hakan ne, mutanen da insuka ki gaskiya basa ma son ganinta wuni daya da nayi zasu iya cewa kwana nayi" juyawa yayi ya shiga dakin hajiya itako ta tsaya daga palon tana kallo a TV."Hajiya kinajin abinda Abba yake shirin yimin ko" shidinma haushinsa take ji dan haka tace "meyasa bazai maka haka ba? Menene yake damunka? Menene abin sha'awa ajikin wannan yarinyar? Kasani kake take sani Abbanku bazai sake yarda dakai ba kuma ni banason tashin hankali tunda kai ka janyo kaje ni babu ruwana" bata rai yayi yana hango tsananin matsalar da yake ciki amma sai ya juya ya fita yasan dole hajiya bazata rasa abinyi ba akan dai afasa wannan lamarin.
Fitowa yayi daga dakin ya kare mata kallo daga nesa ta kurawa TV ido tana motsa bakinta kamar tana karanta subtitle dinda ake rubutawa a star plus dasuke wani Indian series, seda yakai kofar fita sannan yace "ke!" Ta dago kai ta kalleshi batareda yayi magana ba ya fita, juyawa tayi taci gaba da kallonta tana hada bayanta da kujera, har yakai wurin mota bai ganta ba tsaki yayi ya dauki wayarsa ya kira saima tana dagawa yace "fito palon hajiya ki turomin yarinyar nan tareda magungunan ta dan Allah" amasawa tayi da to sanan ya kashe wayar yana tsaye ya ganta da wani uban sauri tana zuwa ta bude gaban motar ta shige, da mamaki ya kalleta harta rufe kofar shima ya shiga ya zauna, baiyi magana ba har suka daga gidan suka hau titi sannan yace "kibar ganin Abba ya daure miki gindi wai zaki aureni kiyi tunanin zan iya aurenki, idan kinason kanki da zaman lafiya to ki fada masa bazaki aureni ba" ta zaro ido tareda rike baki tana kallonshi sai kuma ta maida dubanta gefe tana cewa "hmmm..." ya sake cewa "ke kinsan nafi karfinki, ko mai goge takalmi na baki isa kikai wannan matsayin ba balle matar aurena, kinsan me ake nufi da aure? Aure yana nufin So? Bayan haka kuma cin amana ta kawai kika zo kika yi inba haka ba ya zaki ce nayi Zina dake bayan babu abinda nayi miki" fuskar ta takai jikin glass din window ta manna hancinta da goshinta da karfi kamar bata jishi ba, ya fitar da huci kadan yana cewa "malama wace unguwa za a kaiki"? Sai lokacin ta juyo da fuskarta tace "Tudun wada zaka kaini malam" seda suka kai yanata kallon unguwar yana yamutsa fuska yajiyota tana cewa "wannan kwanar zaka shiga ta masallaci" yajuya akalar motar ya shiga tafiya ba nisa ya hango ramuka ya tsaya yana cewa "sauka daganan bazan iya shiga wannan unguwar taku ba" gyara zamanta tayi tace "dama bazan fita ba seka kaini har kofar gida kayiwa su baba bayani haka kawai ka tafi ka barni su dake ni, dama gashi dukan da kannenka suka min ban warware shi ba ga sauran zazzabi a jikina, to badani ba wallahi" tsaki yayi aransa yace 'ga rashin tarbiya kuma, sam bata iya magana ba' lallabawa yayi har inda tace masa ya isa ta bude da sauri ta fita, wani irin mamaki ya kamashi ganin gidan data shiga.Da sallama ta shiga gidan inna na zaune rike da fitila a hannunta ta Dalla mata fitilar a fuska tana cewa "la'ilaha illallahu, yar iska se yanzu kika dawo? Da kwana kikayi niyyar yi can ya karasa abinda be karasa ba ko shi kwarton naki? Uwarki ta bar mana bala'i zo nan kiyimin bayani dan ubanki, ta dauki kwanon ruwa dake kusa da ita ta jefeta da shi kafin tabi bayanta da duka.
Shida yake zaune seda ya zabura da karfi kamar zai fita daga motar saboda tsorata da irin faduwar da fadimatu tayi yana kallo ta rike mata hijab tana zaginta batareda yayi kokarin fita ya taimaketa ba, shi a ganinsa zubar da mutuncinsa kawai wayan nan mahaukatan zasuyi tun haduwar farko da yayi dasu bai musu kallon mutane ba face dabbobi.
Tunda ya juya bai waiwayo ba har ya fita daga unguwar.Mikewa tsaye fadimatu tayi tana kuka saboda taji zafin faduwar da tayi tana cewa "haba inna kufa kuka ce inban kawo uban cikin da kuke cewa inada ba kar in dawo, yanzu kuma nazo baku saurareni ba kawai kun hauni da duka"
Inna dake neman abinda zata kwada mata tace "wane irin saurare? Ni mahaukaciya ce da zan saurareki? Hmm bari kishigo gidan ki sameni yau sekin yabawa aya zakinta" tana gama fadin haka ta daga labulen kofar ta shige gida, fadimatu tana goge hawayenta ta durkusa kasa tana tsince magungunanta da suka watse a kasa.
Gidan ta shiga jikinta duk a sanyaye tana niyyar shiga daki taga maman jamila a tsaye ta ajiye ledar gefen kofa ta juyo tana kallonta tace "don Allah maman jamila abinda inna takemin ta kyauta min? Sufa dazu suka korani ina cikin ciwo yanzu kuma na dawo sun hauni da duka, daga na motsa tacemin nayo cikin shege bayan banida komai ni bantaba yin iskanci ba" maman jamila ta rike haba tace "nidai babu abinda zance miki fadimatu saidai in baki hakuri, kinsan halin maman fa'iza yanzu zan saka bakina a lamarin nan kiga jidali ya dawo kaina, indai har cin amanarki take to ai Allah baya bacci baya gyangyadi yana kallonta zai saka miki" inna dake tsaye cikin duhu tana saurarensu ta dallo mata fitila a ido tace "ke ganeki zulai? Hawainiyarki ta kiyayi ramata, kinsan dama ina cike dake akan gumbata da akuyarki ta canye wallahi yanzu sai mu kwashi yan kallo dake" maman jamila ta tabe baki tace "kidai kwashi yan matsalolinki kiyi gaba dasu yarinya ce kin hakikance kina zaluntarta kice ba a magana daga yarki tayi cikin shege se akace dan kowa se yayi tun wuri ki kama kanki ni banda lokacin tsayawa hayaniya dake"
Inna ta maida dubanta ga fadimatu tace "ina shi uban shegen yake duk wunin da kikayi baki sako shi gaba ba"
Shuru fadimatu tayi bata kulata ba dan shiga dakin ma take so tayi ta kwanta inna ta sake tareda tana cewa "baki jini bane"? Juyowa tayi tace "da wanne zanji? Ciwon jikin da kika dawo min dashi ko kuma fadanki da zagi? Nazo da mutum kofar gida yaga kina duka na yayi tafiyarshi dan bai saba ganin haka ba" inna ta dafe kirji tana cewa "badai hassan ba? Dan shi nagani a tsaye lokacin" fadimatu ta tabe baki tace "farar mota dai da kika gani tayi gaba lokacin da kika yarfani kasa shine nasan tsorata yayi ya kara gaba" gaban inna ya fadi ta rike baki tana zagaya awakin dake daure wurin, cak kuma ta tsaya tareda rike kugu tace "ni nasan shegen kwadayinki bazai barki ki zauna waje daya ba ina kika samo mai wannan motar" saida ta daga labulen dakin tace "ke kika kaini wurinshi watan daya gabata" daga haka ta shige dakin inna ko gaba daya ta shiga rudani bata kula bakar maganar da fadimatu tayi mata ba dan ta saba Sam yarinyar bata wani ganin girman ta.