*TSAKA MAI WUYA*

Safiyyah galadanchi

3

Fadima wani labari nakeji a wurin innarki dazu ina shirin shiga masallaci sai gata tazo min da wannan zance, wai jiya kin haihu kuma kinki ki shayar da yaro.
Tunda ya soma magana take dibarsa tana watsarwa da idonta har ya kammala sannan ta saka idonta cikin nashi tace "Malam sani" ya sunkuyar dakai dan yasan halinta, taci gaba da cewa "ka yadda da abinda inna tace"? Kasa kallonta yayi sai ya girgiza kai ta sauke numfashi tace, Alhmdllh ni zan koma aji naga malam babba ya shiga, har ta soma tafiya yakira sunanta tareda cewa, fadimatu amma... saurin katse shi tayi, amma me? Don Allah Mubar maganar nan kasan halina ni bakina in raina yana a bace bashida saiti.
Shuru yayi yana kallon yanda hijabinta ke cika da iska yana sacewa saboda yanayin tafiyarta, girgiza kai yayi yana mamakin yadda akayi ma yake son yarinyar nan, gaba daya tafi karfinshi sannan ko kadan batada natsuwa ji yadda take tafiya kamar ba mace ba tana faman bude kafafuwa.
Zata shiga ajin takusa cin karo da malam babba tayi saurin matsawa gefe tana gaida shi, ya amsa yana cewa, yau inaga bazaki samu karatu ba kiyi hakuri ki shiga aji daya ki koyar dasu malaminsu tareda malamin aji biyu sun wakilci sauran malamai zuwa gaisuwar iyalin alhaji tanimu, amsawa tayi da to sannan ta nufi ajinsu, ko dama batazo da niyyar karatunba dan bata dauko jakar littattafanta ba, tana shiga yaran sai wasa suke da tsalle-tsalle suna ganinta duk suka nutsu dan ita ba ruwanta in yaro baya ji seta kaishi waje cikin rana ya kama kunne har sai yayi kuka.
Karfe shida saura minti goma suka tashi daga islamiya bata tsaya ba ta wuce gida tana sauraren yunwar da takeji gaba daya tashin hankali yasa ta manta dako karin safe batayi ba, tana shiga gidan inna tana zaune da daurin kirji ta daura dankwali ta turo shi gaba tabi bayan fadimatu da harara hartaga shigewarta daki, dakinta ta shiga ta dauko jaririn ta bita dakin dashi ta sameta tana sauya kayan jikinta ta fara cewa, shegen gantalin yawon dai bazaki bar shi ba, waya sani na jaririn nan ko malam sani ne ya dura miki ciki kika haifeshi waike bakida imani ne yaro ya kwana ya wuni ba nono uwarki kikeso yaci? Huci kadan fadimatu tayi sannan ta janyo hijabi daga jakar kayanta ta saka sannan ta samu wuri can gefe ta zauna tana kallon inna, inna ta sake cewa, daina kallona da wannan idon naki masu kaba guliya idanun mota zaki karbi yaro ki bashi abinci ko seya mutu kin janyo mana balai? Fadimatu tayi murmushi tace inna to ai kinga banci komai ba nima yau ina zai samu abinci bayan ni uwarsa ina tareda yunwa idan da fura koma menene kibani na danci sena karbe shi nabashi, inna ta rike haba kamar bazata bata ba sai kuma tace, baza a haifeki a gaba na kiyimin wayo ba, narantse da Allah kika ci abincin nan kika ki karbar shi sena lakada miki duka, kindai san halina ba karamin aikina bane inci ubanki wallahi, fadimatu ta girgiza kai tace, ai kinsan ni danace zanyi abu to ba fashi bana magana biyu.
Fita inna tayi daga dakin taje ta debo tuwon dawa tareda miyar kuka Green shar ta kawo mata, karba tayi ta zauna tana ci saida  duk ta kalmashe shi tasha ruwa, ta saka takalminta ta leko waje inna bata nan tayi wuf ta gudu, inna data shigo dakin tana washe baki sai gani tayi ba kowa ta rike haba tana tunanin kalar dukan da zatayiwa fadimatu.
Sai dare ta dawo tana tunanin karonta da inna amma sai tayi kamar ba ita ba harda bude babbar murya tayi sallama sannan ta karasa ciki a zaune ta samu inna a dakin tana faman tsattsage hakori ga fa'iza zaune a gefenta yaro sai uban kuka yake tsalawa,   mikewa inna tayi tareda riko hijabin fadimatu tana cewa, har abada bazaki sauya ba uwarki ta haifo bala'i ta tafi ta barmu dashi, ni zaki shukawa rashin mutunci dayake baki gadi mutuncin ba ko.
Fadimatu ta bata rai tana kallonta tace, nidai duk abinda zakuyimin kuyi zan dauka amma gaskiya banda sako iyayena aciki, uwata data barni anan ai dan batasan halinda nake ciki bane shiyasa kuma na kusa barmuku gidan ma ku....kafin ta karasa inna ta saka busashen hannunta da buge mata baki tana cewa, in fasa matsiyacin bakin nan naki dai yar iska, da sauri fadimatu ta kwace hijabinta ta fito daga dakin tana kukan karya tareda ihu tana cewa, mamansu jamila  zo kigani don Allah, fa'iza fa tana so abata danta yanata kuka inna ta hana, maman jamila din dake tsaye rike da kwarya ta kalli inna dake faman haki tace, shin waike hannatu bazaki rabuda yarinyar ban ba? Kin dai wahalar da ita iyaka wannan sharri dame yayi kama, kowa yaga Fa'iza yasan itace ta haifi yaron nan ga jini kace-kace a zaninta dazu amma saboda mugun hali bakiso ki yadda, inace watan daya gabata ma yarinyar nan taredake ake tausaya mata da zatayi alada saboda ciwon mara amma zaki rufe ido kice itace ta haihu, kowa ya zuba miki ido amma kin kasa dawowa hayyacinki, ni wallahi yaron ma dake yake min kama.
Daga haka fada ya koma tsakaninsu fadimatu ta sulale ta koma daki, murmushi tayi ganin fa'iza tana shayar da yaron tace ta girgiza kai tace, fa'iza ni nasan ke kika haifi yaron nan amma aka so a lika min yanzu don Allah me zaki cewa bawan Allah? Gara ki fito fili kice kina son aure ayi miki akan kije kina budewa garada kafa suna lalata dake, yanzu ta ina ma zaki gane uban yaron? Fa'iza ta sauke kanta kasa tana cewa, yaron lawali ne fa kuma yasan da cikin. Tsaki fadimatu taja tace, ke kina ganin wai dan ya sani ze karbi cikin ko kuma ya aure ki? Wallahi ya kwashe miki budurci a banza amma duk laifin inna ne.
Itadai fa'iza abin duniya ya isheta tayi shuru tana tunani.

Tun ranar data bar asibitin Dr yake yawan tunaninta, zuciyarshi ta kasa ajiye lamarinta ta dauko na wani, wani gefen yana ganin kamar ya cutar da ita, yayi amfani da rashin wayewar dayagani a tareda ita, kansa ya dafe tunowa da alkwarin daya daukarwa kanshi, takalminta daya ajiye gefen teburinsa ya kalla yana saka ran zata zo kodan takalminta data bari amma shuru bata zo ba.

Hakanan rayuwa take tafiya wasu tana musu dadi wasu kuma tana musu tsanani ta bangaren rashin jin dadi, baba gaba daya baya kula shaanin fadimatu, batada takamammen wuri guda da ake bata abinci a gidan balle sabulun wanki dana wanka, ko ruwan sha bata samu se idan ita ta debo, gefen da take kwanciya ne take ajiye bokiti da ruwa saita saka dankwalinta ta daureshi gudun kar wani abu ya fada mata ciki, idan kuma tayi rashin sa'a wata rana wani daga cikin gidan yazo ya juye ruwan.
Gidan da take zuwa taya matar gidan aiki dama basa jituwa to kuma tun sanda labarin ta haihu ya bazu a unguwa sai mijin matar yace shidai tabar zuwa masa gida tunda aka fara cewa ta haihu koda bata haihu ba tana kusa dan yaga tanada rawar kai, kafin ta baro gidan ranar da matar ta fada mata saida ta baro sako a fadawa mijin na maganganu marasa dadi, wannan dalilin ya saka ta rasa tudun dafawa nan take ta kara ramewa tayi baki.

Sati biyu kenan da faruwar abin ta soma ciwo wasa-wasa har ta kwana ta wuni ba wanda ya nemeta sunata shaaninsu, dakyar takai kanta gidansu uwani dan canne kadai inda take jin sanyi duk da bata samun fuska a wurin mamar uwani din.

Safiyyah galadanchi

TSAKA MAI WUYA Where stories live. Discover now