*TSAKA MAI WUYA*
*Safiyyah Galadanchi*
EXQUISITE WRITERS FORUM
11
Wani irin rufe ido tayi tareda matsesu sosai gabanta yayi faduwar da kamar zai bar jikinta, wannan ne karo na farko data tabbatar tana tsoron mutanen nan, ja tayi ta tsaya bayan ta saki jakar dake hannunta.
Kallon mamaki baba yake mata kafin ya samu tsaida tunaninsa waje daya akan me hakan da tayi yake nufi sai yace "ke kuma daga ina zuwa ina? Kika fito haka kamar wata marar gaskiya" ta sosa kai muryarta na rawa tace "a'a baba ba rashin gaskiya bane tsorata kawai nayi dana ganka banyi zaton ganinka ba gidansu uwani zanje inyi wanki" ya sake hade gefe-gefen babbar rigar dake jikinsa yana cewa "amma wane irin wanki ne yanzu da asubahin nan haske ma bai gama fitowa ba" ta dan ja baya tana cewa "jiya tacemin yau datayi salla zata fara shine nakeso inje in tayata nima in dan dauraye nawa saboda banda sabulu kuma kaga su gidansu da ruwan rijiya nan kuwa sena je debowa" ya gyada kai tareda fadin "to karki dade dai" ta amsa da to sannan ta fita gidan da sauri tana waige, saida ta danyi nisa da gidan sannan ta tsaya tana kallonshi a fili tace "wannan gida ne ko Kango? Hmm Nidai tunda na fito insha Allahu nabarshi har abada sai dai in tareda mama nazo" wani irin dadi takeji kamar ta isa tangaza haka take ji yau, koda taje tayi sa'a babansu uwani bai rufe gida ba bayan ya dawo tsakar gidan ba kowa tayi sallama ta shiga dakin uwani a zaune ta sameta tareda mama gabanta ya fadi dan tasan mama ba sake mata fuska take ba tasan zata iya hana uwani ta rakata, ta koma gefe ta dan zaune tareda gaisheta, maman uwani ta amsa tareda cewa "kinsan sunan mijin da mahaifiyarki ta aura" fadimatu ta girgiza kai tana cewa "Eh nasan sunanshi Alhaji Garba" mama ta danyi shuru sannan ta ce "nasan akwai sunan da ake masa lokacin dayake zuwa neman auren mamanki, bari na tambayo malam se in fada muku dakuma tashar da zakuje, sai dai ke uwani ki dawo kina kaita idan kunga driver din" uwani ta amsa da "insha Allahu mama ai bazan baki kunya ba tunda kika yi mana wannan alfarmar" fita mama tayi uwani ta kalli fadimatu ta ce "kalli kiga mama ta bamu dubu da da nera dari tace inbaki dari takwas ki biya kudin mota dari biyu mu hau napep zuwa tasha idan kin wuce na dawo da nera dari nabawa mai napep din daya dawo dani" fadimatu ta goge hawayen idonta ta ce "Allah ya saka da alkhairi nagode sosai kawata yar amana Allah ya nunamin aurenki" uwani tayi murmushi tare da daukar kwanon gefenta ta bawa uwani, dankalin hausa ne aka soya da mai da yaji, fadimatu tayi murmushi tana kallon kwanon ta ce "nidai kawata bani leda in tafi dashi naci a mota" uwani ta mike tsaye tana duba ledar kafin ta samo mama ta shigo tana cewa "idan kunje kice akaiki gidan alhaji garba naAllah koda baku samu wannan driver din ba wanda mamanki take aikowa da sako" fadimatu tayi mata godiya sosai sannan suka fita, babu dadewa suka samu adaidaita sahu ta wani yaro dan nan unguwar yakaisu kyauta ma a hanya uwani take cewa "idan kinci sa'a ma acan mama saita maidake makaranta ki karasa waec dinki kuma koya suka yi insun biki can karki sake ki dawo, so kawai suke su lalata miki rayuwa ki kare rayuwa a cikin jahilci kamar yadda suke suda yayansu, ni ban taba ganin dangin uwa haka ba sanina yaro ma se yafi shakuwa da dangin uwarsa akan na uba" fadimatu tayi tafi tareda cewa "ai da in dawo gidansu wallahi gara intafi tsaye ina salati saboda su bamutane ne masu daraja ba, musamman ni basu sona bansan me na tare musu ba" a haka suketa maida magana har suka isa tasha suna zuwa suka fara tambayar direban tangaza mai suna hamza nan take aka gane shi amma saidai a motarsa a lokacin ta daga zuwa tangaza sai dai tabi motar dake bayansa saura mutum uku motar ta cika, babu gargada tace ta amince zata shiga motar, uwani ta dan jirata sannan ta ce "bari na wuce idan kin isa ki samu waya ki kira lambar mama dana baki Allah ya tsare" fadimatu ta amsa da ameen sannan sukayi sallama.Lokacin da suka isa tangaza a tasha tayi tambayar hamza ashe shidin ne ma take tambaya yace mata gashi ta ce "gidan Alhaji garba naAllah nake tambaya, nice yar gidan Hadiza wacce take baka sako zuwa sokoto" nan take ya gano yayi saurin cewa "don Allah? Yanzu kuwa babu dadewa na sauke Pasinjan sokoto dana dauko, ai hadiza makotanmu ne gida biyu ne tsakaninmu yanzu muje in kaiki dan akwai sakon dazan karba kinsan mu bama zama yanzu zan juya sokoto" tayi murmushi cikin jin dadi tayi masa godiya sannan ya nuna mata motar ta shiga.
Kallon gidan take ta yi da suka shiga tun daga tsakar gidan ta hadu da kannenta mace da namiji su biyu sayyada da sa'id suka ruga da gudu suna ihun kiran sunan mama tareda fadin "wallahi ga yaya fadimatu nan" tana fitowa daga daki tayi tsaye gabanta yana faduwa wace fadimatu kuma ana zaune lafiya, tana cikin wannan tunanin sai gata ta shigo da sallama tana ganin mamanta tayi saurin jefar da jakar hannunta ta ruga da gudu ta rungumeta, mama itama rungumeta tayi tana cewa "zuwa haka Batula babu sanarwa ince dai lafiya"? Maimakon ta bata amsa sai ta saka kuka dama daganinta mama tasan ba lafiya ba tundaga yanayin kayan jikinta ta hadiye wasu yawu masu daci sannan tace "ya isa mana ko dukan ki wani yayi" ta girgiza kai tana cewa "mama kece fa kika dade baki zo ba nayi kewarki da yawa" murmushi tayi tareda fadin "shine kuma zaki tayarmin da hankali ki saka kuka? Yanzu ba gashi ke kinzo ba? Ya kika baro su zulai da yaransu" saida ta turo baki tace "suna lafiya sunce a gaisheki" ta sauke ajiyar zuciya tana cewa "ina amsawa amma menene haka batula sai kace ba budurwa ba dubi yadda kika lalace don Allah" fadimatu tayi kasa dakanta dan batason fadin wani abu yanzu so take sai ta dan kwana biyu daidai ta dan huta itama mama ta saki jikinta, mama ta katse mata tunani da cewa "nidai tashi kiyi wanka kafin makota su shigo a ganki a haka kamar mahaukaciya duk kin yamutse wai da sunan kina zama a birni, tashi ki shiga a kwai zani a jikin kofa ki cire wannan kayan ki daura kizo nan ga ruwa a tukunya ki juye ki zuba min wasu" mikewa tayi ta shiga dakin ta cire kayan sannan tazo tashiga wankan tana fitowa mama ta kalli gashinta ta ce "wai ni koro sukayi ne kika zo a haka batula, gashinki duk ya lalace baki kula dashi ko" bata ce komai ba ta wuce cikin dakin nan mama ta bude jakar kayanta a tsakar gida mamaki ya kamata saboda yadda kayan suka kode wasu daga ciki har sun yage sai wani tashi sukeyi marar dadi, ranta yayi matukar baci dan a duniya ta tsani kazanta.
Dakin ta shiga ta sameta ta shafa mai tana taje gashinta sai ihu take saboda zafi mama tace "anya yarinyar nan kinada hankali? Wancen kayan da kika zo dasu badai sune kayan sawarki ba ko"? Tana kallonta tace "mama sune mana, babu mai yimin dinki inba ke ba sune kayan sawata" mama ta zauna kusa da ita tace "ke fadamin gaskiya wallahi banson iskanci, duk ina kayan da nake aika miki" idonta ya cika da kwalla ta ce "mama basa bani ko kayan sallar da kika aika min inna zulai faiza ta bawa bata bani ba duk aiken dakikayi bayan kin dawo nan ba a bani ba mama, gidan nan kamar zaman kaina nake, babu sabulun wanka babu na wanki babu abinci mama" mama tayi wani irin tsuke fuska tareda cewa "to ina shi baban su fa'iza da sauran kawunan ki" kuka ne ya riketa dakyar tace "sunanan babu mai kula dani wani lokacin sai maman jamila, yanzun ma dana zo sun saka ranar da za'a zo neman aurena ne nikuma na gudo nan" mama ta tashi tsaye tace "Aure a gidan ubanwa? Na rantse da Allah har yanzu mutanen nan basu san halina ba wallahi amma su sani dani suke zancen" fadimatu ta danji sanyi dama tasan iskancin dasu baba keyi saboda bata nan ne saboda tasan halin mahaifiyarta badai fada ba saboda ta sake tunzurata tace "kuma mama kwanaki fa'iza ta haihu cikin shege suka ce Ni na..." "ke dalla daga can ki rufe min baki doluwar banza, ni wallahi kamar bani na haifekiba baki gado halina ba ke bakisan ciwon kanki bane zaki zauna suna cin amanarki har haka, ciki uban waye ya miki da zaki haife shi duk suna zaune basuga ciki ba se haihuwa? Na rantse da Allah dukansu su kiyayi haduwarmu dan bazatayi kyau ba ko koto sena maka su dan bazan zauna su lalata miki suna ba shikuma mai gidan bari ya dawo duk yadda za'a yi sedai ayi dan inbazaki zauna gidan nan ba sedai mu duka musan nayi, ina ji ina gani da raina da lafiyata alalatamin rayuwarki shine abinda bazan lamunta ba, dama nan yara ne suka tauyeni saboda tausayinsu yan Marayun Allah amma yanzu dole ne na samu lokaci naje" shuru fadimatu tayi dan ta fara tsoron uwar tata shiyasa tayi gum bata karasa fada mata labarin ba sai can tajiyota tana cewa "shi wanene suke neman bawa auren naki kuma yaya zancen makarantar ki a sanina wannan shekarar zaku gama...."