*TSAKA MAI WUYA*

Safiyyah galadanchi

EXQUISITE WRITERS FORUM

7

Driving yake amma tunanin ma yadda zai iya nuna wannan family yace family din matarsa ne a wurin friends dinsa ai girma ya gama zubewa, dogon tsaki yaja tareda fadin "indama na sani nayi mai gaba daya insan da dalili Abba zai aura min ita, amma ya kamar wannan yarinyar zata nuna bata san komai ba? Hmmm..."

Koda ya koma gida bai shiga part dinsu ba nashi ya wuce dan gaba daya ji yake kamar ya rusa gidan, haka ya koma kamar zararre har bai ma sanin lokacin dayake fadin wata maganar a fili, yana ganin kamar ma Abba so yake ya tozarta shi.

Halisa da saima ne zaune a dakinsu suna tattaunawa akan maganar su kansu mamakin suke yadda Abba zai iya hada yayansu aure da wannan yarinyar, halisa tace "wai saima kinji warin da yarinyar nan takeyi ranar? Ga uban gashi ba'a san darajarshi ba gaba daya dakin nan seda ya dauka, sefa dana wanke mata gashin dan nasan yaya bazai bari ta shigar mai mota ba" saima ta tabe baki tana yamutsa fuska tace "shiyasa banma biyo ku ba tsaf sena amayar da abinda naci,tsabar talauci ne yasaka basu ma iya kula da jikinsu, ni da Abba zai hakura idan aure yakeso yayiwa yaya ga kanwar sadeeq nan mai sunan hajiya" halisa ta girgiza kai tace "raba kanki bakiji me Abba yayiwa hajiya ba aike inaga sedai duka"  ta sauke ajiyar zuciya tace "amma dai kinsan wannan yarinyar abin kunyane ma aga yaya Hisham da ita wai matarsa ce ko? Koda yake shi ya jawa kansa dan jarabar tsiya" Halisa tayi dariya zatayi magana wayarta tayi ringing...

Washe gari tunda tayi sallar asuba ta fito tsakar gidansu ta zauna bakin kofar dakinsu tana ta mamakin bataga fa'iza ba bayan tare suke kwana adakin, har rana ta fito tana zaune wurin tana kallon yara da iyayensu daketa kai da kawo cikin gidan, ita dai yanzu gaba daya hankalinta ya koma wajen mahaifiyarta so take ta ganta ko suyi magana, ta gaji da zama gidan nan, inna ta fito ta dora dumamen tuwo, fadimatu na kallonta ta gaida ita amma taki amsawa, muryarta na rawa kamar zatayi ta isa kusa da ita tace "inna don Allah kiyi hakuri" inna ta dago kai ta kalleta tace "inyi hakuri da kikayi min uban me? Matsa daga kusa dani kinaji ko" ja baya tayi kadan ta sake cewa "don Allah ki kiramin mamata tazo ta dauke ni" dafe kirji inna tayi tana raba ido a tsakar gidan tace "wani kicihin da kilibibin zaki tsiro dashi shiyasa kika zo nan kika zauna tun dazu kinata kunci, wannan yarinya uwarki ta gode Allah data haifeki lafiya, bari inkira baban fa'iza yazo yaji abinda kika fadamin" daga haka ta isa kofar dakinta ta daga labulen dakin tareda cewa "taho kaji da kunnenka abinda fadimatu take fadamin yanzu" zaburowa yayi daga shi sai babbar riga yana faman kakkamawa yace "wai me take cewa"? Inna ta buntsire baki tace "cewa take a kira mata uwarta tazo ta dauke ta" ya rike baki yana hararar fadimatu yace "uwarki tazo ta daukeki akan wane dalili? Baiwar Allah duk kokarin da take dake duk da bakya gari baki gani sekin bita ki kaso mata auren ta dawo ta zauna dake nan ko"? Inna ta dauki robar tuwo tana jefa malmayen tuwon cikin tukunya tana cewa "ahto tambayeta dai sekace wani abin ake mata a gidin nan, gaba daya ta rainamu da abinda muke mata, kuma wallahi akwai abinda bata sani ba mune ita duniya da lahira" baba ya kalli fadimatu yace "yunwa gareki ko kishin ruwa? Ko wani ya takuraki ya hanaki yin abinda kike so kiyi ne? Ai mu za a yiwa sannu tunda kiketa dauko mana abin magana, yanzu wannan cikin ina kikeso mutafi dashi, illa muyita hakuri tunda kun gama lalacewa" kallon baba fadimatu tayi tafeda fadin "baba ni wallahi banda cikin komai malaria ce da typhoid yake damuna, jiya munzo tareda likita amma inna bata saurareni ba ta hauni da duka  harya tafi" kusan dukanta yayi ta matsa da sauri tana sake cewa "inna ko ruwanta bata bari nasha kuma wallahi baba bata bani abinci kullum inyita zama da yunwa" inna ta saki robar hannunata tana tafa hannun tareda fadin "innalillahiwa'inna'ilaihiraji'un, Wannan karon wallahi inaga da isiya zan hadaki yayi miki dan banzan duka, kuji shegiyar yarinya, kin taba zuwa gidan nan kikace in baki abinci na hanaki? Mugun hali dai duk inda kikayi sekin nuna shi shiyasa mijin lawisa ya hanaki aiki gidansa" baba yayi tsaki yace "shi likitan ina kika sanshi da har yasan cewa ba ciki bane koshine kwarton naki"? Bata kula shi ba ta koma bakin kofar ta zauna tana kuka, inna ta zuba tuwon a kwano ta kalleta tana cewa "zo ki dauka badan halinki ba" amma ki sani dakin gama kizo ki sharemin dakina tun rana ita yau ban samu zama ba balle in share da kaina dansu mai sunan uwata makaranta suke zuwa yanzu babu zama"
Fadimatu taje ta dauki robar ta shiga dakin ta zauna tana kallon tuwon, abincin gidansu Hisham ta tuna ga nama amiya kamar miyar naman akayi zalla nan ko bata tunanin ma da kayan miya aciki kila yaji ne aka Barbada aruwa aka kada kukar.
Hakanan tadan tsakuri tuwon ta ajiye dan gaba daya ya fita ranta ita kawai inda mama takeson taje.
Magani tasha tadan huta sannan taje ta share mata dakin sama-sama sannan ta fita daga gidan.

TSAKA MAI WUYA Where stories live. Discover now